Sunday 5 July 2020

Shin Dagaske Ne Dr. Isah Ali Pantami Ya Mallaki Manyan Gidaje A Birnin Tarayya?

Tura Wannan Zuwa Ga
Kafar watsa labarai ta yanar gizo (Sahara Reporters) ta wallafa labarin ƙarya ta na iƙirarin cewa wai "Ministan Sadarwa da tattalin arziƙin fasahar sadarwar zamani, Shaik, Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami ya sayi wasu gidaje guda uku tun bayan zamansa Minista".

Dr. Isah Ali Pantami

Marubuci:- Garba Tela Hadejia

Wannan labari ne na ƙanzon kurage da aka kitsa da manufar ɓata kima da darajar Minista Pantami, domin tun bayan zamansa Minista babu wani gida da ya saya a ko'ina a faɗin duniya.

Ɗaya daga cikin gidajen da aka wallafa a jaridar, Dakta Pantami ya mallake shi ne tun a cikin watan Janairu na shekarar 2017 sama da shekara biyu kafin ya zama minista. Ya yin da shi kuma ɗaya gidan ya kasance hayarsa ya karɓa tun a ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 2019. Biyu daga cikin hotunan kuwa ba shi da masaniya a kansu.

Gidajen Da Ake Yaɗawa...

A matsayin Dakta Pantami na minista, albashinsa da alawus-alawus ɗinsa bai kai abin da ya ke samu ba a matsayin Farfesa a Jami'ar musulunci ta ƙasa da ƙasa da ke Madina, saudi Arabia ba. Kuma har yau a tarihi shi kaɗai ne ɗan Nageriya na farko da ya koyar a wannan mataki. Ya dawo Nageriya ne da manufar ba da gudunmawarsa a gina ƙasa.

Gidajen Da Ake Yaɗawa...

Dakta Pantami na ɗaya daga cikin ƴan Nageriy ƙalilan da su ke sadaukarwa kan kishin ƙasa. Ɗan kasuwa ne da ya yi nasara tare da samun kykkyawar rayuwa. A nagarta irin ta Dakta Pantami mutum ne da ya ke yaƙi da rashawa da cin hanci a tsakanin gwamnati da al'umma ba a Nageriya kawai ba har ma duk duniya.

Gidajen Da Ake Yaɗawa...

Mu na fata jama'a za su yi watsi da duk wani yunƙuri na ɓata kima da darajar Minista Pantami, sannan kuma mu na fatan kafofin sadarwa a Nageriya za su riƙa samar da tsare-tsaren bin diddigin labari kamar yadda tsarin aikin jarida ya tanadar tare da gujewa labaran kanzo kurege domin kare martabar aikinsu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user