Sunday 8 October 2017

Kasashen Waje: An Hallaka Mutum 2 Har Lahira a Masarautar Saudiya

Tura Wannan Zuwa

An kashe wasu masu gadi biyu aka kuma
raunata wasu uku a wani hari da wani dan
bindiga ya kai kan wata fadar Masarautar
Saudiyya a Jeddah.

Ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta
Saudiyyar ta ce, maharin wanda yana dauke ne
da bindiga mai sarrafa kanta da kuma bama-
bamai na fetur, wato hadin gida, shi ma an harbe
shi.

Bayan binciken da aka yi an gano cewa mutumin
mai shekara 28, dan kasar ne kuma sunanshi
Mansour al-Amri.

Lamarin ya faru ne, da misalin karfe uku da minti
15 agogon kasar (daya da minti 15 agogon
Najeriya). a wani wurin binciken ababan hawa a
wajen kofar shiga fadar ta Al Salam, inda ya tuka
motarsa har zuwa wurin sannan ya bude wuta.

A halin da ake ciki dai Sarki Salman na Saudiyyar
yana kan wata ziyara ta kasashen waje. Kawo
yanzu babu wani karin bayani da aka bayar na
game da dalinlin maharin na kai wannan farmaki.

Kafin wannan harin ofishin jakadancin Amurka ya
yi gargadi ga 'yan Amurkar da ke kasar a ranar
Asabar, da su yi takatsantsan wurin zuwa
unguwar, bayan wasu rahotanni da ba a tabbatar
ba na kai hari a yankin.

A 'yan kwanakin da suka gabata 'yan sandan
Saudiyyar sun yi wa wasu wurare uku dirar
mikiya, a babban birnin kasar Riyadh, wadanda
ke da alaka da wata kungiya da ake zargi ta 'yan
ta'adda ce, mai dangantaka da kungiyar IS,
wanda a lokacin suka kashe mutane biyu, sannan
suka kama wasu biyar.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com
.
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: