Tuesday 26 November 2019

Karanta Addu'ar Kunutin Wutiri

Tura Wannan Zuwa Ga
اَللَّهُمَّ اِهْدِنِي فِيمَنْ هَدَيْتَ، وَعَافِنِي فِيمَنْ عَافَيْتَ، وَتَوَلَّنِي فِيمَنْ تَوَلَّيْتَ، وَبَارِكْ لِي فِيمَا أَعْطَيْتَ، وَقِنِي شَرَّ مَا قَضَيْتَ، فَإِنَّكَ تَقْضِي وَلاَ يُقْضِى عَلَيْكَ، إِنَّهُ لاَيَذِلُّ مَنْ وَالَيْتَ،[وَلاَ يَعِزُّ مَنْ عَادَيْتَ]، تَبَارَكْتَ رَبَّنَا وَتَعَالَيْتَ.

Allahummah-dinee feeman hadayt, wa'afinee feeman 'afayt, watawallanee feeman tawallayt, wabarik lee feema a'atayt, wakinee sharra ma kadayt, fa-innaka taqdee wala yuqda 'alayk, innahu la yathillu man walayt, [wala ya'izzu man 'adayt], tabarakta rabbana wata'alayt.

Yayin Addu'a

Ya Allah! Ka shirye ni cikin wadanda ka shiryar, ka amintar da ni daga mummuna cikin wadanda ka yi wa aminci daga mummuna, ka jibinci lamari na cikin wadanda ka jibinci lamarinsu, ka albarkance ni cikin abin da ka ba (ni), ka kiyashe ni sharrin abin da ka kaddara, domin kai ne kake hukunci, babu wanda yake hukunci a kanka. Tabbas wanda ka jibince shi ba zai wulakanta ba, wanda kuma ka ki shi ba zai daukaka ba. Alherinka ya yawaita, ya ubangijinmu! Kuma ka daukaka.

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِرِضَاكَ مِنْ سَخَطِكَ، وَبِمُعَافَاتِكَ مِنْ عُقُوبَتِكَ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْكَ، لاَ أُحْصِي ثَنَاءً عَلَيْكَ، أَنْتَ كَمَا أَثْنَيْتَ عَلَى نَفْسِِكَ.

Allahumma innee a'oothu biridaka min sakhatik, wabimu'afatika min 'uqoobatik, wa-a'oothu bika mink, la ohsee thana-an 'alayk, anta kama athnayta 'ala nafsik.

Ya Allah! Ina neman tsari da yardarka daga fushinka, da kuma rangwamenka daga ukubarka, kuma ina neman tsari da kai daga gare ka. Ban isa in tuke ga yabo mai cancanta gare ka ba; kai dai kamar yadda ka yabi kanka ne.

اَللَّهُمَّ إِيَّاكَ نَعْبُدْ، وَلَكَ نُصَلِّي وَنَسْجُدُ، وَإِلَيْكَ نَسْعَى وَنَحْفِدُ، نَرْجُو رَحْمَتَكَ، وَنَخْشَى عَذَابَكَ، إِنَّ عَذَابَكَ بِالْكَافِرِينَ مُلْحَقٌ. اَللَّهُمَّ إِنَّا نَسْتَعِينُكَ وَنَسْتَغْفِرُكَ، وَنُثْنِي عَلَيْكَ الْخَيْرَ، وَلاَ نَكْفُرُكَ، وَنُؤْمِنُ بِكَ، وَنَخْضَعُ لَكَ وَنَخْلَعُ مَنْ يَكْفُرُكَ.

Allahumma iyyaka na'bud, walaka nusallee wanasjud, wa-ilayka nas'a wanahfid, narjoo rahmatak, wanakhsha 'azabak, inna 'azabaka bilkafireena mulhak. Allahumma inna nasta'eenuk, wanastaghfiruk, wanuthnee 'alaykal- khayr, wala nakfuruk, wanu'minu bik, wanakhda'u lak wanakhla'u man yakfuruk.

Ya Allah! Kai kadai muke bautawa, kuma gare ka kadai muke sallah, muke sujada, kuma gare ka kadai muke kokari muke gaugawa wajen aiki. Muna kaunar rahamarka, kuma muna jin tsoron azabarka. Lallai azabarka mai riskar kafirai ce.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Zikirin Safiya da Maraice

Karanta Addu'a Ga Wanda ya Razana a cikin Bacci Da Wanda Ya Kasa Yin Bacci

Karanta Yadda ake Yin Addu'ar Sallar Istihara Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai Aikata Wani Abu

Ya Allah! Muna neman taimakonka, kuma muna neman gafararka, kuma muna yabon alheri a gare ka; ba ma kafirce maka, kuma muna imani da kai, muna kaskan da kai gare ka, kuma muna yarbe wanda yake kafirce maka.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user