Tuesday 25 September 2018

Karanta Kaji Dalili: Yanzu Bani da Burin da ya wuce nasamu Miji Nagari Inyi Aure - Zainab Indomie

Tura Wannan Zuwa Ga
Zainab Indomie, kamar yadda masoyanta da ma'abota fina-finan Hausa suka fi sanin ta, ta yi fice a masana'antar Kannywood a shekarun baya musamman sakamakon irin rawar da ta taka a wasu manyan fina-finai.


Bayan kusan shekara biyar ba a jin duriyarta a harkar fina-finan Kannywood, Zainab Abdullahi ta yanke shawarar komawa bakin sana'arta.

Daga cikin fina-finan da suka sanya jarumar ta shahara akwai 'Wali-Jam', da 'Ali' da 'Garinmu Da Zafi' da sauransu.

Sai dai tana tsakiyar tashe aka daina jin duriyar jarumar, abin da ya kai ga ana diga ayar tambaya da yada jita-jita a kan dalilan daina ganinta a fina-finai.

"A lokacin da jarumar ke kan ganiyarta kusan ana iya cewa ta yi wa sauran matan wannan masana'antar fintinkau", a cewar Kabiru Jammaje, wani mai shirya fina-finai a masana'antar Kannywood.

Jammaje ya ce akwai daraktoci da masu shirya fina-finan wadanda yanzu haka suka shirya su yi aiki da Indomie saboda hikima da kuma kwarewarta a harkar fina-finai.

Mece ce hakikanin abin da ya boye Indomie?

Daina fitowar Indomie a fina-finai ya ja hankalin masoyan fina-finan Hausa, har aka rika danganta hakan da wasu bayanai da halayen da ake ganin su suka tilasta mata daina fitowa a fina-finai.

Sai dai Zainab Indomie ba ita ce jarumar Kannywood ta farko da ta daina haskawa a fina-finan ba, akwai da dama irinsu Kubura Dhako da Ummi Nuhu da Saima Muhammad da Ummi Zee-zee da dai sauransu.

Ko da yake akwai tsoffin jarumai irinsu Safiya Musa da Fati Ladan da Zainab Raga da aure ne ya boye su.

A tattaunawarta da BBC Indomie ta karyata dukkanin rade-radin da ake yi a kanta, ta kuma shaida cewa kawai ta yanke shawarar tafiya hutu ne domin dagawa 'yan baya kafa.

"A kowanne lokaci ana son wani ya bai wa wani dama don shi ma ya samu lokacin damawa, don in da ina tsaye a kan karagata da ban bai wa 'yan baya dama ba.

"Na dawo bakin sana'a ta wadda In Allah Ya yarda idan aka ga na koma to sai dai idan aure ne", inji Indomie

Zainab Indomie ta ce a yanzu takamaimai ba za ta iya cewa ga fim din da za a soma ganinta a cikinsa ba, sai dai ana tuntubar ta kuma a cikin wannan watan ma akwai shirin fim da take aiki a kan shi.

Labarin dawowarta fina-finai ya ja hankali a shafukan sada zumunta musamman shafin Instagram bayan da fitattun jarumai irinsu Adam A. Zango da Ali Nuhu suka wallafa hotunanta don taya ta murnar dawowa masana'antar.

Kabiru Jammaje, wanda ke shirya fina-finan Turanci a Masana'antar Kannywood, ya ce yanzu haka akwai wani shirin fim na Ingilishi da yake shirin haska Jarumar.

Akwai soyayya tsakanin Indomie da Zango?

An sha yada jita-jitar soyayya a tsakanin Adam A. Zango da Zainab Indomie; ko a wannan lokacin wasu na ganin cewa shi ya taimaka mata sake dawowa bakin sana'arta.

Amma Indomie ta ce: "Ni na dauki Adamu ubangida na ne kuma kamar dan uwa na dauke shi kamar yadda ya dauke ni amma babu komai tsakani na da shi.

"Zango ya na taimaka min sosai, musamman don ganin na cimma nasara a wannan sana'a".

Indomien dai ta ce ba ta da wani buri da ya wuce samun miji na gari ta yi aure.

Karanta Kaji: Shin dagaske ne Zainab Abdullahi Indomie tayi Film din Batsa na Blue Films?

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user