Wednesday 30 May 2018

Karanta Yanzu Kaji: Shin Mene ne hukuncin daukar hoto a wuraren Ibadah???

Tura Wannan Zuwa


Daukar hoton a wuraren ibada abu ne da mutane suke yawan yi kuma su wallafa hotunan a shafukan sada zumunta na zamani inda abokansu za su gani su kuma yi tsokaci ko magana ko kuma yayata hoton.

Ba sabon abu ba ne mutun ya dauki hoto a masallacin idi ko na harami a Makka ko Madina ko kuma a filin Arfa.

Bugu da kari wasu na daukar hotuna na bidiyo a lokacin dawafi ko kuma lokacin hawa Arfa kuma su wallafa a shafukan sada zumunta na zamani.

Wata kila wasu na yin hakan ne domin su nuna wa duniya cewa sun samu zuwa wannan waje, yayin da wasu kuma suna son su nuna wa wadanda suke gida yadda wurin ibadar yake ne.

To amma wani lokacin hakan ba ya rasa nasaba da aikin riya da Musulunci ya hana.
Irin wannan dabi’ar ta samo asali ne tun zamanin da, inda mahajjata ke dawowa gida da kallo-kallo daga aikin hajji inda yara da sauran mutane da ba su samu zuwa aikin hajji ba za su samu ganin wuraren aikin hajji ta hotunan da ke cikin kallo-kallon.




Riya ce?

Wasu na tunanin cewar daukar hoto a irin wadannan wuraren ibadan son a-sani ne, wato riya ce. Amman mene ne hukuncin irin wannan dabi’ar a Musulunci?

Ustaz Hussaini Zakariya, ya ce, “Maganar daukar hoto idan aka je Harami ko Madina, malamai sun rabu gida biyu kan wannan batu.”

“Daya mai tsanani kwarai da gaske, shi yana ganin cewa hoton ma haramun ne a ko ina aka yi, ba sai lallai cikin Harami ba, kuma yi a cikin Haramin ma ya fi muni.”
Amma akwai wadanda suke ganin cewa daukar hoto ba aikin ibada ba ne. Ba wanda zai dauki hoto ya ce ya yi sunnah ko mustahabi ko kuma ya yi farilla.”

Malamin ya kara da cewa: “Don haka ba aikin ibada ba ne balle a ce in ka yi jama’a sun gani, aikinka ya baci. Don haka yana ganin cewa halal ne matukar dai mutum ba wai ya yi wannan abin don jama’a su ga cewa yana wajen wata ibada kuma burinsa ya cika ba ne.”

Ya kwadaita wa wadanda Allah bai ba su ma su roki Allah Ya kai su wannan wurin, kuma ya sanar da danginsa da abokansa cewa ga shi Allah Ya kawo shi wurin da duk Musulmi yake son ya zo.”

“Ina ganin wani abu ne na raba abin farin cikin da ya samu mutum da ‘yan uwansa da abokansa.”

Saboda haka Ustaz Zakariya ya ce yana ganin wannan ba aikin addini ba ne kuma ba riya ba ce.

Shi kuma Dokta Abdulkadir Sulaiman na Sashen koyar da addinin Musulunci a jami’ar Abuja cewa ya yi daukar hoto kansa ba ya halarta.

Amma batun ko daukar hoto tare da wallafashi a shafukan sada zumunta zai iya janyo riya, ya ce wannan wani lamari ne mai sarkakiya.

Malamin ya yi bayanai tare da kawo hadisai da ke nuna cewa yanke hukuncin riya ba hurumin dan Adam ba ne domin wannan al’amari ne da ke zuciyar dan Adam, kuma Allah (SWT) ne kawai zai iya sanin abin da yake zuciyar bawansa.




Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©BBC HAUSA and MURYAR AREWA
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user