Sunday 20 September 2020

Kalli Abinda Dole Ne Ya Sa Ku Yin Kuka | Kai Rayuwa | Kai Duniya | Taron Karshe Na Marigayi Dr. Shehu Idris Sarkin Birnin Zazzau

Tura Wannan Zuwa Ga
A yau lahadi ne Allah yayiwa Sarkin Birnin Zazzau Alh. Shehu Idris rasuwa, an yi jana'izar sa da misalin ƙarfe biyar na yammaci yau.


MUTUWA ƘARAR KWANA

Idan ba zaku manta ba, a cikin wannan shekarar da muke ciki (2020) ne aka yi bikin cikar shekaru arba'in da biyar da hayewan marigayi HRH. Shehu Idris kan  karagar mulkin birnin Zazzau.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye...

Ya rasu yana da shekaru tamanin da huɗu a duniya, wanda yayi dai-dai da watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin (20/02/1936 zuwa 20/09/2020).

MURYAR HAUSA24 muna fatan Allah ya haskaka makwancinsa, yasa mutuwa hutu ce a gare sa, ya kuma sanya Aljannah Firdausi ta kasance masaukin sa na ƙarshe, mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da kuma Imani Amin Ya Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user