Saturday 25 January 2020

KARANTA NASIHOHI GUDA 10 GA 'YAN UWANA MATASA

Tura Wannan Zuwa
Duba da yanayin rayuwar Matasan Mu a yau, wannan dalilin yasa zanyi Nasiha ga 'yan Uwana Matasa dangane da abinda ya shafe mu Ni da Ku.

Matasa sune ƙashin bayan kowacce irin al'umma..

Marubuci: Safwan Umar Yahya

1. Ka mu'amalanci mutane da mu'amala mai kyau, kada ka yaudare su, ka ha'ince su ko ka ci amanar su bayan sun yarda da kai.

2. Ka zama mai gaskiya wanda baya saɓawa abin da ya faɗa, wato idan zaka yi zance ka yi adalci, kuma kada ka zama mai sassaɓa zancenka a kowani lokaci.

3. Kada ka riƙa yi wa mutane ƙarya, domin kuwa Hausawa suna cewa "Karya fure take bata 'ya'ya"

4. Ka zama mai amfanar da jama'a ta kowani bangare na abin da Allaah ya azurtaka da shi; Ilmi, kuɗi, sarauta, mulki, sana'a ko kasuwanci.

5. Kada ka keɓe iyalanka kaɗai ka ce su kaɗai ne naka, in ban da su babu wanda ya isa ya ci dukiyar ka, shin ba ka san mabuƙata suna da hakki a kan dukiyar ka ba ne? Kana kwana da abinci ko kana cin duk abin da ka yi niyya ga makwabtanka nan da 'yan uwanka suna kwana da yunwa.

6. Idan mutuwa ta zo maka ba zata ce ka yi maza ka kashe duk abin da ka tara ba, ko kuma a haɗa ka da dukiyar ka a birne ka da ita tare ba, shin ko ka taɓa jin labarin wani sahabi da ya bar wasici da a bayar da gonarsa wacce take cike da kayan marmari, lokacin da Manzon Allaah (S.A.W) ya je gonar ya ga dabino guda ɗaya ya faɗo ya ɗauka ya ce "Wannan dabinon ya fi masa alheri ya yi kyauta da shi a lokacin da yake raye fiye da ya bar wasiycin wannan gonar!".

7. Yanzu ba zaka hankalta ba? Shin ko kana tunanin dukiyar da Allaah ya baka dabararka ce da wayonka ya sa a baka ita ko kuma ya fi son ka ne shi ya sa ya baka ita ya hana wasu mutanen?

8. Talaka zai riga mai kuɗi shiga Aljannah da shekara ɗari biyar, za a tsare mai kuɗi ya yi bayanin duk hanyar da ya samo kuɗinsa da hanyar da ya bi ya kashe su, lokacin da ake yi masa tambayar zai riƙa yin zufa wacce da raƙuma ɗari za su ci kaikayi ba za su iya shanye shi ba. Lokacin da talakawa suka ji wannan labarin daga bakin Manzon Allaah (S.A.W) suka yi farin ciki har wasu suke tambayar ko suna daga cikin talakawan? Karshe dai wanda ya zama daga cikin talakawan shi ne; wanda bashi da cin yau da na gobe, kayansa kala ɗaya ne, idan ya nemi bashi a wajen mutane ba za su bashi ba kuma idan ya fita neman kuɗi da ƙyar yake samu wani lokacin ma baya samu, amma duk da haka yana wuni yana mai godiya ga Allaah (S.W.T).

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA INGANTACCIYAR HANYAR YIN MU'AMALA DA MUTANE

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa Cikin Sauki

Shin Zan Iya Zama Sanadin Shiriyar Abokina?

9. Matuƙar kana son wani abu na Duniya ko na Lahira, ka nema a wajen Allaah, shi ne kaɗai wanda zai iya baka, kada ka je kana yin maula da neman taimakon wani koma bayan Allaah.

10. Idan zaka so mutum ka so shi don Allaah, haka ma idan zaka ƙi shi ka ƙi shi don Allaah, da wannan nake baka shawarar nisantar abota da mutanen banza, lallai su suna kai duk wanda suke abota da shi zuwa halaka.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user