Thursday 31 January 2019

KARANTA SHAWARA GA SAMARI ‘YAN SOYAYYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Yi ammafani da kalaman soyayya masu dadi da inganci a lokacin da kake gwagwarmayar samun amincewar zuciyar dukkan wata yarinya da ka gani kana son mallakarta.Kasance mai lissafawa tare da tauna dukkan wata magana kafin ka furta ta ga masoyiyarka bayan ta nuna maka amincewarta a soyayyarka.

Karda ka kasance mai takura wa tare da matsantawa a kan dole sai ta yi wani abu da ta nuna maka bata son yi a zahiri ko ta nuna maka alamun hakan, domin kuwa hakan zai sanya ta fara gajiya tare da kosawa da kai.

A dukkan lokacin da kake son ta yi maka wani abu to ka gabatar mata da bukatar ka cikin siyasa da zolaya amma idan ka nuna mata dole to kuwa ba zaka samu yadda kake so ba idan ka samu an yi ma kenan.

Kasance mai yin dukkan wani abu da ka san zai faranta mata ka kuma guji yin dukkan wani abu da ka san zai kuntata mata. Yi mata kyauta a lokacin da bata zaton samun hakan daga wajen ka, yin hakan zai sanya ka burgeta zai kuma kara sanya soyayyar ka a cikin zuciyar ta.

Karda ka cika yi mata kyautar kudi ko bata wasu abubuwa barkatai domin kuwa yawan yin hakan zai sanya ka kasa banbance cewa soyayyar gaskiya take yi maka ko kuma kudin ka take so.

Mace bata son takura bata son ka fiya maimaita mata abu daya, ba kuma ta son ka cika kushe wani ko wata a gaban ta, bata son kuma a lokacin da kuke tare kake nuna kulawa ko fifiko ko nuna wata ta fita kyau ko wani abu makamancin haka. Mata suna son kake yabon kyawun su.

Ka kasance mai bayyana mata cewa ita kyakkyawa ce a duk lokacin da kuka yi waya ko kuma kuke tare, ka ke bayyana mata cewa muryarta na da dad’i sosai kana samun nutsuwa a duk lokacin da ka ji sautin muryar ta, ka nuna mata cewa ta iya kwalliya kuma tana da tsafta.

A duk lokacin da kuka hadu ko a waya ko a zahiri ko kuma sako ka tura mata to ka bayyana mata kana sonta kafin ku rabu.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user