Showing posts with label Labari da Dumi-Dumin Sa. Show all posts
Showing posts with label Labari da Dumi-Dumin Sa. Show all posts

Wednesday, 13 November 2024

Dan Bello Ya Maida Martani Na Kaitsaye Ga Masu Son Ya Tsaya Takara

Dan Bello Ya Maida Martani Na Kaitsaye Ga Masu Son Ya Tsaya Takara

Tun ba yau ba matasa daban-daban suke yin kira ga Ɗan Bello da ya fito takara, za su goya masa baya, sai dai bai taɓa mayar da martani kan hakan ba.

Ɗan Bello Galadanchi ya maida martani ga masu neman ya tsaya takara

A ranar biyu ga watan nuwambar wannan shekarar da muke ciki ne dai Ɗan Bello ya yi hirar kaitsaye a shafin shi na sada zumunta na facebook kan batun yaran nan da aka kama saboda sun ɗaga tutar ƙasar Rasha a yayin gudanar da zanga-zanga, a cikin hirar kaitsaye ɗin ce ɗaya daga cikin mabiyansa mai suna Muhammad Bello Rum Biki ya yi masa tambaya kan cewa "Dan girman Allah ka fito takara". Inda shi kuma ya amsa masa da cewa "Ni ba ɗan ƙasar ba ne, kundin tsarin mulki ba ya bai wa 'yan wasu ƙasar dama su tsaya takara.".

DUBA WANNAN: Kalli Zafafan Hotuna Tare Da Tarihin Bello Galadanchi/Dan Bello

Ɗan Bello dai ya samu karɓuwa ne a gurin jama'a saboda yadda ya shahara wajen tona asirin 'yan siyasar da suke cin amanar fararen hula.

Sunday, 4 August 2024

Kalli Yadda 'Yan Saudiya Su Je Har Ɗakin Ka'aba Don Taya 'Yan Najeriya Zanga-Zanga

Kalli Yadda 'Yan Saudiya Su Je Har Ɗakin Ka'aba Don Taya 'Yan Najeriya Zanga-Zanga

A yau Lahadi ne aka shiga rana ta huɗu da fara yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a faɗin ƙasar Najeriya.

Mazauna ƙasar Saudiya

A saboda haka ne, aka samu wasu mazauna ƙasar Saudiya waɗanda 'yan asalin ƙasar Najeriya ne suke taya 'yan Najeriya kokawa kan al'amuran da ke damun su.

Kalli bidiyon kai-tsaye anan..

Wani daga cikin su ma har ɗakin ka'aba ya je ya yi addu'a ta musamman domin Allah ya kawo wa ƙasar mafita.

Tuesday, 2 July 2024

Umar Bush Ya Kunyata Masoyiyar Sa A Gaban Jama'a

Umar Bush Ya Kunyata Masoyiyar Sa A Gaban Jama'a

Martanin da Umar Bush ya yi wa masoyiyarsa.

Umar Bush ya kunyata masoyiyarsa

Bayan ya gama kushe ta, sai ya kunyata masoyiyar tasa, inda ya mayar mata da martanin cewa "Ki kashe kan naki idan har sai kin aure ni."

Kalli martanin nasa kai-tsaye anan...

A makon nan ne dai aka samu ɓullar bidiyon wata matashiyar budurwa wadda ta yi ikirarin cewa "Idan har ban auri Umar Bush ba, Wallahi Tallahi zan iya datse kaina."

Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe don samun cikakken tarihin Umar Bush nan bada daɗewa ba.

Monday, 1 July 2024

Zan Iya Kashe Kaina Idan Har Umar Bush Bai Aure Ni Ba

Zan Iya Kashe Kaina Idan Har Umar Bush Bai Aure Ni Ba

Wata matashiyar budurwa ta yi ikirarin kashe kanta idan har Umar Bush bai aure ta ba.

Zan iya kashe kaina a kan Umar Bush

Matashiyar budurwar ta cire duk wata kunya ta 'ya mace inda ta bayyana soyayyar ta ga Umar Bush.

Kalli bidiyon kaitsaye

Ta yi ikirarin cewa "Idan har ban auri Umar Bush ba, Wallahi Tallahi zan iya datse kaina."

Sunday, 30 June 2024

Gaskiya Game Da Mala'ikan Da Ya Bayyana A Makka

Gaskiya Game Da Mala'ikan Da Ya Bayyana A Makka

Madam Talash mata-maza ne, wanda mafi yawan mutane a arewacin Najeriya suka yi zaton cewa Mala'ika ne ya bayyana a siffar Ɗan Adam, sai dai kuma wasu bayanan suna nuni da kasancewar sa a matsayin wanda ya sauya jinsin sa.

Gaskiya game da mala'ikan da ya bayyana a makka

Sai dai a zahiri mutum ne kamar kowa, mazaunin ƙasar Pakistan, wanda ya kasance mai yin raye-raye a guraren tarurruka, ba kamar yadda wasu mutanen suke yin zaton Mala'ika ba ne.

Kalli bidiyon kai-tsaye

Ku ci gaba da kasancewa tare da mu don samun cikakken tarihin Madam Talash.

Wednesday, 1 May 2024

Kalli Zafafan Kyawawan Hotunan Fatima Mai Zogale

Kalli Zafafan Kyawawan Hotunan Fatima Mai Zogale

Fatima Aliyu wadda aka fi sani da Fatima Mai Zogale, tana  ɗaya daga cikin waɗanda nasarar su take zama abar tattaunawa a gurare daban-daban a yau.

Fatima Aliyu
Hoto: Fatima Mai Zogale 

Fatima Mai Zogale, ita ce wadda fitaccen mawaƙin nan na Arewa wato Dauda Kahutu Rarara ya rera wa waƙa.

Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.

Fatima Mai Zogale ta kasance masoyiyar waƙoƙin Rarara ce ita tun kafin ma ta san shi.

Waɗannan ƙarin wasu ne daga cikin kyawawan hotunan nata;

Fatima Mai Zogale
Hoto: Fatima Mai Zogale 

Fatima Aliyu
Hoto: Fatima Mai Zogale 

Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe don samun tarihin Fatima Mai Zogale da zafafan hotunan ta na musamman.

Wednesday, 18 November 2020

Kalli Bidiyon Abin Mamakin Da Wata 'Yar Kasar China Mai Jin Yaren Hausa Tayi Ya Girgiza Duniyar Hausawa

Kalli Bidiyon Abin Mamakin Da Wata 'Yar Kasar China Mai Jin Yaren Hausa Tayi Ya Girgiza Duniyar Hausawa

Wani bidiyon wata basiniya 'yar ƙasar China ya karaɗe shafukan sada zumunta, wanda bidiyon yake nuni da yadda wasu 'yan ƙasar China suke hawa kan tsohuwar waƙar Hausa ta mawaƙi Abubakar Sani, anyi wa waƙar taken "ZAKKA".

KANDE GAO

Duba da yanayin yadda dukkanin su, suka hau kan waƙar ya ɗauki hankulan al'ummar Hausawa,  tamkar dama sune ainihin waɗanda suka fara hawa kan waƙar ZAKKA.

Sai dai dukkannin su, sun koyi yaren Hausa ne, a ɗaya daga cikin jami'o'in ƙasar Nijeriya, inda ake yiwa macen laƙabi da KANDE yayin da ake yiwa namijin laƙabi da MURTALA.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Wasu ɗalibai ne, waɗanda suke yin karatu a ƙasar Sin, suka buƙaci su taya su ɗebe kewa da waƙar Zakka.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Saturday, 31 October 2020

Karshen Duniya: Yayiwa 'Yar Cikinsa Cikin Shege

Karshen Duniya: Yayiwa 'Yar Cikinsa Cikin Shege

Idan baka mutu ba, zaka ga abubuwan mamaki, wasu na farin ciki wasu kuma na baƙin ciki yayin da wasu kuma na takaici.

Yayiwa 'Yar Sa Fyaɗe

An samu wani magidanci yana kwantawa da 'yar cikinsa bada son ranta ba (Fyaɗe).

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Mahaifiyar yarinyar tayi cikakken bayanin yadda abun yafaru a tattaunawar ta da jaridar Rigar 'Yanci.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan Allah ya kiyaye mu daga sharrin sha'awa  Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Sunday, 20 September 2020

Kalli Abinda Dole Ne Ya Sa Ku Yin Kuka | Kai Rayuwa | Kai Duniya | Taron Karshe Na Marigayi Dr. Shehu Idris Sarkin Birnin Zazzau

Kalli Abinda Dole Ne Ya Sa Ku Yin Kuka | Kai Rayuwa | Kai Duniya | Taron Karshe Na Marigayi Dr. Shehu Idris Sarkin Birnin Zazzau

A yau lahadi ne Allah yayiwa Sarkin Birnin Zazzau Alh. Shehu Idris rasuwa, an yi jana'izar sa da misalin ƙarfe biyar na yammaci yau.

MUTUWA ƘARAR KWANA

Idan ba zaku manta ba, a cikin wannan shekarar da muke ciki (2020) ne aka yi bikin cikar shekaru arba'in da biyar da hayewan marigayi HRH. Shehu Idris kan  karagar mulkin birnin Zazzau.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Ya rasu yana da shekaru tamanin da huɗu a duniya, wanda yayi dai-dai da watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin (20/02/1936 zuwa 20/09/2020).

MURYAR HAUSA24 muna fatan Allah ya haskaka makwancinsa, yasa mutuwa hutu ce a gare sa, ya kuma sanya Aljannah Firdausi ta kasance masaukin sa na ƙarshe, mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da kuma Imani Amin Ya Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Saturday, 25 July 2020

Labari Mai Ratsa Zuciya: Allahu Akbar!!! Ya Kasa Tafiya Ya Bar Mahaifiyar Sa

Labari Mai Ratsa Zuciya: Allahu Akbar!!! Ya Kasa Tafiya Ya Bar Mahaifiyar Sa

Wannan hoto da kuke gani wani bawan Allah ne Mahaifiyarsa ta kamu da cutar CORONAVIRUS (COVID-19).

Abin tausayi! Allahu Akbar!!!

Marubuci:- Musa Muhammad Dankwano

An kai ta wajen killacewa (Isolation Center) shi kuma ya kasa tafiya gida, sannan an hana shi shiga ya ganta, shi ne ya kama katanga ya hau kan tagar ɗakin da take ciki domin ya hango ta.

Jiya kuma Allah Ta'ala Ya yi wa Mahaifiyar ta sa rasuwa! Ta mutu! Allahu Akbar ta mutu! Inna Lillahi wa inna ilaihi Raji'un ta rasu.

Wannan labari gaskiya ne. Malam Haitham Al-Huwainiy (Ɗan babban Malamin Duniya Shaikh Abu Ishaq Alhuwainiy) ne ya wallafa hoton tare da bayani a shafinsa na facebook.

Allah Ya yi mata Rahama Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 24 July 2020

Ina Son In Yi Aure Amma Bansan Dalilin Da Yasa Samari Suke Jin Tsoron Yi Min Magana Ba - Fatima Zahra

Ina Son In Yi Aure Amma Bansan Dalilin Da Yasa Samari Suke Jin Tsoron Yi Min Magana Ba - Fatima Zahra

Ɗaya daga cikin mabiya shafin sada zumunta na dandalin twitter Fatima Zahrah tayi wani jawabi wanda ya girgiza hankulan dubban mutane mabiya shafukan yanar gizo.

Ina Buƙatar In Yi Aure

A cikin jawabin nata tace "Ni ba ƙaramar yarinya bace amma kuma bansan dalilin da yasa samari suke jin tsoron yi min magana, kuma gashi ina buƙatar yin aure".

Aure Nake So

Biyo bayan wannan jawabin nata, nan take samari suka fara yin tururuwa don nuna sha'awar su, don ganin sun gwada sa'ar su ko zasu dace.

Kalli ƙarin hotunan Fatima Zahrah a ƙasa:

Ina Buƙatar In Yi Aure

Ina Buƙatar In Yi Aure

Ina Buƙatar In Yi Aure

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Sunday, 5 July 2020

Shin Dagaske Ne Dr. Isah Ali Pantami Ya Mallaki Manyan Gidaje A Birnin Tarayya?

Shin Dagaske Ne Dr. Isah Ali Pantami Ya Mallaki Manyan Gidaje A Birnin Tarayya?

Kafar watsa labarai ta yanar gizo (Sahara Reporters) ta wallafa labarin ƙarya ta na iƙirarin cewa wai "Ministan Sadarwa da tattalin arziƙin fasahar sadarwar zamani, Shaik, Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami ya sayi wasu gidaje guda uku tun bayan zamansa Minista".

Dr. Isah Ali Pantami

Marubuci:- Garba Tela Hadejia

Wannan labari ne na ƙanzon kurage da aka kitsa da manufar ɓata kima da darajar Minista Pantami, domin tun bayan zamansa Minista babu wani gida da ya saya a ko'ina a faɗin duniya.

Ɗaya daga cikin gidajen da aka wallafa a jaridar, Dakta Pantami ya mallake shi ne tun a cikin watan Janairu na shekarar 2017 sama da shekara biyu kafin ya zama minista. Ya yin da shi kuma ɗaya gidan ya kasance hayarsa ya karɓa tun a ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 2019. Biyu daga cikin hotunan kuwa ba shi da masaniya a kansu.

Gidajen Da Ake Yaɗawa...

A matsayin Dakta Pantami na minista, albashinsa da alawus-alawus ɗinsa bai kai abin da ya ke samu ba a matsayin Farfesa a Jami'ar musulunci ta ƙasa da ƙasa da ke Madina, saudi Arabia ba. Kuma har yau a tarihi shi kaɗai ne ɗan Nageriya na farko da ya koyar a wannan mataki. Ya dawo Nageriya ne da manufar ba da gudunmawarsa a gina ƙasa.

Gidajen Da Ake Yaɗawa...

Dakta Pantami na ɗaya daga cikin ƴan Nageriy ƙalilan da su ke sadaukarwa kan kishin ƙasa. Ɗan kasuwa ne da ya yi nasara tare da samun kykkyawar rayuwa. A nagarta irin ta Dakta Pantami mutum ne da ya ke yaƙi da rashawa da cin hanci a tsakanin gwamnati da al'umma ba a Nageriya kawai ba har ma duk duniya.

Gidajen Da Ake Yaɗawa...

Mu na fata jama'a za su yi watsi da duk wani yunƙuri na ɓata kima da darajar Minista Pantami, sannan kuma mu na fatan kafofin sadarwa a Nageriya za su riƙa samar da tsare-tsaren bin diddigin labari kamar yadda tsarin aikin jarida ya tanadar tare da gujewa labaran kanzo kurege domin kare martabar aikinsu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng

Saturday, 23 May 2020

A Karan Farko Malaman Addini Sun Fara Bijirewa Umarnin Sarkin Musulmai a Nigeria Muhammad Sa’ad Abubakar III

A Karan Farko Malaman Addini Sun Fara Bijirewa Umarnin Sarkin Musulmai a Nigeria Muhammad Sa’ad Abubakar III

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya faɗi matsayarsa dangane da yin Sallah ranar Asabar.

Matsayar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

A wannan ɗan taƙaitaccen bidiyo mai matsakaicin zango malamin ya faɗi dalilin da yasa ya gamsu dayin Sallah a ranar asabar saɓanin sauran al'ummar ƙasar Nijeriya mafi yawancin su a gobe Lahadi zasu yi bikin idin ƙaramar Sallah.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye....

Shehin malamin ya bayyana yau a matsayin ranar Sallah, inda ya ƙara da cewa, anga wata a wasu garuruwan ƙasar don haka su sun ajiye azumin, a cewar sa yau ɗaya ne ga watan shawwal.

A ƙasar Niger maƙwabciya ga ƙasar Nijeriya yau take idin ƙaramar sallah, a ƙasar Saudiyya gobe Lahadi ne ranar idin ƙaramar sallah wanda yayi dai-dai dana ƙasar Nijeriya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Wednesday, 20 May 2020

LOCKDOWN: KALLI YADDA KASUWANCI YA KOMA A JIHAR KANO

LOCKDOWN: KALLI YADDA KASUWANCI YA KOMA A JIHAR KANO

Ranaku biyu gwamnatin Kano ta sassauta a lockdown ɗin da ake ciki, wato Litinin da Alhamis don yin siyayya, a tsakanin ƙarfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

YADDA KASUWANCI YA KOMA A JIHAR KANO 

Marubuci:- Kabiru Yusuf Fagge

Amma a zahiri mutane na fitowa ne tun da asubar fari, wato tun ƙarfe 5 ko 6, kuma har zuwa ƙarfe 8 ko fiye na dare al'umma suna harkokinsu.

Kasuwannin 'Yankaba (na kayan miya) da 'Yanlemo (kayan marmari) kaɗai gwamnatin Kano ta amincewa su buɗe, sai kawai manyan kantunan siyar da kayan masarufi.

Amma gwamnati ta ƙi amincewa a buɗe manyan kasuwannin da ke Kanon kamar kasuwar Sabongari da ta haɗa duk irin kayayyakin da ake buƙata, da kasuwar Kantin Kwari ta shaddodi da atamfofi, da Kasuwar Wambai da Kasuwar Rimi da Kasuwar Singa ta kayan masarufi da sauransu.

Sai dai 'yan kasuwannin nan sun koma cin kasuwar tsaye da tsaye inda suke cika unguwannin da ke gefen ire-iren waɗannan kasuwanni musamman unguwar Fagge. Inda ake cika layuka ake kasa kayayyaki, kuma aka yi cunkus fiye da kasuwannin ma.

Hukumomin tsaro sun yi ƙoƙarin hana cin irin waɗannan kasuwannin, amma abin ya gagara.

An samu cunkuson ababen hawa fiye da yadda ake zato a duk manyan da ƙananan titunan da ke Kano, don wasu wuraren da za a iya zuwa a mintuna goma sai a yi awa ɗaya a hanya ana tafiya.

An yi bonono, wato rufe ƙofa da ɓarawo,domin tarin baki daga jihohin Nijeriya suna shigowa Kano a duk lokacin da aka ce an buɗe ɗin nan (ranakun Litinin da Alhamis) su yi siyayya, su fita.

Kayayyakin da ake buƙata sun yi matukar tsada. Waɗanda ba a buƙata kuwa masu su, suna karyarwa su siyar don su samu abin da za su siyi abinci.

Ta dalilin rufe kasuwanni, kayan wasu 'yan kasuwa za su lalace, musamman irin maya-mayai da sauransu, saboda zafi.

Al'umma ba sa yin amfani da takunkumin rufe hanci, ba a damu da tazarar tsakani ba (social distancing), ba a yawaita wanke hannu da sauransu.

Tabbas kasuwanci a Kano yana cikin wani hali, fatanmu Allah ya farfaɗo da shi, bayan an yarda za a rayu cikin wannan annoba, Allah Ya magance mana ita, Amin.

Hoto Daga: Hafiz Amin Fagge

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Sunday, 17 May 2020

Da Dumi-Dumi: Za Aci Tarar Sama Da Miliyan Biyu Ga Duk Wanda Bai Sa Takunkumin Rufe Fuska Ba

Da Dumi-Dumi: Za Aci Tarar Sama Da Miliyan Biyu Ga Duk Wanda Bai Sa Takunkumin Rufe Fuska Ba

Duk wanda ya fito waje ba tare da ya saka takun-kumin rufe fuska da hanci ba (Face mask) zai biya dollar dubu hamsin da biyar ($55,000) a matsayin taran karya dokar magance cutar Sarƙewar Numfashi (Coronavirus) a kasar Qatar.

Dokar Ta Ɓaci..

Marubuci:- Abdulhadi Isah Ibrahim

Taran dala dubu 55,000 dai-dai yake da kuɗin Nigeria Naira miliyan 21 da dubu dari biyu da 'yan kai.

A sabuwar dokar da hukuncin da za'a yanke wa masu karya dokar saka face mask a Qatar.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tuesday, 4 February 2020

Hauwa Yunusa Kyakkyawar Bafulatanar Da Ta Jefa Kanta Cikin Harkar Garkuwa Da Mutane

Hauwa Yunusa Kyakkyawar Bafulatanar Da Ta Jefa Kanta Cikin Harkar Garkuwa Da Mutane

Hauwa 'yar shekaru 24 kacal, amma ƙwararriya ce wajen fashi da makami, garkuwa da mutane da aikata kisa. Ta yi aure sau uku, tana rabuwa da mazajen saboda rashin jin maganarta.

Karshen Duniya...

Marubuci: Sa'eed Usman Assalafy

'Yar asalin ƙabilar Fulani ce wacce take zaune a garin Masaƙa dake jihar Nassarawa amma haifaffiyar jihar Jigawa.

Ita ta shirya yadda aka yi garkuwa da samarinta guda uku, inda suka biya kuɗin fansa. Saurayinta na farko ya bada miliyan biyu bayan da aka ba ta dubu ɗari biyu, bayan ya kwashe kwana biyu a hannun abokan aikata laifin nata, shi kuma na biyu ya biya miliyan ɗaya, inda aka ba ta naira dubu hamsin, na ukun kuma ya bada dubu ɗari biyar saboda a cewar ta shi ba mai kuɗi bane.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye..

Duk waɗan nan kuɗaɗe basu ishe ta ba, hakan ya sa ta haɗa baki da abokan ta'addancinta suka sace ƙawar ta mai suna Zainab saboda ta ji abokiyar tata tana faɗin cewa an turo mata da kuɗi har N600,000.

A dalilin wannan Zainab ta rasa ranta saboda tsantsan wahala da ta sha, sai Hauwa ta je ɗakinta ta dauki ATM din Zainab da nufin ta kwashe duk kuɗin dake cikin asusun ta, sannan ta sauya wa motar Zainab fenti sannan ta sayar da ita, kazalika ta sayar da dukkannin kayayyakin da marigayiya Zainab ta mallaka.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ABU BIYU NE KAWAI ZAKA IYA YI IDAN KA HADU DA WANDA YAFI KARFIN KA

KARANTA ABINDA YA KAMATA KU YI DA ZARAN ANYI GARKUWA DA 'YAN UWAN KU

MARYAM SANDA SHARI’AR ALLAH TA’ALA KO CONSTITUTION??

Hauwa dai a halin yanzu ta shiga hannu kuma ƴan sanda tun farkon shekarar da ta gabata, suna gudanar da bincike a kanta.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Wednesday, 29 January 2020

Wallahi Zan Auri Maryam Sanda Idan Har aka Yafe Mata Laifin Ta - Abdulwahab Haladu Zarma Hina

Wallahi Zan Auri Maryam Sanda Idan Har aka Yafe Mata Laifin Ta - Abdulwahab Haladu Zarma Hina

Dama haka rayuwa take, a lokacin da wani ya tsaneka wani a lokacin ne wani yake masifar Son Ka.

Ra'ayi Riga..

Bayan Kotun babban birnin tarayya ta yankema Maryam Sanda hukuncin Kisa ta hanyar Rataya bisa laifin da ake tuhumarta da kashe mijin ta Bilyaminu Bello har Lahira.

Sharhin Abdulwahab Haladu Zarma Hina

Wani bawan Allah mai suna Abdulwahab Haladu Zarma Hina ya Bayyana a shafin sa na sada zumunta Cewa "Ni Wallahi idan aka Yafema Maryam Sanda Laifinta zan aureta idan ta amince, Allah yasa a mata ahuwa".

Abinda Abdulwahab Haladu Zarma Hina yace Bayan an Yankema Maryam Sanda Hukuncin Kisa..

Kalli Bidiyon Kai Tsaye... 

Kamar yadda wakilin Muryar Hausa24 ya Shaida mana Cewa "Maryam Sanda ta Kashe Mijinta Bilyaminu Bello a ranar 9-11-2017". Kotu ta yanke mata hukuncin Kisa a ranar 28-01-20202.

Marigayi Bilyaminu Bello da Matar sa Maryam Sanda

Wasu daga cikin hotunan Maryam Sanda bayan kotu ta yanke mata hukunci Kisa ta hanyar rataya.

Maryam Sanda tayi Kururuwa bayan an zartar mata da Hukuncin Kisa... 

Alkalin da ya yankema Maryam Sanda Hukuncin Kisa... 

Maryam Sanda a cikin Kotu bayan Alkali ya yanke mata hukuncin Kisa.. 

Hotunan Maryam Sanda tare da Mijin ta.

Maryam Sanda tare da Mijin ta Bilyaminu Bello

Maryam Sanda tare da Ɗiyarta

Ku ci gaba da kasancewa da shafin mu a www.muryarhausa24.com.ng don samun cikakken abinda Ke faruwa da Maryam Sanda bayan kotun babban birnin tarayya ta yanke mata hukuncin Kisa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

ABINDA YAFARU A DARAN JIYA NI DA MATA TA

TONAN SILILI ZUWA GA MAZAN FACEBOOK SAKO DAGA FADILA H. ALIYU KURFI

KARANTA ILLOLIN ZAMA DA MATAR AURE GUDA DAYA

Maryam Sanda

Insha Allah nan bada daɗewa ba MURYAR HAUSA24 zamu kawo muku Cikakken Tarihin Maryam Sanda (Biography of Maryam Sanda ).

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Friday, 20 December 2019

'YAN AREWA SUN KAFA TARIHI A YANKIN KUDU MASO KUDANCIN NIGERIA SUN GINA JAMI'AR KIMIYA DA FASAHA

'YAN AREWA SUN KAFA TARIHI A YANKIN KUDU MASO KUDANCIN NIGERIA SUN GINA JAMI'AR KIMIYA DA FASAHA

Wannan shine hoton ginin katafariyar cibiya na horarwa a kan fasahar sadarwa wanda hukumar NITDA ta gina a cikin jami'ar jihar Rivers dake birnin Fatakwal, kwanaki biyu da suka gabata Maigirma Ministan sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami yaje ya kaddamar da cibiyar a madadin gwamnatin Nigeria.

Yayin Bude Makarantar Kimiya da Fasaha

Marubuci: Datti Assalafy

Abin farin ciki garemu masoya Malam Dr Isah Ali Ibrahim Pantami, shine mutum na farko da ya fara gina wannan katafariyar cibiya a tsakiyar kudu maso kudancin Nigeria, sannan sai amintaccensa wato Malam Kashif Inuwa yazo ya karasa, wannan wani abu ne na tarihi.

An yiwa cibiyar lakabi a turance da "The Information Technology Innovation and Incubation Park Building" an kashe miliyoyin Naira kafin a gina cibiyar, mutanen yankin kudu maso kudancin Nigeria gaba dayansu sune zasu amfana da cibiyar.

Maigirma Ministan sadarwa Dr Isah Ali Pantami a gurin kaddamar da cibiyar yace; lokacin da nake shugabancin hukumar NITDA, shugabanta na yanzu Kashif  Inuwa yana matsayin mai bani shawara akan harkokin gudanarwan ma'aikatar, na kawo batun gina irin wannan cibiya a kusurwa shida na fadin tarayyar Nigeria ta yanda za'a samarwa matasa aiki, a farfado da tattalin arzikin kasa.

Yayin Bude Makarantar Kimiya da Fasaha

Maigirma Ministan yayi la'akari da gurin da yafi dacewa a fara gina wannan cibiya saboda yawan masana'antu da yankin ke dashi, wanda zai inganta tattalin arzikin Nigeria, sai ya fara a yankin kudu maso kudancin Nigeria ba tare da la'akari da ya fara a yankinsa ba, saboda kyakkyawar manufa da kishin Nigeria.

Ministan yaci gaba da cewa, na tabbata idan aka gudanar da wannan cibiya bisa gaskiya da rikon amana yadda ya dace, cibiyar zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Nigeria, shugaban Kasa Buhari yayi alkawarin yin adalci a kowani sassa na Nigeria, shiyasa hukumar NITDA zata tabbatar da wannan muradi na shugaban kasa wajen gina irin wannan cibiya a kusurwa shida na fadin tarayyar Nigeria.., inji Ministan

A nasa jawabin, shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwan zamani na Nigeria (NITDA) Malam Kashif Inuwa  a gurin kaddamar da cibiyar, yace an gina wannan cibiyar ne a cikin jami'ar Portharcourt don daliban ilmi, manyan masana'antu da kanana, 'yan kasuwa da sauransu akan manufa na inganta tattalin arzikin Nigeria .

Malam Kashif Inuwa yaci gaba da cewa, gwamnatin tarayyar Nigeria karkashin shugabancin Muhammad Buhari tun a shekarar 2016 ta kafa kwamitin kwararru a harkokin kasuwanci da aka yiwa lakabi da "Presidential Enabling Business Environment Council" tare da taimakon bankin duniya (World Bank) domin kwamitin ya cimma matsaya akan abubuwa guda uku, na farko; a farfado da tattalin arzikin kasa, na biyu: a gina hanyoyin inganta tattalin arzikin kasa, sannan a gina al'umma.

Gwamnati ta fahimci cewa kimiyyar fasahar sadarwan zamani zai iya kawo mafita ga matsalolin tattalin arzikin kasa, shiyasa ta bada muhimmanci a kai, a sakamakon haka, yanzu bangaren bunkasa fasahar sadarwa a Nigeria ya wuce man fetur da gas wajen inganta tattalin arzikin kasa.., a cewar Malam Kashif Inuwa shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwan zamani na Nigeria (NITDA).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Kalli Yadda Soyayya ta sa Wani Bawan Allah ya Sauya Sunan Shi Zuwa na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Kalli Yadda Wani Dan Sanda Ya Harbi Wani Matashi Dalibin Computer Science Har Lahira

SHIN TA YA YA KAKE JIN MAGANAR DA WANI KE FURTAWA?

Ina kira ga 'yan uwana na arewacin Nigeria mu dinga sanya wadanann bayin Allah cikin addu'ah na fatan samun nasaransu, manufarsu mai kyau ce, babu shakka akan sun rike amanar da shugaba Buhari ya damka musu da gaskiya.

Muna rokon Allah Ya daukaka darajarsu, Ya sa dukkan jama'ar  Nigeria su amfana da rayuwarsu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Wednesday, 11 December 2019

Kalli Yadda Soyayya ta sa Wani Bawan Allah ya Sauya Sunan Shi Zuwa na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Kalli Yadda Soyayya ta sa Wani Bawan Allah ya Sauya Sunan Shi Zuwa na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Soyayyar da yakewa Shugaba Muhammadu Buhari ta sanyashi canza sunansa daga na asali wanda iyayensa suka saka masa zuwa sabon sunan Muhammadu Buhari a wannan rana.

So Hana Ganin Laifi...

Marubuci: Rabi'u Biyora 

Anyi babban bukin raɗa suna a jihar Kano, inda aka kawo Goro da alewa tare da gayyato malamin daya raɗa sabon sunan, sannan aka yanka Rago na sabon suna.

Inda Ranka.....

Haka dai rayuwar ke juyawa, kowa yana da 'yancin gabatar da yadda ya tsarawa kansa rayuwarsa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Kalli Yadda Wani Dan Sanda Ya Harbi Wani Matashi Dalibin Computer Science Har Lahira

DUK MAI HANKALI IDAN YA KARANTA JAWABIN SHUGABAN KASA BUHARI SAI YA ZUBDA HAWAYE

KARANTA ZAFAFAN SHAWARWARI 10 ZUWA GA SHUGABAN KASAR NIGERIA MUHAMMADU BUHARI

Idan ba'a ga laifin mai canza suna saboda adawa ba, ina ganin shima mai canzawa saboda soyayya bai kamata aga laifinsa, musammam idan abun daya aikata bai saɓa da ƙa'idojin addini ba.

ALLAH DA IKO YAKE......

Ka kyautawa kanka, musammam ma daka biyawa zuciyarka abun da takeso.