Thursday 26 October 2017

Tarihi: ALAWA IRIN TA-DA: RAYUWA A TSOHUWAR KASAR HAUSA.

Tura Wannan Zuwa

Idan kimiyyar wannan zamani ta gaza samar
mana da na'urar hawa wadda zata kaimu gaba
ko baya da lokaci, abin da yafi kamata sai mu
saurari yadda rayuwar ta kasance, sannan mu
fasalta-ta da tunani-kan mu.

Kafin rikicewar zamunna da al'adu, kafin
sauyawar zamantakewa da ɗabi'u tsakanin
hausawa, kafin kwararowar baki wannan yanki na
hausa, sarakunan gargajiya keda wuka da nama
a fannin mulki.

Daga zantukan da mukaji, ance asalin sarautar
kowanne gari ta soma ne daga wanda ya kafa
garin, ko kuma ace wanda ya soma zama a inda
daga baya ya zama gari babba.

Misali, wani mai suna Dala akace ya soma zama
akan wani shahararren dutse zamani mai tsawo
daya shuɗe, don haka sai ya zamo mai faɗa aji
ga duk wanda yazo wurin daga baya.

Kalmar Sarki da ake kiran mutumin da yake rike
da sarauta mafi kololuwa a gari, ance ba
daɗaɗɗa bace.

Tana iya yiwuwa asalin hausawa
bada sarki suke kiran shugaban suba.

Watakila
kodai suna kiran duk wanda ya samu mulkinsu da
sunansa na yanka ta yadda bayan ya mutu sai
sunan ya likewa wannan sarautar, ko kuma akwai
wani suna da kalmar sarki ta maye gurbinta.

A wancan zamanin, akwai karancin kwanciyar
hankula a garuruwa saboda yake-yake da kamen
bayi daga masu karfi, amma kuma akwai amana,
mutunci da girmamawa a tsakanin mutane.

Wannan yasa kowanne gari suke yin dabarar
zagaye biranensu da ganuwa, watau katanga
wadda ake gina ta da kasa, sannan ayi mata
tagogi daga sama don hango mahara da kuma
kofofi na shiga tare da sanya mai kula da
buɗewa da rufewar kofofin.

A wancan zamanin, sarakuna ababen kauna ne,
ababen girmamawa kuma. Zai wuya wani ya
shiga gari ko ya fita ba tare da sarki yaji labarin
saba. Sannan babu waya ko motocin hawa a
zamanin, amma da zarar an nufi wani gari da
mugunta, ko wata tawaga zata shige ta wani
yanki, kafin abin ya riski garin zakaga har labari
ya samesu suna shirin ɗaukar mataki
gwargwadon iko.

A zamanin maguzanci a kasar hausa, noma ne
babbar sana'ar mutanen lokacin. Sai kuma
sauran sanaoi da akeyi misalin kira, jima, fawa da
wasu kalilan da suke safarar hatsi daga gari
zuwa gari a jakuna.

Don haka ance mutanen zamanin kan ware wani
lokaci domin gangamin hadaya/sadaka bisa
murnar arzikin da suka samu bayan girbe
amfanin gona.

Akan kira ranar taron da 'Ranar Dutse', ko 'Ranar
Gangare', ya danganta dai da yankin mutane.
Idan ranar tazo, anan ne ake fito da abinci da
abinsha daro-daro ana rabawa mutane kyauta,
makaɗa kuma da mawaka suna cashewa a
dandali.

Wannan fa, wani abune da mutanen da basu san
Ubangiji ya wanzu-ba sukeyi bisa muradin kansu,
kawai saboda sunyi imanin cewa sai sun
farantawa marasa karfin cikinsu sannan zasu
samu babbar nasarar noma a shekara mai zuwa.

A irin wannan taron ne akace ake haɗa
auratayya tsakanin budurwa da saurayi. Ma'ana,
idan iyaye sun haɗu a dandali, sai firar iyali ta
shiga, take sai kaji wasu sun aminta dasu kulla
aure tsakanin yaransu. Wasu kuma anan zasu
nemi karin aure, tunda a zamanin magidanci kan
auri mata sama da biyar shi kaɗai.

Don haka da zarar sun yanke magana, sai su
dawo gida su sanar da iyali cewa an baiwa wane
ɗan gidan wane auren wance. Shikenan..

Ance idan an kulla aure, maza ke kai duk wata
hidima da al'ada ta tanadar izuwa gidan amarya.

Kuma anfi kiran abin da (baye).
Idan biki yazo kuwa, shagali ake sha kala-kala na
al'ada.

Misali, akan tafi da amarya ayi mata wanka da
lalle, abinda ake kira wankan Amarya.

Akwai ranar da ake warewa domin yin kwanan
zaune.
Sannan shima ango ana wankeshi da lalle. Sai
kaji ance 'An sashi, ko an sanyata a Lalle'.
Sannan kiɗe-kiɗe da wasannin al'ada basa
yankewa tunda ance akan shafe sati guda cur
ana shagalin aure.

Idan ranar kai amarya tazo kuwa, gangami akeyi
kamar za'a raka sarki yaki, musamman idan nesa
za'akai amaryar.

Anan zakaga tawaga ta haɗu, 'yammata da
samari, tsoffi kakannin amarya da sauran iyaye.
Sai kuma uwa uba makaɗa da zabiyar waka.

Duk da kasancewar zuwa yanzu mun gaza
samun cikakken labari akan dutsen nan na amare
mai tsohon tarihi, amma labarun baka sun
tabbatar da cewa wata amarya za'akai wani gari
inda suka haɗu da wata musiba har suka zama
duwatsu.

Don haka idan mutum yaje wajen zai
ga dutsen da akace amaryar ta zama, sai kuma
duwatsun kayan kiɗa da tawagar amarya.

Daga tsoffin kayayyakin kiɗa na wancan zamani,
akwai misalin Kuru, Dundufa, Banga, kuttuku,
Ganga da Kalangu, sai kuma tambura, algaita da
sarewa na busawa.

A baya-baya ne akace fulani sun iso da
kayayyakin samar da sauti misalin Tilliɓuro, sirik'i
da korama da wasunsu.

Daga nesa, tawagar kurum zaka hango ana tafe
ana bushe-bushe da kaɗe kaɗe, zabiya na bada
waka, 'yammata na amsawa, yayinda ita kuma
amaryar aka lulluɓeta da tufafi don kada a ganta,
duk da wasunsu akasari kukan rabuwa da gida
suke rafkawa a wannan lokaci..

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By © SADIQ TUKUR GWARZO, RN

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: