Friday 19 April 2019

KARANTA KA JI : MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA KASHI NA GOMA

Tura Wannan Zuwa Ga
Domin taimaka wa dalibai masu nazarin harshen Hausa, da kuma masu so rubutunsu ya yi ma'ana da saukin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.






Darasi Na 10

WASU KALMOMI MASU RIKITARWA

Akwai wasu kalmomi da sukan rikitar yayin rubuta su, inda galibi akan rubuta su haɗe a koyaushe, duk da kasancewar a maganar baka ba a siga guda akan furta su ba, domin kalmomi biyu ne masu mabambantan ma’anoni.

Wasu daga cikin irin waɗannan kalmomi su ne:


1. sa’a da sa a
Kalma ta farko (sa’a), suna ne da ke nufin neman dacewa, ko sunan mace wanda ke nufin “Sa’adatu” a taƙaice.

Don haka a haɗe ake rubuta ta.

Misali:

ya nemi sa’a wajen Malam
Sa’a ta tafi ƙauye
Kalma ta biyu kuwa (sa a), aikatau ne mai gaɓa ɗaya (sa, wato sanya), sai lamirin lokaci na umarni ko bayanau na hali da kan biyo bayan aikatau ɗin.

Kalmomi biyu ne ke nan, don haka a rabe ake rubuta su.


Misali:


na sa a dubo mutumin

Ladi aka sa a lalle

2. ba’a da ba a
Kalma ta farko (ba’a), suna ne da ke nuna faɗar aibun mutum ta hanyar ambaton wata siffa tasa a kaikaice ko kai tsaye.

Kasancewarta kalma guda, a haɗe ake rubuta ta.

Misali:

abin ma na ba’a ne?

yana ta yi wa mutane ba’a ana dariya
Ita kuwa kalma ta biyu (ba a), kalmar korewa ce (ba) tare da lamirin suna majahuli na lokaci mai ci.

Don haka a rabe ake rubuta su.

Misali:

ba a shiga gidan

da ya dawo ba a nan ya sauka ba



Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah.

Wannan wani sabon darasi ne da
Waziri Aku tare da haɗin gwiwar Shafin Muryar Hausa24 su ka ɗauki nauyin kawowa 'yan uwa ɗalibai masu yin nazarin harshen Hausa da kuma masu son koyon ƙa'idojin rubutun harshenl Hausa domin rubutunsu ya yi ma'ana da sauƙin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.

A lura da haƙƙin mallaka wajen kwafin ɗin rubutu, darasin zai rika zuwa muku duk ranar Juma'a, daidai wannan lokaci, tare da taimakon Malam Nasir G. Ahmad .


KARANTA KAJI : MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA KASHI NA TARA


Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com

Mungode .




Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user