Thursday 19 September 2019

Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai da Harin da aka Kai a Matatar Man kasar Saudiyya - Shugaba Buhari

Tura Wannan Zuwa Ga
Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kai a matatar man kasar Saudiyya tare da kuma tabbatar wa Kasar Saudiya goyon bayan ta.

Shugaba Muhammadu Buhari

Marubuci: Sani Twoeffect Yawuri

Shugaba Buhari yace Gwamnatin Tarayyar Najeriya tana nuna alhininta tareda Jajintawa Kasar Saudiya bisa wannan harin da aka kai mata a matatar man kasar dake Khurais da Abqaiq.

A cikin kalaman nasa, shugaba Buhari yace:

" Muma anan Najeriya mun taba samun irin wannan harin a matatar man mu. Amma insha Allahu kamar yadda basuyi nasara a baya ba, haka ba zasuyi wata nasara anan gaba ba da yardar Allah.

"Koda yake har yanzu ba'asan ko suwaye suka kai harin da jirgi maras matuki ba akan matatar man ta Saudiyya, da kuma a ina suke ba. Tabbas wannan wani hari ne wanda manufarsa itace lalata tattalin arzikin kasar kamar yadda za'a iya gani a zahiri, amma ainihi hakan yana nufin lalata ababen more rayuwar Jama'a ne kawai.

"Saboda irin wannan zai cutar da al'umma ne da basu jiba basu gani ba

"Wadanda suka kai wannan hari tabbas ba zasu samu magoya baya ba akan hakan daga kasashen Duniya koda kuwa su wayesu. Saboda haka, da yardar Allah zasu girbi abinda suka shuka".

DUBA WADANNAN:

Karshen Duniya Kidnappers Sun Sato Yaro Aljani...Latest Video

KARANTA BAYANI AKAN AIKIN MAMBILA HYDROPOWER PLANT DAKE JIHAR TARABA

Karya Kake Ka ce Jihar Ribas ta Kiristoci ce - Martanin Asari Dokubo ga Gwamna Wike

Kalaman Shugaba Muhammadu Buhari kenan.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user