Sunday 29 October 2017

10. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa

A nan Sufi Sefer ya kare Iabarinsa, ya ce kuma
dayan ya ci gaba da ba da nasa. Shi kuma ya
kama, ya ce, "Ubana shahararre ne game da
shari'a a Birnin Kom. Duk cikin Farisa ba a taba
wani wanda ya fi shi wajen rashin fashin yin
salla da azumi ba.

A takaice dai, shi cikakken
Musulmi ne abin kwaikwayo. Yana da ’ya’ya da
yawa, dukammu kuwa an goye mu da tsananin
kiyaye addinimmu. Da muka ga an tsananta
mana sai muka yi dabarar kubcewa, muka shiga
shashanci. Darajar mu wadda a ke ganimmu da
ita ta bata, aka kuwa ce mu ne cikakkun
makaryata da mazambata. Hasali ma a cikinsu ni
ne babba. Da na ga abin ya zama haka, sai na
zama sufi. Ga labarin yadda na yi farin jini a
cikin wannan hali.

Da isata Tehran na sami wani gida wanda ya ke
daf da wani gidan sayad da magunguna na
zauna. Ina zaune sai wata tsohuwa ta kira ni
cikin gaggawa, ta ce mini maigidanta mai sayad
da magani ya kamu da ciwo mai tsanani yanzu,
saboda ya ci abinci fiye da yadda cikinsa ke iya
dauka. Maganin kuma da ya sha bai yi masa
amfani ba, don haka danginsa suna so su jarraba
su ga abin da laya za ta yi masa. To, a lokacin
kuwa ba ni da takardu da alkalami, balle
taddawa.

“Aka kai ni wurin da ya ke kwance, ga shi ya
mimmike, mata kuwa sun kewaye shi sai cewa
su ke, ‘Wayyo Allah, zai mutu, zai mutu !’ A gefe
guda kuma ga magunguna iri iri, ba wanda ba a
gwada ba. A wani gefen kuma ga likita nan tim a
kujera yana busa lofensa, ko kulawa bai yi ba.

Shi likitan nan ne ya ce a nemo mai sihiri ya
gwada irin tasa hikimar, don shi abin ya gagare
shi.
Da shigata aka ba ni wata takardar da aka nade
wani magani. Ni kuwa na zauna na cika ta da
zane iri iri, kamar dai yadda a ke rubuta hatimi.

Da na kare, na ba likita, shi kuma ya sa aka kawo
masa ruwa ya wanke rubutun a cikin kwano.

'Yan kallo kuwa sai addu’a su ke yi wai maganin
ya ci. Likitan ya dauki kwanon ya ba mara lafiyar,
ya ce masa ya sha. In kaddara ce zai mutu, to,
ba makawa tilas ya mutu. In kuwa ba kaddara ba
ce, Allah ya sa maganin ya yi amfani.

“Aka ba shi rubutun ya sha, duk aka kura masa
ido a ga abin da zai auku. Ya dan jima babu
alamar rai jikinsa ko kadan, can sai ya yi gurnani
ya bude ido, ya ta da kansa a hannunsa ya ce a
ba shi kwano. Da aka kawo masa, ya cika shi da
amai.

A takaice dai, ya warke ! “Ni dai a zuciyata
na ce ba abin da ya sa shi amai sai daudar da ke
jikin takardar da na yi masa rubutun. Amma fa
na ce wa wadanda ke wurin da ba domin rubutun
da na yi ba, da ya mutu ba shakka.

“Likitan nan kuma shi ma ya dauki duk yabon a
kansa. Da dai ya ga mutumin ya bude idanu, sai
ya ce, “Ashe ban fada maka ba ?" Da kuma ya ga
mutumin yana warwarewa sosai, ya ce da ba
domin ya ce a ba shi wannan magani ba, mutuwa
zai yi ba wata shakka. Da na ga haka, na kwabe
shi da cewar in dai shi likita ne, me ya hana ya
warkad da shi, sai da ya kira ni ? Na ce masa ya
rabu da abin da ba ruwansa. Daga nan ya ce mini
shi ba shi da shakkar na iya yin aikina, amma
kowa ya san yadda sufi ya ke. In sufi ya yi
tsubbu har abin ya yi amfani, to, amfanin nan ba
don tsarkinsa ba ne.

"Muka dai tsaya muna ta gardandami, abin ya so
ya kaure da fada, sai wata mace ta sa baki. Ta
ce ga ’Yan Sanda nan suna kwankwasa kofa,
suna tambayar dalilin wannan tashin hankali.
Wannan ya raba mu.

Sauran ’yan kallo kuwa duka
suka goyi bayana, suna kallona kamar wani
Annabi, wai rubutun da na yi kawai ya warkad da
mutum !

“Shi kuwa likitan da ya ga abin ba dama, sai ya
saci jiki ya gudu.

Amma kafin ya tafi sai da ya
tsaya ya tsine duk gashin gemunsa wadanda na
cire masa ya gama da wadansu nawa, ya kada
mini su a fuska, ya ce, ‘Tsakanina da kai za mu
ga wanda za a yi masa dariya in na kai ka gaban
Alkali gobe, na sani kome tsubbunka ba ka iya
sayensu ba.’ (A can kasar gabas an dauki gemu
kamar abu ne mai tsarki, don haka in wani ya
cire maka, ka kai shi kara, za a ci tararsa sule
uku ga kowane gashi !)

“Na tabbata bai kai maganar gaban Alkali ba don
gudun kada darajarsa wadda aka san shi da ita
ta yin magani ta ragu. Duk da haka tsoro ya
kama ni, na yi iyakar kokarina in yi amfani da
wannan sa’a wadda na samu ta warkad da
mutum. Labari ya watsu ko ina wai ga wani sufi
ya rayad da wani wanda ya ke bakin mutuwa. Shi
ke nan mutane suka fara ganin girmana.

“In na zauna tun abin safe ina rubuta layoyi sai
da dare na ke samun shakatawa. Mutane sun yi
yawa. Nan da nan fa arziki ya fara samuwa gare
ni. “Da na ga dai kada wata ran a kure ni sai na
bar garin in yi rangadi a kasar Farisa. Kowane
gari na tafi na kan yi iyakar kokarina in yi kome
da fasaha har da labarina zai riga ni zuwa garin
da zan tafi.

Mai sayad da magungunan nan kuma
ya ba ni takardar shaida da hatiminsa a kai, ita
ce na ke ta nuna wa mutane duk garin da na
sauka, don su kara gaskata labarin da suka
rigaya suka ji a kaina. “A wannan hali na ke har
yanzu, ana kuwa girmama ni. A yanzu kam ina
samun abin kaina kwarai da gaske. Duk ran da
na ga abin yana son ya bashe ni, sai in sake
kasa."

A nan ya kare ba da nasa labarin, sai kuma na
ukunsu ya kama: “Labarina kankane ne, ko da ya
ke ba da labari shi ne aikinsa. Ni dai dan wani
malamin makaranta ne. Da ya ga ina da baiwar
rike duk abin da na ji, sai ya sa ni in yi ta karanta
masa galibin tarihe-tarihe wadanda aka rubuta su
da harshemmu. In na kare karantawa kuma im
maimaita masa ya ji. “To, da ya ga ilmin nawa
bai yi zurfi ba, sai ko wannan baiwa da Allah ya
ba ni, sai ya ce im fita duniya in zama mai ba da
labarai.

“Da farko da na fara, abin bai yi kyau ba ko
kadan. lm masu jin labarin nawa sun ji, sai kowa
ya tashi ya tafi abinsa, ba mai ba ni ko da anini.
A hankali dai na fara koyon dabara.

In na fara ba
da labari mai dadi, na matso kusa da karshe, sai
in tsaya in dubi mutanen in ce musu in za su ba
ni kudi to, zan karasa musu labarin. Ka san in
labari mai dadi ne kowa yana so ya ji yadda ya
kare. Da na fara yin haka, haba, na yi ta samun
kudi. Da haka dai na fara samun abin kaina. In na
ga kamar mutanen sun fara gajiya da ni da
labaraina, sai in tafi wata kasar in ci gaba.”

(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi

Za mu ci gaba

na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: