Thursday 26 October 2017

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.

Tura Wannan Zuwa

Kashi na Huɗu

Bayan yaki ya kare, sai Turawa suka mika da
tafiyarsu izuwa Sokoto.
Ragowar dakarun can kuwa da suka tsere, sai
suka nufo kano da gudu don neman mafaka.

Sai dai tun kafin su iso, tuni har labari yazo ga
turawan da suka rage a kano, waɗanda aka barsu
a gari da zimmar su tsare garin tunda sun karɓe
iko dashi.

Ai kuwa tun kafin dakarun su iso, sai turawan
suka haɗa tawaga suka nufi wajen ganuwa, suka
jejjeru suna sauraren su.

Bayan misalin awa guda suna jira, sai ga dakarun
sun karaso. Wanda ya karɓi shugabancin
tawagar shine Wamban Kano Abbas, tunda idan
ba'a manta ba, da fari Sarki Alu ne ke
shugabancin dakarun, amma bayan ya sulale sai
Waziri Amadu ya maye gurbinsa, yanzu kuwa da
waziri Amadu baya nan, shine Wambai Abbas ya
zama jagora.

Turawan nan suka tsaida waɗannan dakaru,
sannan suka karɓe dukkanin makaman dake
jikkunan su.

Daga nan aka basu damar shiga garin kano bisa
sharaɗin kowa gidansa kurum zai nufa, banda
kuma yinkurin tada tarzoma.

Anyi haka a lokacin tsakiyar sanyi na wannan
shekarar.

Daga nan kuma, sai Turawa bayan sun koma gida
suka shiga neman shawarwari daga gurin
Larabawa mazauna kano akan wanda ya kamata
a naɗa sarki a kano musamman wanda ya fito
daga zuriyar Abdullahi.

Sai larabawan nan sukace ai kuwa Wambai
Abbas ne yafi dacewa, tunda babban su waziri
Amadu ya rasu.

Sai turawa suka amsa da cewar haka nan ne.

Sai dai fa duk da haka, turawa sun shiga
tambayar Manyan kano na wancan lokacin dake
zaune a birni, cewar wa ya dace ayiwa sarki, sai
suma ɗin kuwa suka ce abaiwa Wambai Abbas
sarauta.

To kunji yadda sarki Abbas ya zama sarki na
farko a kano a zamanin turawa.

Yanzu kuwa, bari mubi sawun turawa izuwa
sokoto, karkashin jagorancin Bature mai kwagiri
domin muji yadda ta kasance.

Koda turawa suka shiga kasar sokoto, sai suka
game da wasu dakarun turawa dake zaune a
wani gari mai suna Argungu, suka nufi sokoto
baki ɗayansu.

A yammacin ranar wata lahadi Turawa suka isa
garin sokoto, a wannan yammacin kuma yaki ya
kaure a tsakanin Dakarun sarkin musulmi kuma
sarkin sakkwato Attahiru da turawa.

Ance a wannan rana sai da aka shafe dare babu
bacci ana gwabza yaki, ba tare da wani ya samu
galaba akan ɗanuwansa ba.

Da garin Allah ya waye, sai aka sake komawa
fagen fama. Aka shiga gwabzawa.
Amma a wannan karon, cikin kankanin lokaci aka
soma rinjayar dakarun sakkwato da yaki, saboda
salon faɗa da turawa suka sauya.

Da sakkwatawa suka ga ba dama, sai runduna ta
yage..

Sarkinsu Attahiru Abdu yaja tawaga yayi gabas
da gudu.

Wazirinsa mai suna Muhammadul Bhukari kuma
yaja tasa tawagar yayi arewa da gudu.

Shikenan, sai turawa suka shiga cikin garin
sokoto cikin salama.

Suka shiga tara mutane wuri ɗaya, sannan sukayi
musu jawabi cikin girma da arziki.
Sukace "kada wanda ya tsorata, domin mu ba
zamu cutar da kowa ba."

Harma sun kasance suna cewa mutane "Ku
zauna a gidardajinku, yakin ya kare, a yanzu kuna
cikin kariya da tsaro, don haka kada wani abu ya
firgita ku "

Sai dai kuma wani abin haushi ga turawa shine,
har yanzu basu kama Sarkin Kano Ali da
Abokinsa Magaji ɗan Yamusa ba, don haka.

Wannan karon ma, ba tare da jimawa ba sai suka
sake yin shiri suka fita daga sokoto izuwa neman
ababen harinsu..

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: