Saturday 24 February 2018

Idan ka Karanta saika Zubda Hawaye: RANAR BAN-KWANA DA DUNIYA KARANTA KAJI

Tura Wannan Zuwa Ga

Ko zaka iya kwatanta kanka kamar gaka nan Ka
zube a Qasa domin fitar ranka, Irin zubewar da
ba zaka sake tashi tsaye ba, Sai dai
aranar
hisabi.

Kwatanta kanka yayin da zazzabin mutuwa ya
ratsa cikin jikinka, Mutuwa ta lullubeka da
Wahalhalunta da 'dacinta da fizge-fizgenta..

Kamar ga Mala'ikan mutuwa nan ya fara fizgar
ruhinka tun daga Dugaduganka, amma zafin
fizgar nan ya ratsa duk sassan jikinka har tsakar
Kayinka..

Yana ci gaba da fizga, ya janyo ranka ta cikin
naman jikinka da Qasusuwanka da 'bargonka da
jijiyoyinka...

Yawun bakinka ya Qafe, idanuwanka sun kakkafe,
alokacin ne ka tabbatar mutuwa zakayi...
Sannan
ne zaka wofintar da duniyar nan da abin cikinta..

Zakayi nadamar Miyagun ayyukanka..

Yayin da zafin radadin kusantowar mutuwa ya
ratsa dukkan Sassan jikinka, Zuciyarka ta cika da
bakin ciki da damuwa, Ka dena gane mutanen
dake wajenka.

Amma jikinka ya kai mutuka
wajen tsananin yanayin da yake ciki..

Awannan lokacin ne zaka tabbatar cewa babu
matsera babu mafaka daga wajen Allah sai zuwa
gareshi (SWT).

Ka tabbatar cewa babu makawa
gareka yau sai kaji bishara daga Mala'ikan
daukar ranka..

Kodai yayi maka bisharar shiga
Aljannah, cikin ni'imomin da babu yankewa, ko
kuma yayi maka mummunan albishir din shiga
cikin Azabar wutar Jahannama..

Wajen zaman da
babu rayuwa kuma babu mutuwa.
Kuma babu
sauki balle sassauci (Allah shi kiyayemu).

Yayin da kake cikin tsakiyar wannan yanayin
damuwar da dimaucewar da tsananin bakin cikin
jiran Qarshenka. Kana 'daga kanka sai ka ha'da
ido da Mala'ikan daukar ranka..
Kodai yazo maka
bisa mafi kyawun siffah, ko kuma bisa
mummunar siffar da babu irinta..

Zaka ganshi ya Miko hannunsa zuwa cikin
bakinka domin ya fitar da ruhinka daga cikin
jikinka..

A sannan ne zaka raina kanka.. Zaka
Qaskanta Matsayinka..

Domin tunaninka yana
rataye da irin bisharar da ka samu daga gareshi.

Kodai yace maka "Bishara gareka Ya Kai
Masoyin Allah! Ina yi maka bisharar samun
yardar Allah da ni'imominsa..".

Ko kuma yace maka "Ya Kai Makiyin Allah! Ina yi
maka albishir da samun Fushin Allah da
Uqubarsa..

Ga iyalai sun kewayeka sai kuka sukeyi.. Masu
yin fifita suna yi, amma kai baka san abinda
sukeyi ba..

Domin ba zasu amfanar dakai komai
ba..
Kururuwarsu ba zata hana Mala'ikan nan yin
aikinsa ba..

Kuma kukansu ba zai sauya maka
sakamakon da ka janyo ma kanka ba.

A sannan ne zaka Gwammaci ka bayar da
dukkan dukiyarka da abinda ka mallaka, don a
jinkirta maka koda minti guda, ko kuma a
saukaka maka zafin radadin nan koda na second
guda.. Amma inaa!!!.

Asannan ne zakayi ban-kwana da duniya...

Ka
tafi kenan zuwa sabuwar rayuwar da baka ta'ba
gani ba.. Ka tafi gidan gaskiya. Daga kai sai
halinka..

Lallai daga Allah muke, kuma gareshi zamu
koma.

Babu wajen gudu babu matsera daga gun
Allah sai zuwa gareshi.

Ya Allah kasa mu cika da
imani.

Ka kyautata Qarshenmu don alfarmar
soyayyar Annabinka (saww).

Amin ya ALLAH

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©M. Kabiru Muhammad

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: