Saturday 30 September 2017

5. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa

Sai kuma aka kira na biyu. Alhassan ya ce masa. “Kai wane ne? Wace sana'a ka ke yi ?" Na biyun ya ce, “Ni Alkali ne matalauci.” Alhassan ya ce, “In kai matalauci ne, me ya sa ka ke kwance a gado mai kyau ? In ka yi mini karya yanzu zan sa a sare wuyanka. Ce kai mai arziki ne.”

Ya ce, “Ni Alkalin Galadoun ne. Gwamnan Isfahan ne ya yiwo kirana, don a bincika maganar kudin hayan kauyen da na ke ciki.” Alhassan ya ce, “Ina kudin hayan ?" Ya ce, “Shi ne na zo in ce ba ni da kudin, don fari sun bata mini duk amfanin gonata, kuma an yi karancin ruwa." Aka yi ta bugawa dai har aka ce in dai shi Alkalin kirki ne, laIle mutanensa za su fanshe shi da kudi masu yawa.

Aka kira na ukun kuma aka yi masa tambayoyi kamar yadda aka yi wa wadannan. Shi kuma ya ce shi bawa ne. Tun da aka fara bugunsa sai ya hakura ya ce shi dan kasuwa ne. Ni kuwa da ganinsa na san lalle gaskiya ce ya ke fadi da ya ce shi bawa ne. Ai da na bude baki na fadi haka, kada ka so ka ji bakaken maganganun da aka yi mini. Aka ce muddin na sake fada, to, za a maishe ni bawa kamar da. Shiru! Na kame bakina, na bar su su yi abin da suka ga dama.

Da dai Barayin nan suka ga ba za su sami wata riba game da mutanen nan uku ba, sai aka Shiga shawarar yadda za a yi da su. Wadansu suka ce a kashe mawaƙin nan da bawa a bar Alkali. Wadansu suka ce a bar Alkalin don a fanshe shi, a sa bawan nan bauta. Dukansu suka yarda da a kashe mawaki. Da na dubi mawakin na ga irin halinsa sai tausayi ya kama ni. Da na ga am matsa a kashe shi, sai na ce, “Wace irin wauta ku ke son yi? Ashe ba ku sani ba mawaka sau da yawa su kan yi arziki, in kuma sun ga dama su kasance masu arziki har abada? Ko kun manta da labarin nan na wani Sarki wanda ya ba wani shahararren mawaki zinariya da yawa ga ko wane baiti da ya yi? Wa ma ya sani, watakila ma mawakin Sarkin ne wannan?"
Sai wani ya ce, “In haka ne, bari ya yi mana wadansu baitoci yanzun nan, in ko wane baiti bai ci zinariya da yawa ba, za mu kashe shi." Nan da nan baki daya aka dauka, “Yi mana waka yanzu, in ka ki mu kashe ka.” Aka dai yi shawarar a bar su duka uku, a kai su can tsaunukan Kifcak, inda mu ke, da zarar an raba ganimar da muka samo.

Bayan an gama wannan hargitsin, kura ta kwanta, Alhassan ya tara mu duka, ya ce kowa ya kawo abin da ya sato. Wadansu suka fito da jakankunan azurfa, wadansu kuma na zinariya. Ga lofe tuli na zinariya, ga kwanonin zinariya, kai, kaya dai barkatai. Da aka kawo kaina sai na fito da jakar kudin nan. Da gani sai aka dauka gaba daya ana yabona. Muryar Alhassan ita ta fi amo. Ya ce, “Ya Alhaji, dana, na rantse har da raina da rawanin ubana ka yi jaruntaka. Im mun koma gida zam ba ka daya daga cikin barorina mata ta zama matarka, ka zauna tare da mu. Zam ba ka gida na kanka, da raguna ashirin mu yi bikin aurenka.”
Wadannan maganganu suka sake karfafa ni cikin niyyar da na yi ta da zarar na sami sarari zan gudu. Amma a lokacin nan na fi mayad da rai ga samun rabona na ganima, don na yi zaton an samu da yawa. Ayya, ina gani suna rabo, amma ko anini ba a ba ni ba. Na fa tsaya kiri da muzu sai am ba ni nawa rabon, amma ina! Sai ji na ke, “In ka kara yin maganan yanzu ma fille maka kai." Ai tilas na hakura da £30 din nan da ke gare ni tun farko. Ba kuwa wanda ya san ina da su. Sa'an nan ’yan’uwana kuma kowa sai kokarin ya sami nasa rabon ya ke yi. Abu dai ya kai har ga buge-buge da mare-mare, kisa ne kadai ba a yi ba. Shi ma dai an kusa a yi shi da ba domin wani ya ce, “Me ya sa mu ke fada haka, ga shi muna da Alkali a nan? Bari ya raba mana gardama.”
Nan da nan aka turo keyar Alkali ya zo ya tsaya a tsakiya, aka sa shi ya raba kayan tsakaninsu. A cikin kayan kuma har da na Alkalin, yana ganinsu ya raba ba damar cewa ko uffan. Da ya kare aka sake tasa keyarsa cikin ’yan’uwan kamunsa. ko ladar rabo bai samu ba.

Bayan an gama kici-kicin rabon kayan sata, sai muka dunguma duk da bayimmu zuwa gida ta hanyar da muka bi da. Ko da ma na ce tun da na ga mawakin nan na san shi mutum ne mai girma. Na yi iyakar kokarina aka sa ni in lura da shi a wannan tafiya. Duk cikinsu ba wanda ya ji harshemmu, don haka muka yi ta surutammu ba wanda ya san abin da mu ke cewa. Na fada masa yadda aka yi na shiga irin wannan hali, ya kuwa yi murna, don bai yi zaton zai sami aboki haka ba. Garin maganarmu ne na gane ashe shi Sarkin Mawaka ne. Ya fito daga Shiraz ne zai tafi Tehran, a ran nan ya isa Isfahan. Bayan na fada masa duk labarina, na tambaye shi ya ba ni nasa. Ga abin da ya ce :
“An haife ni a Kerman, sunana kuma Asker. Tun zamanin Aga Mohammed Shah ubana shi ne Gwamnan kasan nan. Makiyansa da yawa sun yi ta kokarin a tube shi, amma abu ya ki. Sai daga baya dai ya mutu cikin kwanciyar rai. Aka yardam mini in gaji dukan abin da ya ke da shi, jimla duka wajen jaka saba'in. Tun ina yaro na ba da himma ga neman ilmi, sa'ad da na cika shekara 16 na shahara ga yin rubutu. Na iya hafiz da ka. Ba fannin da ban gwada iyakar kokarina ba. Har na rubuta littafin waka. Ko ina kuwa na shiga sai in rera wakar
“A wannan lokacin Sarki yana yaki da Sadik Khan, wanda ya ce shi ne Sarki. Sarki da kansa ya zama shugaba a wannan yaki, aka kuwa sami nasara bisa Sadik Khan. Da karewar yaki sai na wake Sarki, na yi ta yabonsa. Aka kuwa kwashe labarin aka fada wa Sarki. Sarkin kuwa ya ba ni daraja mai girma wad da a ke bai wa mawaka. Watau ya sa aka cika bakina da kudin zinariya a gaban majalisarsa da gaban jama’a. Yin wannan ya sa na sami girma, aka ce in shiga cikin majalisa in rika rubuta baitoci ko wane lokaci.

Na ce wa Sarki tun da ya ke an rigaya an rubuta Tarihin Sarakuna zai dace in rubuta Tarihin Sarkin Sarakuna, don Farisa ba ta taba yin wani kasaitaccen Sarki kamarsa ba. Sarki kuwa ya ba ni iznin in rubuta wannan littafi.
“Babban makiyina a cikin Majalisar Sarki, shi ne ma’aji.

Shi ne ba wani kwakkwaran dalili ya ce im biya tarar jaka tamanin da hudu, Sarki kuwa bai yarda ba. Wata rana ana cikin tadi a majalisa, sai aka yi maganar kyautar da Sarki Mahmud Shah ya bai wa wani mawaki. Aka ce wannan Sarki ya ba da zinariya da yawa ga wannan mawaki ga ko wane baiti da ya yi.

Da na ji haka na ce kyautar wannan Sarki ma za ta fi, don kuwa ita waccan kyautar am ba da ita ne ga shahararren mawaki a Farisa, amma wannan za a yi ta ne ga mawaki matalauci.

“Daga nan sai majalisa suka kosa su ji yadda na sami wannan daraja. Na ce musu, ‘Da farko dai ubana ya mutu ya bar mini gadon jaka saba'in, Sarki kuwa ya yarda in ci gadon. Da yana so da ya rike. Kuma ga shi ma’aji yana son ya ci ni tarar jaka tamanin da hud’u, Sarki bai yarda ba.’ Na dai yi ta yabon Sarki, aka kuwa kwashe aka fada masa. Shi kuma ya ba ni rigunan daraja, da kwat da 'yar ciki da hula da alkyabba. Sa'an nan kuma ya ce ni ne Sarkin Mawaka. Ga al’ada kuwa a kan sa wannan hula har kwana uku ba fashi, don mutane su yabe ni. Na kuwa sa.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: