Tuesday 26 November 2019

KARANTA ABINDA YA KAMATA KU YI DA ZARAN ANYI GARKUWA DA 'YAN UWAN KU

Tura Wannan Zuwa Ga
1- Da zaran masu garkuwa da mutane sun kama 'dan uwanku, sannan suka kira waya don neman kudin fansa, kai da zaka tattauna da su ta waya ka nutsu sosai, kayi magana da su cikin fasaha da wayo, kar ka bayyana tashin hankalin da kuke ciki garesu.

Nemi Tsari da Sharrin Masu Garkuwa da Mutane

MarubuciDatti Assalafiy

2- Kayi kokarin jin muryan 'dan uwanka da akayi garkuwa dashi don ka tabbatar da cewa 'dan uwanka yana raye a hannun masu garkuwa da shi.

3- Da zaran masu garkuwa da 'dan uwanka sun bukaci adadin kudi naira kaza kar kayi saurin amincewa da adadin kudin, kayi kokarin bayyana musu wasu dalilai da zasu baka lokaci don ka yanke hukunci akan kudin da suka bukata.

4- Kar ka musu alkawari akan abinda ba zaka iya biya ba, yin hakan zai iya jefa rayuwar 'dan uwanka cikin hatsari na rasa rayuwarsa a hannun masu garkuwa dashi.

5- Idan masu garkuwa da 'dan uwanka sun takura akan lallai sai an biya kudi adadi kaza kafin su saki 'dan uwanka, to ka rokesu cikin salo na dabaru, ka fada musu cewa zaka nemi shawaran sauran 'yan uwa akan abinda suke bukata, sannan ka nuna musu cewa kudin nan fa da kuke bukata babu su tukunna.

6- Da zaran anyi garkuwa da 'dan uwanka kayi saurin kai rahoto zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa, ko hukuma na tsaro, sannan ka bukaci a hadaka da babban ofisa dake lura da ofishin jami'an tsaron ba tare da bata lokaci ba, domin zai fi fada maka abinda ya dace ayi .

Nemi Tsari da Sharrin Masu Garkuwa da Mutane

7- Da zaran ka kai rahoto zuwa ofishin 'yan sanda ko wata hukumar tsaro, kar kayi gaggawan bayyana abinda ya faru da 'dan uwanka ga al'ummah, saboda ta iya yiwuwa masu garkuwa da 'dan uwanka suna da 'yan leken asiri hatta a cikin 'yan uwanka, hakan zai iya jefa rayuwar 'dan uwanka cikin hatsari.

8- Bayyana bayanai ko hotuna na 'dan uwanka da akayi garkuwa da shi ta kafofin sada zumunta babu abinda hakan zai haifar mai kyau face tona asirin 'dan uwanka da jefa rayuwarsa cikin hatsari, kuma hakan zai bada wahala sosai wa 'yan sanda da sauran jami'an tsaro su iya kubutar dashi.

8- Ko da ka kai rahoton garkuwa da 'dan uwanka zuwa ofishin 'yan sanda ka bukaci lallai a hadaka da rundinar 'yan sanda kwararru a bangaren yaki da masu garkuwa da mutane "Anti-Kidnapping Unit" (AKU) ko rundinar 'yan sanda masu yaki da 'yan fashi da makami "Special Anti-Robbery Squad" (SARS) a matakin jihohi kenan, ko kuma rundinar 'yan sanda kwararru masu kaiwa agajin gaggawa wadanda suka hada da IGP Intelligence Response Team (IRT) IGP Special Tactical Squad (STS) a matakin tarayya kenan lura da girman matsalar.

10- Ka san cewa rundinar 'yan sanda kwararru wadanda suka hada da IGP-IRT, IGP-STS, AKU, F-SARS sune wadanda gwamnatin Nigeria ta basu horo na musamman akan yaki da masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami, ofisoshin 'yan sanda musamman a matakin kanana basu da isasshen horo da kuma yawan jami'an tsaro da zasu iya tunkarar masu garkuwa da mutane.

11- Idan wadanda sukayi garkuwa da 'dan uwanka suka nemi yin magana da 'yan uwanku dabam-dabam to kayi kokarin shirya wata dabara da kai kadai ne zakayi magana da su don kar a samu matsala.

12- Kar ka goge nambar waya, ko hiran da kayi da masu garkuwa da 'dan uwanka, saboda zai taimakawa jami'an tsaro masu bincike.

13 - Da zaran anyi garkuwa da 'dan uwanka, a kowani lokaci ka kasance mai neman shawaran kwararrun jami'an tsaro da suka kware a yaki da masu garkuwa da mutane kafin ka dauki kowani irin mataki, domin a duk lokacin da aka samu matsala tsakaninka da wadanda suke rike da 'dan uwanka zai iya jefa rayuwar 'dan uwanka cikin hatsari, kuma da zaran baka gamsu da jami'an tsaron da suke bibiyar halin da 'dan uwanka yake ciki ba, ka nemi ganawa da babbansu ba tare da bata lolaci ba.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KALLI YADDA DUBUN SHUGABAN MASU GARKUWA DA MUTANE TA CIKA A HANNUN ABBA KYARI... LATEST VIDEO

Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai da Harin da aka Kai a Matatar Man kasar Saudiyya - Shugaba Buhari

Karshen Duniya Kidnappers Sun Sato Yaro Aljani...Latest Video

Insha Allahu shafin Datti Assalafiy zai cigaba da wayar da kan jama'a akan matsalolin dake tattare da garkuwa da mutane, da yadda ake tattaunawa da su, da matakan da za'abi don a tsallake tarkon masu garkuwa da mutane.

Muna rokon Allah Ya tsaremu daga dukkan sharri da cin amana da zalunci Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user