Lokacin da jirgin fataken ya fashe a tsakiyar teku, sai Allah ya yi wa ɗaya daga cikinsu gyaɗar dogo, ya riƙi wani ɓalgace na jirgin, iska ya yi ta ingiza shi, har ya kai shi bakin gaɓar wani tsibiri. Falke ya yi godiya ga Allah da ya kuɓutar da shi daga halaka.
Marubuci: Bukar Mada
Ya zauna a wannan wuri, kullum yana roƙon Allah ya koro wani jirgin da zai fitar da shi daga wannan tsibiri. Wasa-wasa dai ya share watanni da yawa, babu jirgi babu alamunsa. Ya haƙa 'yar bukka wadda yake kwana ciki, kullum kuma sai ya fita neman abinci. Wani lokaci ya farauto ƙananan dabbobi irinsu zomo, kurege da batsiya, wani lokaci kuma ya yi su, ya kama kifi. Yana nan haka har ya fara sabawa, kullum kuwa yana kan addu'ar Allah ya fitar da shi wannan tsibiri. Tun yana tsammani Allah zai karɓi addu'arsa, har ya fara ɗebe tsammani.
Ran nan ya dawo daga neman abinci, sai ya tarar da 'yar bukkarsa na ci da wuta bal bal bal, hayaƙi kuwa ya turniƙe ya yi sama. Duk 'yan tarkacen da ya tara ciki suka ƙone, ban da suturar jikinsa bai tsira da komai ba. Nan take sai ya harzuƙa, Shaiɗan ya shiga zuciyarsa ya fara yi masa kururuwa.
Falke ya ɗaga kai sama yana faɗin, "Allah laifin me na yi maka? Wata da watanni ina roƙon ka fisshe ni daga wannan wuri, babu wanda ka turo domin ya taimake ni. Ga shi kuma yanzu duk ɗan abin da na tanada a wannan wuri ya ƙone." Ya durƙusa a kan gwiwowinsa yana mai baƙin ciki, gayar baƙin ciki.
Yana cikin wannan hali sai ya hango wani abu daga nesa a kan ruwa kamar jirgi. Ya murje idonsa ya sake murjewa, ya ƙura wa abun nan ido. Da ya matso kusa sai ya ga lalle dai jirgi ne har da mutane ciki. Nan take zuciyarsa ta yi fari, ya manta da halin da yake ciki.
Da masu jirgi suka iso wurin shi, suka tambaye shi labarinsa, ya kwashe duk ya gaya musu. Suka ɗauke shi suka juya. Bayan sun miƙa cikin teku sai ya tambaye su yadda aka yi suka san yana wurin. Sai shugabansu ya ce hayaƙi suka hango daga nesa yana tashi, sun kuwa san duk inda hayaƙi yake to akwai mutum a wurin.
Falke ya yi wa Allah godiya, ya kuma nemi gafararsa a kan izgilin da ya tashi yi da fari. Ashe Allah ya yi nufin kuɓutar da shi ne, shi ya sa 'yar bukkarsa ta kama da wuta, hayaƙin nan da ya tashi sama shi ya jawo hankalin masu jirgin da ke wucewa, suka zo suka cece shi.
Komai yana da dalili. Abin duk da Allah ya yi, yana da dalilin yin shi, sai dai mutum ya kasa fahimtar dalilin.