Thursday 26 October 2017

TARIHI: TUNAWA DA YAK'IN BASASAR KANO

Tura Wannan Zuwa Ga

Galadima Yusufu mutane keso ba Alu ba. A garin
Garko ya kamu da cuta mai tsanani kuma acan
ya mutu.

Kafin rasuwar sa, kowa yayi amannar
cewa shine zai zamo Sarkin kano, amma sai ciwo
ya kamashi har ya mutu a Garko.

Daga nan sai sarakunan bayin Sarki da 'ya'yansu
sukace yanzu menene abinyi? Sai wasu sukace
abu d'aya ya kamata muyi, mutum d'aya ne
kurum zai iya jagorantar mu zuwa Kano.

Shine
Mallam Babba, Alu kenan. Daga nan suka aika
masa, sannan suka dora shi a gadon Mulkin
Yusufu.

Bayan sunyi haka, da dare suka binne Yusufu da
hasken fitilu. Suka kawo Alu suka zaunar dashi
akan karagar mulki. Sukayi masa nad'i. Sai kuma
akace fadawa kowa yazo yayi mubaya'a. Kaji
yadda Alu ya zamo Sarki.

Kuma shine dalilin da
yasa dayaji turawa na tafe ya tafi sokoto domin
ziyartar hubbalen Shehu tayadda Sarkin Musulmi
zai amince da zamowar sa Sarki tare da goya
masa baya.

Jama'ar gari, mafarauta da maharba ne sukayi
bore ga Sarki Alu a lokacin da yakin Basasa ya
barke.

Basasa anan na nufin yakin da akayi don dora
Alu akan karagar mulki. Anyi shine a Ramli
shekarar 'Ba-Sa-Sha'. 'Sha' a ilimin Hisabi na
nufin 1000, 'Sa' na nufin 300, 'a' na nufin 1, yayin
da 'ba' ke nufin 2. Idan ka hada lissafi zai baka
shekara ta 1303 kenan bayan Hijira. (Dai-dai da
1894 miladiyya).

Ana kiran Alu da suna 'Mallam Babba' (Ma'ana
babban malami), domin a wurin mu duk wani dan
Sarki Mallam ne koda bai koyi karatu ba. Amma
da zarar Sarki ya bashi wata sarauta sai a daina
cewa Mallam, a koma kiransa da wannan
sarauta.

Alu ya shiga Kano ranar wata Laraba. A wannan
lokacin mutane da yawa sun bar Kano izuwa
Kamri wajen Tukur, domin shi akafi so.

An kashe Tukur ne a Gurum (Kamri da Gurum
wasu kauyuka ne dake kusa da juna a kasar
katsina).

Naji labarin cewa anji masa raunika
sannan aka kawo shi gaban Sarki Alu. Ance Sarki
Alu yayi fushi sosai akan cewa don me zasu yiwa
d'an uwansa na jini haka? Sarki Alu yace "kuyi
maza ku kawo masa ruwa yasha".

Amma sai
Sarki Tukur yace "kada a kawo min ruwa, azumi
nakeyi, bazan sha ruwa ba". A haka kuwa Allah
ya amshi ransa. Allahu Akbar!!!

A garin Gurum aka binne Sarki Tukur, shiyasa
ake Kiran sa da 'Maje-Gurum' kamar yadda ake
kiran Galadima Yusufu 'Maje-Garko', ake kiran
Sarki Abbas kuma 'Maje Nasarawa'.

Marigayi Alhaji Mahmud Koki tafinta ne na
turawa, shine kuma ya bamu wannan labari. An
rubuta labarin a cikin tarihin sa wanda aka
wallafa a shekarar 1977.

ASALIN YAKIN BASASA

Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi shine d'a na
biyu ga Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya rasu a
wajajen shekara ta 1882 miladiyya a wani gari
mai suna Kauran-Namoda. Sai k'aninsa
Muhammad Bello (shima dan Marigayi Ibrahim
Dabo ne) ya hau karagar mulki.

Ance Sarki Muhammad Bello ya rinka kokarin
karbe muk'amai daga hannun 'ya'yan 'yanuwansa
yana dasa 'ya'yansa na cikin sa. Sannan ya kara
yawan jakadu masu tattara Haraji, abinda yayi
sanadiyyar jefa talakawa cikin matsi kenan, tare
da janyo masa bakin jini a gurinsu.

Ance tun
alokacin ya fara sharewa dansa Muhammad
Tukur hanyar zama Sarki bayan ya rasu. Ya rinka
aikawa da Kyaututtuka izuwa Sokoto domin
neman goyon bayan Sarkin Musulmi.

Shikuwa Sarkin Kano Muhammad Tukur, sarkin
musulmi Abdurrahman (danyen kasko) ne ya
nada shi bayan mutuwar mahaifin Tukur din,
watau Sarkin Kano Muhammad Bello. Wasu
sunce bai kai shekaru arba'in ba aka nad'ashi
mulki, Wasu kuma sunce bashi da karsashin Rike
mulki.

A wannan lokacin, sai dan uwansa Galadima
Yusuf, wanda yake d'a ga marigayi Sarkin Kano
Abdullahi Maje-karofi tare da jama'ar sa suka
gudu izuwa garin Takai wadda ke kudu maso
gabashin Kano.

Mutuwar Galadima Yusuf ce sanadin dora Sarkin
kano Alu a mazauninsa. Sannan a hankali suka
rinka cinye garuruwan kano da yaki.

A haka har
sai da rundunar su tayi karfi, suka shigo kano a
ranar wata Laraba, 19 ga watan agusta na
shekarar 1894 miladiyya ana buga tambura na
sarauta bayan ya samu nasara akan Sarki Tukur,
wanda ya gudu ya bar Kano bayan rundunar
yak'insa ta raunana.

Dafatan zamu amfanu da darussan wannan
labari.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By © SADIQ TUKUR GWARZO, RN

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: