Monday 8 January 2018

Karanta Kaji Sharhin Fina-finai: Wasu kurakurai 5 da akayi a fim din Ciki da Raino

Tura Wannan Zuwa Ga
Tare Da: Saddika Habib Abba
Suna: Ciki Da Raino
Tsara labari: Nazir Adam Salihi Furodusa: Ibrahim Sinana Bada umarni: Falalu Dorayi
Kamfani: TJ Multipurpose Concept
Jarumai: Adam A Zango, Sulaiman Bosho, Falalu A. Dorayi, Hadiza Aliyu Gabon, Ibrahim Sinana, Umma Shehu, Tijjani Asase, Hauwa Malali
farkon fim din an nuna Shamaki (Sulaiman Bosho) ya na zaune a wurin sana’arsa ta gadi, matarsa Zara’u (Hadiza Gabon) ta bugo ma sa waya ta shaida ma sa cewar a asibiti an tabbatar ma ta da cewar ta na da juna biyu. Shamaki ya nuna murnarsa da jin dadinsa sosai sakamakon wannan albishir da a ka yi ma sa a lokacin har ya zo ya rabawa abokan aikinsa kudi. A wani bangaren kuma na fim din an nuna Alhaji Bashir (Ibrahim Sinana) tare da matarsa Sa’ade (Hauwa Malali) ita ma ta nuna ma sa cewar ba ta da lafiya kuma da alamun ta na da juna biyu. Shi ma ya nuna jin dadinsa sosai, sannan ya umarce ta da su je asibiti domin likita ya tabbatar mu su.
A bangaren gidan Nafi’u (Falalu A. Dorayi) shi kuwa wata budurwarsa, Fadila (Umma Shehu), ya yiwa ciki ta zo gidansa ta tare ta tabbatar ma sa da cewar sai ta haife abinda ya ke cikinta, sannan ta tafi kauye ta direwa mahaifinsa. Nafi’u da Fadila su ka buga su ka buga a kan cewar shi ba za ta zauna a gidansa ba, sannan shi cikin ma bai yarda nasa ba ne, amma daga karshe Fadila ta tubure har sai hakura Nafi’u ya yi, domin a yadda a ka nuna Fadila ta fi shi sanin kan tsiya. An nuna Alhaji Bashir ya kawo matarsa asibiti, domin a tabbatar ma sa da cikin matarsa.
A lokacin su ka hadu da Shamaki shi ma ya kawo matarsa. Kwatsam shi ma Nafi’u sai ga shi ya kawo Fadila, domin a tabbatar ma sa, saboda da ma shi tun farko ya karyata cewar akwai cikin. Kowaccensu Dakta (Adam A Zango) ya ba ta gwaji, a ka je aka tabbatar da cikin sannan a ka ba su lokacin da za su dinga zuwa awo.
A wannan zuwan da su ke yi su na kawo matan awo a nan a ka saba da Bashir da Shamaki da kuma Nafi’u, amma duk wannan abinda a ke yi su a zatonsu Nafi’u da Fadila mata da miji ne, domin idan za su yi masifarsu gefe su ke komawleaders
dannan cikkunna na matan kowanne ya janyo ma sa wahala; kowacce ta dinga wahalar da mijinta; yau wata ta ce goruba za ta ci, wata ta ce fasadabur, wata ta ce goba. Kuma idan sun sha wahala sun nemo sun kawo mu su, sai su ce ya fita daga ransu.
Haka kowacce ta cigaba da wannan diramar har lokacin da kowaccensu ta haihu. Sai kuma su ka maida raino hannun mazan. Ita Fadila budurwar Nafi’u ta haifi namiji, ita kuma Zara’u matar Shamaki ta haifi mace, ita kuma Sa’ade matar Alhaji Bashir ta haifi namiji. Haka zumunci ya kullu tsakaninsu tamkar da ma can sun san juna. An nuna hatta rainon a guri daya su ke yi mu su.
Idan banda wahalar da su da matan ke yi babu abinda su ke yi. Su ne su ke yi mu su rainon yaran, goyo, rarrashi duka har sai lokacin da wani dan duniyar abokin Nafi’u Namaroko (Tijjani Asase) ya zo daga Legas ya koya mu su dabarun yadda za su dinga yiwa matan nasu su daina wahalar da kansu.
A cikin abinda ya koya mu su ya nuna mu su cewar idan yaran su na kuka, to su dinga kyale su, idan su ka ga haka da kansu za su dinga kulawa da ‘ya’yannasu, domin uwa ta fi kowa son danta; uba ya na iya damka dansa a hannun hukuma, idan ya yi laifi, amma duk runtsi uwa ba ta iyawa. Haka kuwa a ka yi yaran su na fara kuka su ka yi burus su ka kyale su, sai ga shi kowaccensu ta dauki danta ta na jijjigawa. Alhaji Bashir da Shamaki da Nafi’u su ka nuna jin dadinsu sosai da abinda Namaroko ya yi mu su, domin da ma sun gaji.
A lokacin Nafi’u yaja abokinsa Namaroko gefe a kan ya ba shi shawarar ya ya zai yi ya rabu da nasa jaririn da Fadila uwar jaririn tunda an same shi ne ba ta hanyar aure ba? Namaroko ya ba shi shawarar kawai ya zo ya bi shi su gudu Legas su cigaba da shan sha’aninsu a can. Namaroko ya shaida ma sa cewar, shi zai wuce Kaduna a ranar. Ya fada mi shi cewar ya biyo shi Kadunan washegari, daga nan sai su wuce Legas. Nafi’u ya yarda da shawarar Namaroko ya hada kayansa, washegari ta na yi Fadila ta na bacci ya saka kaya a mota ya dauki hanyar Kaduna. Sai da ya yi nisa sai ya ji kukan jariri a bayan motarsa.
Ya na dubawa sai ya ga ashe bai sani ba Fadila ta saka masa dansa a bayan motarsa. Takaici ya saka Nafi’u ya rushe da kuka, don babu tafiya tunda abinda a ke gujewa ga shi a bayan mota.
Abubuwa Birgewa:
1- An nuna tsantsar kulawa tsakanin miji da mata, musamman a lokacin da mace ta ke da juna biyu
2- Jaruman sun yi kokari wurin isar da sakon
3- An yi amfani da kayan aiki masu kyau, musamman kyamara da kuma abin daukar sauti
Kura kurai:
1- Akwai wurin da Zara’u ta ke bugowa Shamaki waya ta ke shaida ma sa ta je asibiti an shaida ma ta ta na da ciki kuma daga bisani sai mai kallo ya ga sun kuma zuwa asibiti a tabbatar mu su. Shin sun manta Zara’u ta je asibiti ne kuma a can a ka tabbatar ma ta ta na da juna-biyun?
2- Akwai wurin da su Fadila su ke zuwa sayen kayan marmari da Nafi’u ta ke fadawa mai kayan marmarin ita koriyar tufa ta ke so, ya ce ‘to’, kuma sai mu ka ga ya dauko jar tufa ya saka ma ta alhali sharadin da ta saka bai cika ba kuma bai ce babu ba. kuma da ya kawo ta bude ta fara ci ba a ga mamaki a fuskarta ko ta nun aba haka ta ce ma sa ba.
3- An nuna cewar fim din ya na magana ne a kan Musulmai kuma Hausawa da al’adarsu, amma sai mu ka ga Fadila ta tare a gidan Nafi’u na tsawon lokaci har ma ta haife juna-biyun jikinta ba tare da hakan ya janyo abin magana a unguwa ba. A zahirin addini da al’adar Bahaushe hakan ba ya faruwa, domin ba muharraman juna ba ne, babu hurumin da ya ba ta damar zama a gidansa. Idan ma za a yi hakan sai dai a ce daga baya ya aure ta tunda cikinsa ne ta haihu a gidansa, amma ba wai su cigaba da irin wannan zama wanda addini da al’ada su ka haramta ba kuma ba tare da komai ya biyo baya a cikin al’ummarsu ba.
4- Kwatsam! Bayan matan uku sun haihu sai mu ka ga mazajensu da yara a wani lambu su na raino. An gaya ma na cewar sun kawo matansu asibiti, amma sai mu ka ga matan nasu a zaune cikin lambu su na shakatawa da lafiyyen abinci. Ya dace a ce an nuno su a cikin asibiti kuma a fadi dalilin da ya kawo su, ba wai a nuno ma na su a lambu ba, domin duk mai kallon da ya ga wajen ya san ba asibiti ba ne.
5- Shin fim din a birni a ka dauke shi ko kuma a kauye? An rikitar da masu kallo domin wani wurin sai a gan shi birni, amma wani wurin kuma a kauye musamman hanyoyin.
Karkarewa:
Fim din ya kayatar, amma babu sakonni masu karfi a ciki kuma wasu abubuwan ba a nuna karshensu ba.
Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba
Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
ALLAH yabar Zumunci Amin
Source By ©Leadership A Yau
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user