Wednesday 23 January 2019

Karanta Kaji: Yadda al'umma su Taimakawa Ciroki da Kudi Fiye da ₦200,000 Domin Ya Daina....

Tura Wannan Zuwa Ga
Shafin sada zumunta na Instagram na Northern_hibiscuss ya bayyana abin da ya sa suka tara wa Bashir Bala Ciroki kudi fiye da naira 200,000 a ranar Talata.

Bashir Bala Chiroki

An fara tara wa daya daga cikin `yan wasan farko da suka shahara a masana'antar fina-finan Hausa ne bayan da aka samu labarin cewa yana tallan kunun aya.
Aisha Falke, mai shafin Northern_herbiscuss ta ce sun tallafa wa dan wasan ne saboda tausayi.
A wata hira da gidan talabijin na Arewa24 , Ciroki ya yi ikirarin cewa masu shirya fina-finai da jaruman Kannywood sun daina sanya shi a fim, shi ya sa a yanzu yake sayar da kunun aya.

'Ban taba tunanin ina da masoya a duniya irin wannan ba'

Shafin Northern_hibiscuss ya wallafa gangamin nema wa dan wasan taimako.
Sai dai kafin hakan, jarumin fina-finan Kannywood Ali Nuhu ya kalubalanci wani mai amfani da shafin Twitter cewa ya bayyana masa mutanen da abokin sana'arsa Ciroki, ya tallafa wa lokacin da tauraruwarsa ke haske a fagen wasan kwaikwayo.
Shi dai mutumin, wanda ke amfani da sunan Doctor Kiyawa, ya nuna rashin jin dadinsa ne kan yadda ya ce jaruman Kannywood sun yi watsi da Ciroki duk da cewa yana bukatar taimako.
Doctor Kiyawa ya yi zargin cewa mata kan shiga harkar fim cikin shekara guda su yi kudi amma mazan da suka kwashe shekara da shekaru suna harkar ba sa samun komai
"a Kannywood ne za ka ga mace ta shigo fim wannan shekarar amma ta fi wadda ya yi shekara 10 yana sana'ar fim kudi. Ali Nuhu, kai ne wadda yanzu jama'a suke gani da kima a Kannywood, don Allah ku yi wa [Chiroki] wani abu wanda shi ma ba zai manta cewa kun yi masa halacci ba.

Sai dai a jerin martanin da Ali Nuhu ya yi wa masu irin wannan korafi, ya kalubalance su da su nuna masa irin taimakon da Cirokin ya bai wa Kannywood.
"Zan yi maka tambaya: lokacin da Ciroki yake tashe wa ya taimaka wa? Maimakon haka, a kan kudi mene ne ba ya yi wa masu shirya fim? Ya kamata mu san abin da muke yi."
Ya ce bai kamata a rika yi wa 'yan Kannywood rashin adalci ba, wajen dora alhakin gazawar wani daga cikinsu a kansu.
Jarumin ya ce babu wani da ke Kannywood da zai taimaka wa Ciroki, yana mai cewa "ya kamata ya dawo masana'antar ya sasanta da masu shirya fina-finai, sannan ya ci gaba da aiki kawai."
Har ila yau Ciroki ya gode wa shafin Northern_hibiscuss dangane da tallafin naira 215, 000 da suka ba shi a Kano ranar Talata:

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user