Sunday 8 October 2017

8. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa

Da na ga dai ba zai yiwu in sake sayad da ruwa
ba, sai na sayar da salkata, na hada kudin da
wadanda na samu na sayad da ruwa na kuwa
zama mai samu gwargwado. Na yi tunanin in kai
makiyin nan nawa kara, amma na ga ba zan ci
wata riba ba, sai na kyale. Abin haushi kuma, shi
ne abokin nan nawa mai alfadari ya tafi Tehran,
don haka na zama ni daya tal ba aboki.

BABI NA 5

Na Zama Mai Sayad Da Taba
NA FA zauna na shiga shawarwari da kaina irin
sana‘ar da zan kama in rika samun abinci.

Ga
sana’o’i nan dai barkatai. In na ce zan zama
maroki, lalle kuwa zan ci riba da yawa, don
marokan Meshed su kan sami kudi da yawa. Zai
yiwu kuma in kama sana'ar gardawa, in sami biri
in koya masa wasanni iri iri. Na ga dai ba zan iya
wannan ba, sai na watsar.

Zai yiwu kuma in
kama sana‘ata ta wanzanci, amma na ga garin
Meshed ya yi mini nisa da gida.

Daga karshe dai
na zabi sana'ar sayad da taba, don ni kaina
gwanin mashayinta ne.
Shi ke nan shawara ta tsaya. Na sayi tukwanen
taba da yawa iri iri, da kwanon zuba su.

Na sayi
karafa biyu na tsokale tukunyar taba, da gugar
ruwa, da tukunya, da dogwayen jakankuna na
ganyen taba. Duk wadannan a jikina na makala
su. Kamar yadda ka san beguwa ta ke in ta ta da
kayoyinta, haka na ke in na rarrataya kayan nan!

Na raba ganyen tabar sayarwa kashi uku. Kashi
na farko rabi duk kashin dabbobi ne, ita na ke
sayar wa attajirai.

Na biyu, kashi uku daga cikin
hudu duk kashin dabbobi ne, ita na ke sayar wa
masu biye wa attajirai. Sauran talakawa kuwa
sai a ce ma ba taba su ke saye ba, don kashin
dabbobi ya rinjayi ganyen tabar yawa.

Amma in
na fara koda su, haba, sai nan da nan in sayar.

Har na shahara ga sayad da taba a Meshed.

Babban dan cinikina wani sufi ne.

Shi kuwa
gwanin shan taba ne, don haka ba na sayar masa
da taba mara kyau, Ko da ya ke ba ya ba ni
isassun kudi sosai, duk da haka na ci riba ta
wurinsa, don abokansa da dama wurina ya ke
turo su.

Ina cikin halin haka, sai abotarmu da sufin nan ta
fara karfi. Ana kiransa Sufi Sefer.

Har ya dauke ni
wata rana ya kai ni wurin ’yan’uwansa.

Ko
wannensu kuwa sufi ne. Bayan da ya gabatad da
ni a gare su, ya ce mini in ina so in rika zuwa
wurin taron shawara tasu duk lokacin da za su
yi. Na kuwa yi na'am da maganarsa.
Kullum in na zo sai su shanye mini tabata mafi
kyau, ga shi kuwa ba abin in guje su ba. Zama
cikinsu yana da dadi da gaske, don haka na
rinjayi zuciyata in kasance cikinsu.
Ran nan da yamma bayan mun kare shan lofe,
sai muka zauna. Sufi Safer ya ce mini ya kamata
im bar aikin banzan nan na sayad da taba in
zama sufi.

Ya ce watakila ma ban sani ba in
shahara kamar Sheik Sa’adi. Ni kuma na ce masa
ta yaya haka zai yiwu ? Na ce ni jahili ne kwarai,
ban ga yadda zan sami ilmin da zan zama sufi
ba. Na ce ko da ya ke na iya rubutu da karatu,
na sauke Alkur’ani, na hardace Hafiz da Sa'adi,
na karanta littattafai da dama, in an debe
wadannan ni jahili ne na sosai.

Muka dai tsaya
yana ta yi mini bayani wai ba wani ilmi mai zurfi
zan kara a bisa wanda na ke da shi ba. Muddin
dai ina da ban gaskiya zan yi ta aikata al'ajibai,
mutane kuwa su gaskata dukan abin da na fada.
Bayan da ya kare ba ni bayani, ’yan’uwansa suka
tafa hannu suka ce kashegari za su ba ni labarin
kansu.

Kashegari muka sake taruwa kowa na rike da
lofensa yana sha. Bayan da muka natsa, Sufi
Sefer ya fara ba da labarinsa haka.

“Ni dan Luti Bashi ne na Sarkin Shiraz. Sa’ad da
ina yaro abokaina su ne birai da namun daji
wadanda ubana da abokansa su ke da su.

Irin
wasanni da dabarun da a ke koya musu suka sa
ni samun hikima wadda ta yi mini amfani duk
cikin zamana na duniya. Da na cika shekara
goma sha biyar na zama cikakken sharifi. Ina iya
cin wuta, in yi dabo iri dabam dabam. Ina cikin
wannan hali sai ran nan ’yar Janar na Sojan
rakuma na Sarki ta gan ni. Ta ce kuma ba ta son
kowa sai ni.

“A cikin Sojan rakuman nan akwai wani wanda
Janar din nan ya ce masa ya kawo kanwa tasa,
ta zama baranya a gidansa.

Shi Sojan nan aminina ne na gaske, kanwarsa ce
ta fada masa kaunar da ’yar Janar din ta ke yi
mini, shi kuma ya fada mini.

“Da na ji haka, sai na tafi wurin wani mai rubuta
takardu, na ce masa ya rubuta mini takardar
kauna.

Da ya rubuta ya ba ni, sai na kasa
kannewa, na fada masa yarinya da ta shawo
kaina haka, amma na ce masa asiri ne kada ya
fada wa kowa. Da jinsa, bai zame ko ina ba sai
wurin Janar din nan ya fada masa.

Da Janar ya
ji, sai ya roki Sarki a ba shi odar da za ta sa im
bar Shiraz. Aka ba shi.

Shi kuwa ubana ba ya
son ya bata wa Sarkin nan rai, don haka ya
matsa mini im bar garin. Da safe ubana ya kawo
wani katon bika ya ba ni, ya ce im maishe shi
abokina. Ya kuma sa mini albarka, ya ce yana
fata in zama kamarsa. Shi ke nan na yi sallama
da gida.

“Na kama hanyar zuwa Isfahan ina tunanin
wannan yarinya wadda na bari a baya da
abokaina.

Ina cikin wannan zurfin tunani har na
iso wani gidan sufi ban sani ba. Na zauna a wani
dan dutse na yi ta kuka. Da sufin nan ya ji kuka,
ya fito, na ba shi labarina duka. Ya kai ni cikin
dakinsa.

A nan kuma na ga wani sufi wanda ya fi
na farko kwarjini. Hulan nan ma da ka ke gani a
kaina tasa ce.

“Da ganina sai tunani ya zo masa. Shi da daya
sufin suka fita suka yi magana, sa'an nan suka
shigo. Ya ce mini yana son im bi shi zuwa
Isfahan. Ya kuma yi mini alkawarin zai yi mini
alheri in na kame kaina. Zai kuma sa ni a hanya
wadda zan rika samun abin kaina.

Na yarda im bi
shi. Bayan da muka sha lofe, sai ni da shi muka
kama hanya, muna tafiya da sauri, ba mai ce wa
wani kala.

Can sai Sufi Bideen, sunansa ke nan, ya fara yi
mini tambayoyi a kan irin aikina na da. Da na
fada masa, na ga lalle ya ji dadi da abubuwan da
na iya yi. Daga nan ya ci gaba da bayyana mini
abubuwa masu amfani game da zama sufi.

Ya
rinjaye ni in zama daya. Ya ce kuma in na dauke
shi kamar maigidana, shi kuwa zai koya mini duk
abin da ya sani. Ya ce saninsa ba kankane ba ne,
don ya shahara a kasar Farisa. Ya fara ba ni
labarin sihiri iri iri, ya fada mini wadansu
abubuwa da zan rika yi na tsubbu a ko wane
lokaci. Ya ce ta wurin wannan kadai ne zan sami
abin kaina.

“Ya ce mini in an sami wutsiyar zomo an sa ta
karkashin matashin kan yaro, nan da nan barci
zai zo masa. In kuma an sami jininsa am ba doki,
to, dokin nan zai zama maguji kwarai.

In an sami
idon kerkeci da kasusuwan yatsunsa an rataya
wa yaro, sai yaron ya zama jarumi.

In an sami
kitsensa kuma an shafa wa mace, kaunarta ga
mijinta za ta bace. In kuma matsarmamansa aka
samu aka shafa wa mace, za ta yi ta haihuwa.

Amma abin da ya fi daraja duka, shi ne a sami
busasshiyar fatar kura mace a rataya.

In an yi
haka, wanda ya ratayan nan zai yi farin jini ga
kowa. Ya dai yi ta yi mini maganganu irin
wadannan, ya nuna mini abubuwan da zan iya yi,
har daga karshe ya yi mini wata magana wadda
shi kansa ya san ba zan yarda da ita ba.

“Ya ce mini, ‘Sefer, ba ka san irin arzikin da ke
cikin bikan nan ba - ba ina nufin a yadda ya ke
da ran nan ba, amma in ya mutu. Da a ce
matacce ne, zan iya cire wadansu abubuwa daga
cikinsa wadanda zan yi layoyi da su, in sayad da
su da kudin gaske. Ya kamata ka sani, hantar
bika, tun ba irin wanda ka ke da shi din nan ba,
in an yi amfani da ita za ta dawo da kaunar wani
abin da a ke kauna a da ga mai ita. ln ka sami
fatar kewayen hancinsa ka kewaye wuyanka da
shi, ba abin da zai same ka, in dai maganar dafi
ce.

In kuma an kona bikan dungum aka dibi
tokarsa aka sha, sai mutum ya dauki halinsa
duka. watau wayo, da hikima da ikon kwaikwayo
na ko wane iri. Daga nan ya ce zai kashe bikan
nawa.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, da karfe
tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com
.
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: