Thursday 17 September 2020

Nafi Kowa Murnar Mutuwar Lil Ameer - Malam Shu'aibu Salihu Zaria

Tura Wannan Zuwa

A lokacin da naga Duniyar Social Media ta dau ɗumin bada labarin mutuwar wannan yaro, nan
take na fara bincike kan rayuwar sa.


LIL AMEER

Abinda bincikena ya tabbatar min shine: Wannan yaro mawaki ne wanda ake mishi take da ‘Dan Autan Mawaka.

Nayi takaici matuka da naga wannan bayani, ace yaron da alama ke nuna bai balaga ba, dan
musulmai a Arewacin Nigeria ya zama mawaki irin mawakan turawa har ya shahara a duniya, wallahi wannan abun bakin ciki ne ga al’ummarmu.



LIL AMEER


Domin inada tabbas da yayi tsawon
rayuwa, to da yayi rayuwa mara anfani ga
al’umma.


Lil Ameer Da Mahaifiyarsa


Amma da yake Allah Ra’ufur Rahim ne sai ya ɗauki rayuwarsa tun gabanin ya balaga, gabanin
shari’a ta hau kan sa.


LIL AMEER

Ina rokon Allah ya gafarta masa yasa Aljannah
makomarsa da mu baki daya. Allah ka tsare
mana zuriyarmu daga tanbadewa Ameen.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: Hausa tricks
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user