Tuesday 4 February 2020

Hauwa Yunusa Kyakkyawar Bafulatanar Da Ta Jefa Kanta Cikin Harkar Garkuwa Da Mutane

Tura Wannan Zuwa Ga
Hauwa 'yar shekaru 24 kacal, amma ƙwararriya ce wajen fashi da makami, garkuwa da mutane da aikata kisa. Ta yi aure sau uku, tana rabuwa da mazajen saboda rashin jin maganarta.


Karshen Duniya...

Marubuci: Sa'eed Usman Assalafy

'Yar asalin ƙabilar Fulani ce wacce take zaune a garin Masaƙa dake jihar Nassarawa amma haifaffiyar jihar Jigawa.

Ita ta shirya yadda aka yi garkuwa da samarinta guda uku, inda suka biya kuɗin fansa. Saurayinta na farko ya bada miliyan biyu bayan da aka ba ta dubu ɗari biyu, bayan ya kwashe kwana biyu a hannun abokan aikata laifin nata, shi kuma na biyu ya biya miliyan ɗaya, inda aka ba ta naira dubu hamsin, na ukun kuma ya bada dubu ɗari biyar saboda a cewar ta shi ba mai kuɗi bane.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye..

Duk waɗan nan kuɗaɗe basu ishe ta ba, hakan ya sa ta haɗa baki da abokan ta'addancinta suka sace ƙawar ta mai suna Zainab saboda ta ji abokiyar tata tana faɗin cewa an turo mata da kuɗi har N600,000.

A dalilin wannan Zainab ta rasa ranta saboda tsantsan wahala da ta sha, sai Hauwa ta je ɗakinta ta dauki ATM din Zainab da nufin ta kwashe duk kuɗin dake cikin asusun ta, sannan ta sauya wa motar Zainab fenti sannan ta sayar da ita, kazalika ta sayar da dukkannin kayayyakin da marigayiya Zainab ta mallaka.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ABU BIYU NE KAWAI ZAKA IYA YI IDAN KA HADU DA WANDA YAFI KARFIN KA

KARANTA ABINDA YA KAMATA KU YI DA ZARAN ANYI GARKUWA DA 'YAN UWAN KU

MARYAM SANDA SHARI’AR ALLAH TA’ALA KO CONSTITUTION??

Hauwa dai a halin yanzu ta shiga hannu kuma ƴan sanda tun farkon shekarar da ta gabata, suna gudanar da bincike a kanta.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user