Saturday 3 February 2018

KARANTA KAJI: Lallai Ummi Zee-zee Tanayin Abinda taga dama ko Kasan babban Abinda ta Aikata???

Tura Wannan Zuwa
Ummi Ibrahim, wadda aka fi sani da Zee-Zee, wadda a yanzu idan aka kira ta da biloniya babu wata matsala, idan aka yi la’akari da irin manyan motoci da yanayin yadda take rayuwa mai dan karen tsada a yanzu.


Babu shakka za a iya cewa ta kere wa sa’anninta da dama da suka shiga harkar fim tare a ba
Bayan tsohuwar jarumar wadda ‘yar kabilar Shuwa ce daga jihar Borno, ta dan fito a finanan Hausa da kuma matsalar da ta samu da saurayin da ya yi niyyar aurenta, wato Dan Chana, sai ta yi bulaguro zuwa jihar Lagos, inda ta koma can da zama.
Bayan ta koma jihar Lagos da zama ne, Ummi Zee-zee ta soma soyayya da fitaccen mawakin Turancin nan, wato Timaya, inda har ta bayyana cewa tana da burin aurensa idan har ya amince zai Musulunta, amma daga baya sun rabu. Soyayyar Timaya da tsohuwar jarumar finafinan Hausan, ya yi matukar daukar hankalin jama’a musamman na yankin Arewa kasancewar a matsayinta na Musulma tana soyayya da wanda ba addininsu daya ba, amma daga baya sai ta fito ta wanke kanta da zimmar cewa za ta aure shi ne idan har ya amince zai musulunta.
Sai dai daga bisani bayan an rasa ina soyayyar Zee-zee da Timaya ta kwana, kwatsam sai labari ya soma yaduwa na cewa tuni jarumar suka raba gari da mawakin. Wanda kuma bincike ya nuna cewa tun daga wannan lokacin ta yi bulaguro daga jihar Lagos ta dawo yankin Arewa, inda ta koma jihar Kaduna, inda take zama a kawataccen gida, sannan duk inda za ta tare da masu tsaron lafiyarta take zuwa.
A yayin da al’umma suka soma mancewa da batun Zee-zee, kwatsam sai fitacciyar Mujallar nan ta Fim da jaridar Turanci ta Blueprint suka yi hira da ita, inda a hirar ta ce akwai soyayya mai karfi tsakaninta da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, kuma tana sa ran za su yi aure nan ba da jimawa ba.
Idan ba a manta ba, a farkon shekarar da ta gabata, wani na kusa da jarumar, ya fadawa majiyarmu cewa Ummi Zee-zee ta sha fiya-fiya don ta kashe kanta, sakamakon matsalar da ta samu da janar Babangidan, wanda har ta kai ga janar din ya kashe duk wasu lambobin wayoyinsa da ya sa jarumar za ta same shi, kuma ya hana ta mu’amala da duk wasu kadarorinsa da ke jihohin Kano, Kaduna, Niger har ma da na kasashen waje.
Kasancewar Zee-zee tana bukatar janar Babangidan ya san irin halin da ta shiga sakamakon matsalar da suka samu, sai ta bayyana a jaridar Blueprint kan yadda ta yi kokarin halaka kanta ta hanyar shan fiya-fiya, inda bayan an buga labarin wani na kusa da ita, ya kira majiyarmu yake cewa Janar din ya kira ta, kuma har ya tura tawaga zuwa Kano domin duba lafiyarta, ko da bukatar a haura da ita kasar waje domin duba lafiyarta.
Majiyarmu ta ci gaba da cewa tun daga wannan lokaci, a duk sanda aka nemi Zee-zee aka rasa, idan aka tambayi makusantan jarumar, sukan bayyana cewa walau ta wakilci Janar din a wurin taro a fadin kasar nan, ko kuma ta wakilce shi a harkokin kasuwancin da yake gudanarwa a kasashen waje.
Majiyarmu ta kuma kara da cewa, akasarin kwafen jaridun da ake hira da jarumar janar Babangidan yana da su, kamar yadda wani na kusa da tsohon shugaban kasan ya bayyana, inda ya kara da cewa ya sha ganin kwafen jaridar Blueprint mai dauke da hirar Ummi Zee-zee a gidan Janar din.
Sannan kuma duk inda tsohuwar jarumar finafinan Hausa za ta, za ka ganta ta ne a kawatattun motoci tare da masu kare lafiyarta, wanda hakan na nuna cewa akwai alaka tsakaninta da tsohon shugaban kasa.
Wani abun dubawa game da lamarin alakar da ke tsakanin jarumar da Janar din, shine babu wasu daga cikin iyalan Janar din da suka kalubalanci lamarin. Sannan kuma soyayyar dake tsakanin Zee-zee da Janar din ya samo asalin ne tun lokacin da take karama, inda take nuna farin cikinta a duk lokacin da aka nuno sa a talabijin. Haka kuma ta samu ganawa da Janar din ne ta hanyar mahaifinta, tun mai dakinsa marigayiya Maryam Babangida tana raye.
Wanda tun daga wannan lokacin ne ta shaku da IBB din. Kuma ta ce tun kafin su yi ido hudu da Janar din ya soma yi mata goma ta arziki.
Jarumar wadda yanzu haka ta koma kasar Dubai da zama bayan ta sayi gida a can a makon da ya gabata, (sai dai ta shigo Nijeriya na dan wani lokaci ta koma), tana gudanar da kasuwanci, inda take amfani da lakabin Zee-zee a wuraren kasuwancin nata.
A kwannan ma wani kamfanin shirya finafinan Hausa, ya yi amfani da motocinta masu dauke da sunan Zee-zee, inda aka yi amfani da su a fim din mai makamncin wannan suna, wanda Fati Washa ta fito a matsayin jarumar fim din.
Game da ko me ya sa ba a ganin fuskarta a matsayin jakadiyar kamfanonin sadarwa irin su Glo, MTN, ZAIN da Etisalat? Ummi ta ce IBB ya fada mata cewa za ta iya samun sama da naira milyan dari idan har tana bukatar yi wa kamfanin Glo talla, amma a ganinta wannan kudin bai taka kara ya karya ba da har za ta yi tallar ba. Sannan kuma a bangaren shirin fim kuma, ta fadi cewa tana da tabbacin cewa ta wuce matsayin ta yi fim don kudi a yanzu, domin babu furodusan da yake da kudin da zai dauke ta domin sanya ta a fim, sai dai ta taimakawa harkar domin a samu ci gaba.
Sannan ta kuma baiwa masoyanta hakurin daina fuskarta a fim da suka yi, amma kuma za ta dinga amfani da kafafen yada labarai domin su san halin da take ciki. Haka kuma jarumar ta yi ikrarin cewa wasu daga cikin gwamnoni a kasar nan suna ba ta kwangiloli.
Game da batun aurenta da Janar din kuma, ta ce har yanzu maganar na nan, kuma a duk lokacin da labarin ya auren ya bayyana zai dau hankalin al’umma.
Ta kuma ce masu ganin cewa Janar din ba zai aure ta ba, su jira su gani. Sannan kuma a jwabinta na karshe, Ummi ta nuna jimaminta game da rashin lafiyar da tsohon shugaba kasan ya dan yi fama da shi, wanda har ta kai ga an garzaya da shi kasar waje domin duba lafiyarsa, inda ta ce kamar ta mutu.
Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba
Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
ALLAH yabar Zumunci Amin
Source By ©Rariya and Sadikblog
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user