Saturday 7 December 2019

Kalli Yadda Wani Dan Sanda Ya Harbi Wani Matashi Dalibin Computer Science Har Lahira

Tura Wannan Zuwa
Sunan sa Mus'ab Sammani, ɗalibin ilimi wanda ya karanta Computer Science a kasar India, matashi ɗan jihar Kano mai zuciya cike da burikan samar da Ci gaba ga jihar Kano tare da al'ummar Kano.

Mus'ab Sammani

Marubuci: Rabi'u Biyora

A unguwar Niger Street dake jihar Kano, aka ce ɗan karamin saɓani ya shiga tsakaninsa da ɗan Sanda (Police) sai police ɗin ya ɗauki bindiga ya harbi Mus'ab wanda hakan ya janyo rasa rayuwar matashi Mus'ab. 

Tarin ilimin mus'ab tare da burikan sa na taimakawa al'umma ta hanyar ilimin da yake dashi, Police ya dakatar da hakan sakamakon ɗan karamin saɓani.

HAR NA TUNA DA KOLADE JOHNSON

Matashi Bayerabe ɗan jihar Lagos da Police suka harba har ya mutu, sai nan da nan hukumar 'yan sanda ta dauki tsattsauran mataki akan 'yan sandan dake da hannu a kisan, aka bayyana hotunan su da sunayen su a bainar Jama'a domin kowa ya gani, 

Kwamishinan 'yan sanda na lagos ya ziyarci gidan su Kolade, Matemakin shugaban ƙasa da kansa shima ya ziyarci gidansu kolade shima shugaban hukumar 'yan sanda na kasa sai da ya ziyarci gidan su kolade duk don a basu hakuri akan laifin da 'yan sanda sukayi na kashe kolade.

Yanzu an kashe Matashi Mus'ab Sammani a jihar Kano, matashi mai ilimi wanda zuciyar sa ke cike da burikan alheri.

MAKALOLI MASU ALAKA:
Muna fatan hukumar 'yan sandan jihar Kano zasu kwaikwayi kwatankwacin irin yadda hukumar 'yan sandan jihar lagos sukayi a wancan lokacin, su gudanar da bayanai a fili yadda kowanne ɗan jihar kano zai gani, idan da hali Kwamishinan 'yan sandan Kano ya ziyarci gidan iyayen Mus'ab ya jajanta musu.

Justice for Musa'ab

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user