Saturday 4 August 2018

DUK MAI HANKALI IDAN YA KARANTA JAWABIN SHUGABAN KASA BUHARI SAI YA ZUBDA HAWAYE - KARANTA YANZU KAJI

Tura Wannan Zuwa
A ziyaran da shugaban Kasa Alhaji Muhammadu Buhari ya gabatar a Ranar Alhamis a garin Bauchin Yakubu masu tutiya da ayar Allah.

Shugaba Muhammadu Buhari

Marubuci: Datti Assalafiy

Shugaba Buhari yayi jawabai masu sosa rai dangane da makomar Kasarmu Nigeria da tsarin siyasar miyagun shugabanni 'yan jari hujja

Shugaba Buhari yace: "Allah Ya sani bisa kokarin tunanina shine in tabbatar na daura Nigeria kan mizanin da zakuyi alfahari da ita nan gaba.

Akwai wahala cikin kawo sauyi a Kasa , amma muna jureshi iyakar iyawar mu, ko makiya sun tabbatar mun dauki saiti kan makomar Kasar mu Nigeria, amma 'yan jari-hujja munyi musu laifin da bazasu yafe mana ba, laifin shine rufe musu kofofin sata, su ba damuwar su bane Nigeria ta kone ta babbake su sayar da tokanta su gudu .

Sun sako mu a gaba yanzu da dukkan karfinsu suna bukatar a kyalesu su wargaza 'dan abinda muka fara gyarawa.
Basa fatan alheri ko miskala-zarratin wa Nigeria da al'ummar ta

Ziyarar Shugaba Buhari a Jihar Bauchi

Babu wani zabi garemu, zabi yana gareku al'ummar Nigeria, idan kun gaskata kokarin mu ku sake zabanmu mu dora daga inda muka tsaya, hakan zai zama alheri gare ku, idan kuma kun karyatamu ku koma gare su ('Yan jari hujja) su lalata makomarku da Kasar ku.

Amma tabbas watarana zaku tuna na fada muku gaskiya, kuma na doraku akan gaskiya, kuma na rikeku da gaskiya, zabi nakune, kan makomar Kasarku ba batun siyasace a raina ba wallahi face makomar ku nan gaba.." ~Jawabin shugaban Kasa Muhammadu Buhari Hafizahullah

Alherin Allah Ya kai ga shugaba Buhari
Allah Ka tsare manashi daga dukkan sharri
Allah Ka daukaka darajarsa duniya da lahira
Allah Ka bashi dukkan nasara da yake nema
Allah Ka zama jagoransa Amin Summa Amin

Karanta Kaji: Ubangiji ba zai yafe min ba idan na mara wa Atiku baya a zaɓen 2019 – Cewar Obasanjo

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user