Wannan wani sabon darasi ne da Waziri Aku zai rika kawo muku duk ranar Juma'a, daidai wannan lokaci, tare da taimakon Malam Nasir G. Ahmad.
Domin taimaka wa dalibai masu nazarin harshen hausa, da kuma masu so rubutunsu ya yi ma'ana da saukin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.
DARASI NA FARKO.
KA’IDOJIN RUBUTUN HAUSA
Ka’idojin rubutu, wasu dokoki ne da aka yi ittifakin yin amfani da su wajen rubuta daidaitacciyar Hausa. Ita kuwa daidaitacciyar Hausa, daya daga cikin kare-karen harshen Hausa ce da aka zaba, aka daidaita mata ka’idojin nahawu, don yin amfani da ita cikin rubuce-rubuce da harkokin yada labarai a dukkan kasashen Hausa da sauran duniya baki daya.
BAKAKE DA WASULLAN HAUSA:
Jimillar bakaken da ake amfani da su wajen rubuta daidaitacciyar Hausa, su Talatin da daya (31) ne. Ashirin da uku (23) daga cikinsu saukaka ne, Takwas (8) kuma masu goyo. Akwai kuma wasula goma sha biyu (12).
SAUKAKAN BAKAKE
MANYA: B, 'B, C, D, 'D, F, G, H, J, K, K', L, M, N, R, S, SH, T, TS, W, Y, Z, ‘(alhamza).
KANANA: b, 'b, c, d, d', f, g, h, j, k, k', l, m, n, r, s, sh, t, ts, w, y, z, ‘ (alhamza).
MASU GOYO
MANYA: FY, GW, GY, kW, kY, kW, kY, ‘Y,
KANANA: fy, gw, gy, kw, ky, kw, ky, ‘y
WASULLA
GAJERU MANYA: A, I, O, U, E,
GAJERU KANANA: a, i, o, u, e
DOGAYE MANYA: AA, II, OO, UU, EE,
DOGAYE KANANA: aa, ii, oo, uu, ee
MASU AURE:
auren /a/ da /i/ = /ai/
auren /a/ da /u/ = /au/
Akwai kuma auren /u/ da /i/ = /ui/, misali guiwa, kuikuyo, mui gaba (mu yi gaba)
Kamar yadda muka sani, an samo wannan salon rubutu ne daga rubutun Rumawa wanda Turawa suka kawo mana.
To daga cikin ainihin bakaken abacadan Turanci akwai wasu bakake hudu da ba a amfani da su a Hausa, saboda ba mu da irin sautukansu. Bakaken su ne: /p/, /q/, /v/ da /x/. Furucin kowannensu na da takwara a bakin Bahaushe da yake amfani da shi a madadinsa.
Maimakon /p/ ana amfani da /f/ ne. /k'/ a madadin /q/, /'b/ a madadin /v/, sai /s/ a madadin /x/.
Duk da haka, akan rubuta /p/ a wasu sunayen yanka da ba ainihin na Hausa ba ne, kamar Pakistan, Potiskum, Pankshin, da makamantansu.
Babu sautin /ch/ a Hausa, sai dai /c/. Shi ma akan bar wasu sunaye, musamman na garuruwa wadanda Turawa suka rubuta imla’insu a hakan da /ch/. kamar Bauchi, Bichi, Chiranchi, dss.
Ba a nuna dogon wasali ta hanyar rubanya shi a rubutun Hausa na yau da kullum, kamar a ce /zoomoo/, sai dai /zomo/. Don haka kuskure ne rubuta wasu sunaye irin su Sameera, Haleema, Ameen, dss.
Haka ma kara bakin /h/ da wasu kan yi a wasu sunaye, musamman na mata kamar Aminah, Samirah, dss. Hasali ma ba imla’in rubutun Hausa ba ne, na Turanci ne.
Yayin rubanya bakake masu goyo, ana rubanya bakin farko ne kadai, ba duka biyun ba. Misali:
Gwaggwaro ba gwagwgwaro ba.
Kyakkyawa ba kyakykyawa ba.
Fyaffyade ba fyafyfyade ba.
Haka ma:
Shasshaka ba shashshaka ba.
Matsattsaku ba matsatstsaku ba.
BAKIN ALHAMZA (‘)
Na san wasu za su yi mamakin ganin na kira wannan alama da baki. To haka abin yake. Ana kiran sa da “Hamza” ko “Alhamza.”
Shi wannan baki ana rubuta shi ne yayin da ya zo a tsakiyar kalma. Ba a rubuta shi a farkon kalma, sai dai ana kaddara samuwarsa, don shi ne baki ga wasalin da a zahiri za a ga kalmar ta fara da shi, domin babu wata kalma da ke farawa da wasali a Hausa. Ba ya kuma zuwa a karshen kalma.
Misali,
A farkon kalma:
‘amfani, ‘aure, ‘ido, ‘unguwa, ‘ofis, dss.
A tsakiyar kalma:
Ma’auni, Sa’idu, shu’umi, nau’o’i, dss.
Za mu ci gaba sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura tambaya zuwa muryarhausa24@gmail.com mungode.
KARANTA KAJI: MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA DARASI NA BIYU
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.MuryarHausa24.com.ng
Friday 12 October 2018
TURA WANNAN ZUWA GA
Mawallafi: MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA verified_user
MAKALOLI MASU ALAKA
- Blog Comments
- Facebook Comments