Monday 11 June 2018

Kalli Abubuwan Mamaki Wanda su faru A Kasar Morocco yayin da Shugaban Kasar Nigeria Muhammadu Buhari Yakai Musu Ziyara ( Hotuna 12 da Cikakken Labari)

Tura Wannan Zuwa


A duk lokacin da shugaba Buhari ya kai ziyarar aiki jihohin Najeriya Dandazon jama'a sun sha yimai taron ban mamaki, musamman jihohin Arewa, hakanne ta faru a ziyarar da shugaba Buhari yakai kasar Morocco, jiya, inda akamai tarbar karamci.



Sarki Muhammad VI na Moroccon da shugaba Buhari sun fito ta saman mota suna dagawa dandazon jama'ar da suka fito dan yiwa shugaba Buharin maraba, yayin da jami'an tsaro da jerin gwanon motocin alfarma ke kewaye dasu hagu da dama.

Abin ya kayatar sosai, muna fatan Allah ya dawo dashi lafiya.



Gwamnatin Najeriya da takwararta na kasar Morocco sun rattafa hannaye kan wasu yarjejeniya tsakanin kasashen biyu da zasu habbaka tattalin arzikin kasashen biyu, wadanda suka kunshi cigaban iskar gas, zuba hannayen jari da kuma inganta harkar noma.




NAIJ.com ta ruwaito fadar shugaban kasa ne ta sanar da wadanna riba kan riba da Najeriya zata sharba daga ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ma shugaban kasar Morocci Sarki Muhammad na Shida.




Kaakakin shugaba Buhari, Garba Shehu ya bayyana cewa yarjejeniyar da shugaban NNPC ya sanya ma hannu tare da shugaban hukumar man fetir na kasar Morocco, Amina Benkhadra zai haifar da ginin bututun iskar gasa mai tsawon kilomita 5,660 daga Najeriya zuwa Morocco, wanda zai taikama wajen gurbatan yanayi, kare kwararowar Hamada da kuma samar da dubunnan ayyukan yi ga matasa.


Haka zalika, wani babban jami’I a gwamnatin Buhari, Ushe Orji da takwaransa na kasar Morocco, Mostafa Terrab sun rattafa hannu a wata yarjejeniya da zata samar da cigaba ga kamfanonin sarrafa taki na Najeriya, wajen iganta ayyukansu.


Bugu da kari, Ministan noma na Najeriya, Audu Ogbeh da na kasar Morocco, Aziz Akhannouch sun wakilci kasashen nasu biyu a kulla yarjejeniyar horas da jami’an noma na Najeriya da kasar Morocci za ta yi, wanda hakan zai inganta harkokin noma a Najeriya.


Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ganawa da sarkin Morocco,Muhammad VI inda wakilan kasashen biyu suka saka hannu akan yarjejeniyar kasuwanci data hada da ajiye bututun iskar Gas daga Najeriya zuwa kasar ta Morocco.


Ajiye bututun Gas din daga Najeriya wanda zai bi ta kasashen yammacin Afrika zai kai zuwa kasar ta Morocco kuma ya wuce zuwa wasu kasashen turai.


A wata sanarwa da me magana da yawun shugaban kasar ya fitar, Malam Garba shehu ya bayyana cewa, kasashen biyu sun kuma saka hannu akan horas da manoman Najeriya akan hanyoyin adana amfanin gona.


kuma wakilan kasashen biyu sun saka hannu akan bude ma'aikatar sarrafa ma'adanin Ammonia a Najeriya wanda dashine ake yin takin zamani da sauran abubuwan amfani.

Source: Hutu Dole and Hausa Naija


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user