Thursday 26 October 2017

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.

Tura Wannan Zuwa Ga

Kashi na Biyar

Amma dangane da Sarkin Kano Ali ɗan Abdullahi
(maje karofi) Alfallati, munji cewar a zamanin da
yake mulkinsa, sai watarana wani manzo yazo
masa wanda ake kira Baban Kano.

Wannan Manzo ya zone daga Lokoja, a haɓnunsa
kuma akwai wasika daga wani Attajiri Ba'agale
mai hurɗa da turawa, mai suna Adamu Jakada.

Koda manzo yazo fada, sai akai masa iso ga
sarki ya shiga gareshi ana fadanci, yayi gaisuwa
tare da mika masa wannan wasika dake tare
dashi.

Nan take sarki ya karɓi wasikar, ya shiga
karantawa a zuci ba a bayyane ba.
Ance ga abinda ke cikin rubutun:
Daga Adamu Jakadan Kiristoci. Aminci ga sarkin
kano Ali ɗan Abdullahi.

Bayan gaisuwa, wannan manzo Baba Kano na
aiko shine domin ya shaida maka da baki cewar
Turawa na zuwa gareka.
Hakika, kayi sanin cewa babu makawa sai sunzo.

Babu kuma abinda zai tunkuɗe zuwan nasu. Don
haka sai kayi taka tsan-tsan, ka kuma lura da
sha'anoninka.

Idan kanaganin ba zaka iya yakar suba, to zaifi
kyau ka mika wuya a garesu. Kayi musu
kyawawan zantuka, gami da kyaututtuka, ni kuma
nasan da sannu zaka tsira daga garesu dakai da
mutanenka.

Ina mai maka nasiha a bisa haka, don Allah indai
ka aminta da nasihata to godiya ga Allah domin
babu abinda zai faru.

Amma idan baka ɗauketaba, to ina kara jan
hankalinka abisa abinda zai auku mummuna.

Koda sarki Ali ya kammala karantawa, sai bai
cewa fadawansa komi ba, amma ya mayarda
martani da baki ga Baba kano, yana maicewa
"Kayi sani yakai Baba Kano, bazan mika wuya ga
kiristoci ba, ba kuma zan nemi tsira daga wurin
suba.

A maimakon haka, zan yakesu matsawar suka zo
kasata."

Ya faɗi haka a gaban fadawansa, amma fa a
zuciyarsa ba haka abin yake ba domin ya tsorata
har ma yayi shirin tserewa.

Daga wannan rana ne kuwa ya soma shirin tafiya
sokoto domin neman mafaka.

To kuma bayan lokacin tashi yayi ga Sarki Ali har
ma ya fita daga garinsa, ya riski sokoto, kwanaki
kaɗan yayi a garin sai ya baroshi da niyyar
komowa Kano.

Koda suka riski kasar zamfara, suka shiga wani
gari mai suna Gidan Goga (Ko Birnin Goga) sai
suka sauka anan da niyyar hutawa.
Aka baiwa
sarki Ali wani gida ya shige.

Ance Sarki Ali yana zaune a kofar ɗaki sai
kwatsam yaga matarsa mai suna kubura ta shigo
gidan a fusace tare da jama'arta.

Koda sarki ya kaleta ya ganeta, sai yace mata
"yake kubura, menene damuwarki?"
Sai kubura tace "Ya kai wannan sarki, kiristoci
sun shiga turakar ka, sun kuma karɓe iko da
birninka, sun ruguza daular ka."
Sarki Ali yace "Babu sarki sai Allah, yaushe haka
ta faru?"
Kubura ta amsa masa da cewa "kwanaki talatin
kenan bayan barowarka birni."

Sarki Ali yayi jim cikin takaici sannan yace mata
"yanzu menene abinyi?"
Kubura tace "masa idan dai kana son tsira, dole
ka gudu. Komawa kano ba naka bane. Domin
bayan fitowar mu daga kano, munji ance suma
sun fito nemanka.

Don haka tun barowar mu kano muke ta azama
ba dare ba rana domin mu riskeka mu sanar
maka da wannan labari. Kayi sani, wanda duk ya
tsere, to ya kuɓuta."

Da sarki Ali yaji wannan jawabi nata, sai kuma ya
nemi shawararta game da tserewar. Ta kuwa ce
masa lallai ya tsere a wannan dare domin hakan
shine kaɗai mafita.

Ai kuwa da tsakar dare Sarki Ali tare da iyalinsa
da wasu zaɓaɓɓu a tawagarsa suka tsere suka
nufi kusurwar birnin Gobir.

Koda gari ya waye, sai ragowar mutanen sa suka
nemeshi sama ko kasa basu ganshiba, sai daga
baya suka gane cewa da dare ya tsere.

Da aka sanar da ɗan uwansa kuma mai taimaka
masa Waziri Amadu cewar Yayansa ya tsere, sai
yace ina hujjar haka? Sai aka ce masa ai jiya
kubura matarsa ta riskeshi da yammaci.

Waziri Amadu yace "daga Allah muke, kuma
gareshi zamu koma, lallai wannan mutum ya ja
mana abin kunya, yanzu ina ya shiga, kuma
menene dalilin gudunsa?"

Daga nan sai waziri Amadu ya tara sauran
mutane ya sanar musu da abinda ɗan uwansa
yayi. Dajin haka Sai kuwa sukace yanzu suna
karkashin sane, don haka sai ya jagorancesu
izuwa duk inda yaso.

Waziri Amadu kuwa sai yace to indai haka ne,
kowa yahau dokinsa mu nufi kano (domin bashi
da labarin turawa)

Kunji yadda ta faru har waziri Amadu da
tawagarsa sukayi kichiɓus da turawa a dajin
Rubin, wanda akace yana nan kusa da garin
kwatarkwashi ta kasar zamfara, inda har kuma
waziri Amadun ya rasa ransa a fafatawar,
yayinda kaninsa ya tsere da wasu mutanen, yaje
ya mika wuya ga turawa dake kano daga baya
kuma suka naɗa shi sarkin kano.

Ance a yammacin wata ranar jumua aka naɗa
sarki Abbas (maje Nasarawa) sarkin kano. Kuma
sai da kanawa suka shafe sati guda cur suna
kaɗe-kaɗen tambura da ganguna da wasanni don
murna.

Daga bisani Gwamna Lugga ya aika suje
Dungurum ta zungeru don su haɗu dashi.
Ai kuwa haka sarki Abbas yayi hawa da
tawagarsa ya tafi Zungeru.

Gwamna Lugga kuwa ya tarbeshi, yayi masa
godiya gami da kara masa matsayi.

Daga bisani
Sarki Abbas ya komo kano lafiyaaaa.

Anan labarin Abdullahi Alghadamasi yazo karshe.

Sai dai daga bisani, an jiyo cewar watanni huɗu
zuwa biyar da tserewar Sarki Alu, sai turawan
faransa suka kameshi, suka kuma mika shi ga
turawan Burtaniya dake nemansa.

Kuma a
hannunsu ya rasu yana tsare a garin Lokoja.

Zamu ci gaba dakawo muku Tarihi Kasance da Dadinkowa24 aduk inda kuke afadin Duniya

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: