Wednesday 7 March 2018

KARANTA KAJI: DAGA YAU DUK WANDA YA KARA RIGIMA KO HAYANIYA AKAN AN ZAGENI ALLAH YA ISA BAN YAFE MASA BA-Adam A Zango

Tura Wannan Zuwa

Jarumi mai tauraro Adam A.Zango ya gargadi yan uwanshi kan mayar da martani mai tayar da rigima kan wadanda ke zagin sa a shafukar sada zumunta.

Jarumin ya bayyana hakan a shafin sa na instagram tare jawo hankalin kanne da abokanai har ma da yaran shi na yin hanni wajen tayar da hayaniya. "DAGA YAU DUK WANDA YA KARA RIGIMA KO HAYANIYA AKAN AN ZAGENI KO AN ZAGI IYAYENA A CIKIN KANNE NA, ABOKAINA DA YARANA....ALLAH YA ISA BAN YAFE MASA BA" ya rubuta.

Idan ba'a manta ba a kwanan baya jarumin  da abokin aikin sa kuma kuma babban jigo na masana'antar kannywood Ali Nuhu sun samu sabani wanda ya tayar da iska tsakanin mabiyan su.

Duk da cewa jarumai sun sulhunta kansu bayan kokarin da wasu masu ruwa da tsaki na masana'antar kannywood suka yi na neman kawo karshen rigimar dake tsakanin su wannan bai hana wasu daga cikin mabiyan sucigaba da yi ma juna kalaman batanci.

Bugu da kari game da wannan rigimar da jarumai suka yi, sannanne dan wasan barkwanci Ali Idris Muhammed wanda aka fi sani da Ali Artwork yayi fashin baki inda yake cewa sun kirkiro rigimar ne da ganga domin jawo hankalin jama'a.

Aliartwork dai ya bada misali da irin rigimar da jaruman suka yi a shekarun baya wanda ya haifar da tseigumi tsakanin al'umma masu bibiyan harkokin masana'antar kannywood.

Jarumin ya kara da cewa jaruman su biyu azzalumai ne tare da yin la'akarin da yanayin lokacin da yayi dasu tare da yi masu aikin sarrafa bidiiyo wanda bai tsinana abun kirki ba daga gare su duk da kokarin da yayi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Fim Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: