Sunday 26 January 2020

ABINDA YAFARU A DARAN JIYA NI DA MATA TA

Tura Wannan Zuwa
A Jiya na dawo gida a gajiye. Sai na gayawa mata ta cewa zan canza tufafina sannan in ɗan kwanta in huta kafin ta gama abinci.

Guziri ga Matafiyi..

Haka naje na canza kayana sannan na kwanta a kan gado na rufe ida nuna.

Ban buɗe idanuwana ba har saida aka kira Sallar La'asar.

Sai na tashi na fito daga Ɗaki na doshi inda mata ta take dafa abinci, ina ƙarasawa gurin sai naga matata sai jera abinci takeyi akan teburi.

Sai na zauna akan tebur sannan na tambayeta me kika dafamana ne? Rabin zuciyata. Naga tayi shiru.

Sannan na ƙara tambayarta me kika dafamana ne!. Rabin zuciyata.

Amma sai tayi shiru ba tace mini komai ba, sai na ƙara tambayarta a karo na uku da karo na huɗu., amma sai naga tayi shiru batace komai ba.

Sai raina ya ɓaci. Amma sai na tina cewa yau shekarar mu ashirin muna rayuwa a tare. Amma ban taɓa kiranta taƙi amsawa ba.

Sai na waiwaya inda ɗana yake zaune sai nace masa yaje firij ya kawo mini ruwa a kofi, amma sai naga shima yayi shiru ya ƙyaleni. Sai abin ya bani mamaki.

Sai na tashi da niyyar fita daga ɗakin girkin., kawai sai naji matata ta gayama ɗana cewa yaje ɗaki ya taso babansa daga bacci. Sai naji hankalina ya tashi.

Haka ɗana yaje ɗakina don ya tasheni daga bacci, sai na ɗaga muryata nace masa gani anan, amma ko waiwayowa baiyiba.

Haka ya doshi ɗakina a guje don ya taso ni.

Bayan kamar minti ɗaya sai ya dawo a firgice.

Sai babarsa ta tambayeshi, Shin ka tasoshi ne?

Sai yace: nayi-nayi amma yaƙi tashi..

Sai matata ta tafi ɗakina da sauri ɗana yabita a baya.

Sai na bisu don inga yadda zasu tasoni daga bacci.

Sai naga sunata ƙoƙarin tashin wani mutum mai kama dani da yake kwance akan gado na.

Kuma mutumin ya sanya tufafina.

Da taga ta kasa tashinsa daga bacci, kawai sai hawaye ya riƙa fitowa daga idonta. Sai naga ita da 'ya'yana sunata kuka.

Sai naga abin kamar a mafarki.

Yaah Ila'hee, wai me yake faruwa ne?

Waye wancan mutumin mai kama da Ni?

Me yasa inayin magana basaji?

Me yasa basa ganina????

Sai ɗana ya fita da sauri.

Can sai naga ya dawo. shi da Babana da babata da wasu 'yan uwana, dukkanninsu sunata kuka.

Babata ta riƙa rungume wannan mutumin mai kamannina.

Sai naje wajenta na riƙa ƙoƙarin taɓata da yi mata magana, amma abu ya faskara, sai na juya wajen babana da 'yan uwana amma sai naga basa jin muryata.

Sai naji 'yan uwana suna maganar ayi mini jana'iza.

Sai mai yin wankan gawa yazo ya riƙa wanke wannan mutumin mai kama dani da yake kwance a ɗaki na.

'Ya'yana suka taimaka masa aka wanke mutumin aka sanya masa likkafani aka ɗaurashi akan makarah.

Abokaina da Masoyana suka cika gidan mu suna yima babana da 'yan uwana gaisuwar makoki.

Sannan suka ɗauki makarar suka kaita Masallaci, kowa ya fita daga gidan mata kawai aka bari.

Sai nayi sauri na fita na nufi masallaci na iske makwabtana da abokaina sunyi sahu a bayan liman.

Haka na riƙa ratsa dandazon masu Sallah ba tareda na taɓa kowa ba.

Limami yayi Kabbara ta ɗaya.

Ni kuma ina tayi musu ihu, ina cewa "Wai wa kuke salla ta?

Ganinan a atare daku. Bakwa gani ne!!!

Magana nake muku ko ba kwajina ne?

Alokacin da na fitar da rai cewa zasu kula ni, sai na ƙyalesu suka riƙa sallar su.

Ni kuma na nufi inda makara take, na cire likkafanin don inga fuskarsa.

Kawai sai naga ya buɗe idanunsa
yace mini "Ni na gama aikina". Kai kuma har abada kaine zaka riƙa yin komai da kanka.

Domin adah atare mukeyin komai har tsawon shekaru 40.

Amma yanzu ni ƙasah zan zama. Kai kuma hisabi za'a maka.

Ban ankara ba sai jina nayi akan makara, kuma gaɓɓaina sun kasa motsi.Banda ƙarfin yin motsi.

Haka suka binne Ni sukai tafiyarsu.

Tun inajin motsin takalmansu har na daina.

A wannan lokacin ne na fahimci cewa ƙarshena yazo.

Sai na fara tinanin yadda mutuwa tazo mini bagatatan, alhalin ayyuka sunyi mini yawa kuma akwai alƙawarurrukan da ban cika ba.

Kuma akwai waɗanda suke bina bashi kuma ban rubuta ba.

Ban gayama kowa ba. Banyi wasiyya ba.

To yaya zanyi ?

Gashi inaso inyi umarni da kyakkyawa kuma inyi hani da mummuna. Ina cikin wannan tinanin ne naji alamar ana tafiya an doso inda nake.

Babu makawa Munkaran da Nakiyr ne suka taho inda nake.

Sai na fara ihu ina cewa:

Ya Allah a mayar dani duniya.

A mayar dani duniya!

A mayar dani duniya!

A mayar dani duniya!

Domin in aikata aikin alheri.

Haka nayita faɗi har muryata ta disaashe.

Amma aduk lokacin da nace a mayar dani. Sai inji wata murya tana cewa Inah-Inah. Ai lokaci yazo ƙarshe.

Sai naji wata murya a kusa da kunnena ana ce mini Baba! Baba! Baba!

Ina buɗe ido sai naga ashe wata 'yatace take tashina daga bacci.

Nanfa nayi ajiyar zuciya nayi murmushi.

Na godema Allah (S.W.T) Sai na zauna akan katifa gumi nata fitowa daga jikina zuciyata tana bugawa da ƙarfi.

Nanfa na fara tunanin ayyukan alherin da ya kamata in fara aikatawa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

ABOKAI IRI UKU NE A DUK FADIN DUNIYA

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa Cikin Sauki

KARANTA NASIHOHI GUDA 10 GA 'YAN UWANA MATASA

Don haka 'yan uwa kuyi saurin aikata aikin alheri domin rai batasan abinda zai faru a gareta ba gobe, kuma batasan a inda zata mutu ba.

Tace rubutu da kuma tsarawa wakilin Muryar Hausa24 Online Media, don bunƙasa harshen Hausa a Sassan Duniya.

Ya Allah kabamu ikon aikata alkhairi da hani da mummuna.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Source: Rayuwa A Musulinci
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user