Monday 2 July 2018

Kalli Hotunan Jaruman Indiya tare da Jerin sunayen Jaruman Indiya da suka yi Aure domin Kudi - Karanta a Natse Kaji

Tura Wannan Zuwa Ga
1. Sridevi da Boney Kapoor

A shekarar 1996 ne marigayiya Sridevi ta yanke shawarar aurar mai shirya fina-finai wato furodusa Boney Kapoor.


A wannan shekarar ne suka yi aure, kuma sun zauna lafiya saboda yadda Boney Kapoor ke matukar kaunar matarsa.
A karshen shekarun 1970, ne Boney Kapoor ya kyallara ido ya ga Sridevi, kuma tun daga wancan lokaci yaji yana matukar sonta.

Da farko ya sha wuya saboda rashin samun hadin kanta, duk da yana da aure, Boney sai da ya sanar da matarsa wadda suke da yara biyu tare cewa shi fa yana son Sridevi.
Boney Kapoor mai kudin gaske ne, ya kuma yi amfani da kudinsa wajen saye zuciyar jaruma Sridevi.Boney Kapoor dai ya girmewa Sridevi sosai domin ya bata akalla shekara kusan tara.
A tsawon shekara fiye 20 da suka yi suna tare a matsayin mata da miji har Sridevi ta mutu, sun yi zaman lafiya.

Kuma Boney Kapoor ya nunawa Sridevi matukar kauna, domin kuwa a koda yaushe idan kaga zara to zaka ga wata.

Sun haifi 'ya 'ya biyu mata, wato Jhanvi Kapoor da kuma Khushi Kapoor.

2. Juhi Chawla da Jay MehtaJaruma Juhi Chawla na daga cikin jarumai mata na Indiya da suka yi fice saboda irin rawar da suka taka a fina-finai da dama.
Jarumar na daga cikin jarumai mata kyawawa, kuma ta fara fim ne tun a shekarun 1980.


Juhi ta yi fina-finai da dama tare da Shahrukh Khan da kuma Aamir Khan.
Da farko an yi rade-radin cewa suna soyayya tare da Aamir Khan, amma kuma zance ba haka ya ke ba.

Haka shi ma Sharukh Khan, mutane sun zaci akwai soyayya tsakaninsu, amma kuma aminan juna ne har yanzu.

Juhi ta auri shahararren dan kasuwa mai kudin gaske wato Jai Mehta a shekarar 1995, kuma har sun haifi 'ya'ya biyu.

Akwai ratar shekaru a tsakanin Juhi da mijinta, amma kuma da ya ke yana da masu gidan rana, bata kula da hakan ba, ta yi aurenta kuma suna zaune har yanzu lafiya.

Juhi Chawla tayi fina-finai kamar Daar da Qayamat se Qayamat tak da Duplicate da Aaina da kuma Yes Boss.

3. Shilpa Shetty da Raj KundraShilpa Shetty ma na daga cikin jarumai mata na Indiya da suka yi fice, kuma kusan fina-finanta ta yi sune da jarumi Akshay Kumar.

Da farko Shilpa sun fara soyayya ne da Akshay Kumar, kuma har yaso ya aure ta, to amma da ya nuna cewa baya so ta ci gaba da fitowa a fim, sai ta nuna masa cewa ita fa bata shirya dakatar da yin fim ba
Wannan dalili ne ya kawo karshen soyayyarsu a shekarar 2007.

Daga bisani kuma ta hadu da hamshakin matashin mai kudi Raj Kundra, wanda ya taso a Birtaniya, ya ke kuma kasuwancinsa.
Shilpa ta girmi Raj Kundra da watanni uku, amma kuma hakan bai hanasu aure ba.
Sun yi aure ne a shekarar 2009, suna kuma da da tare.

Har yanzu suna zaman su lafiya ba tare da wata matsala ba.

Shilpa Shetty ta fito a cikin fina-finai da suka yi fice kamar Dhadkan da Main Khiladi Tu Anari da Baazigar da kuma Auzar.

4. Vidya Balan da Siddharth Roy Kapoor


Vidya Balan, jaruma ce da ta shiga harkar fina-finai da kafar dama.

Ta fito a fitattun fina-finai kamar The Dirty Picture da Kahaani na daya da na biyu da Parineeta da Lage Raho Munna Bhai da kuma Paa.

Ta samu lambonin yabo da dama.

Vidya Balan ta auri mai shirya fina-finai Siddharth Roy Kapoor, wanda hamshakin mai kudi ne a shekarar 2012.

Ya girmeta sosai, amma kuma da ya ke mai hannu da shuni ne, Vidya Balan ba ta ga hakan ba.

Suna tare har yanzu, amma ba su haihu ba.

5. Ayesha Takia da Farhan Azmi


Ayesha Takia jarumar fina-finan Indiya ce da itama ta taka muhimmiyar rawa.

Ta fara fitowa a fim ne a shekarar 2004, inda ta fito a fim din Tarzaan.

Daga nan ta ci gaba da fitowa a fina-finai, kuma ita mai tallan kayan kawace.

Ayesha ta na da kyaun da kowanne mutum zai so ta zama matarsa.

To amma, duk da rububin aurenta da mutane suka zo suyi, sai ta yi ke meme ta ce ita sai Farhan Azmi, wanda hamshakin mai kudi ne, ya kuma girmeta da shekara hudu.

Mutane dai sun yi ta sukar aurenta, saboda ta yi aure ne tun tana da shekara 23 da haihuwa, kuma bisa yadda aka kashe kudi a bikin, domin anyi kasaitaccen biki ne, za a fahimci cewa lallai ta auri mai kudin gaske.

Sun yi aure a shekarar 2014, kuma yanzu haka suna da da.

Ayesha Takia ta fito a fina-finai kamar Wanted da Dil Maange More da kuma Dor.

6. Tina Ambani da Anil AmbaniTina Munim jaruma ce da ta yi fice a shekarun 1980.
A zamaninsu tana daga cikin jarumai mata 'yan gayu da suka iya kwalliya.
Ta fito a fina-finai da dama kamar Yeh Vaada Raha da Rocky da Fiffty Fiffty da kuma Karz.

Tina Munim ta yi soyayya da jarumi Sanjay Dutt, da ya ke abokai ne tun suna yara, koda suka girma, sai kawance ya rikide zuwa soyayya.

Sun rabu saboda halayyar Sanjay Dutt ta shan giya.

Ta kuma auri mijinta da har yanzu suke tare Anil Ambani wanda mai kudin gaske ne tun a shekarar 1991.

Suna da 'ya 'ya biyu.

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna, Hausa Videos,Wakoki Hausa, Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya


FARIN CIKIN KU SHINE FARIN CIKIN MU

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari  ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: BBC HAUSA
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user