Wednesday 20 March 2019

KARANTA KASHE-KASHEN SOYAYYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Kashe-Kashen Soyayya.


Soyayya ta kasu izuwa gida uku kamar haka:

1 Soyayya Don Sha’awa.

2 Soyayya Don Abin Duniya.

3 Soyayya Ta Ha’ki’ka Ko Gaskiya.

1-SOYAYYA DON SHA’AWA: A wani lokaci mace kan ga namiji ko kuma namiji ya ga mace, sai d’aya daga cikinsu ya ga wani abu a jikin d’ayan har ya ja hankalinsa ya ba shi sha’awa, ya ji yana son wannan mutum saboda wannan abu.

To irin wannan ba soyayya bace sha’awa ce da zarar d’aya daga ciki ya biya bu’katar tashi sai a fara neman hanyar rabuwa da juna.

2-SOYAYYA DON ABUN DUNIYA: Irin wannan soyayya Ita ce wadda ake yi don kud’i, ko dan kyau ko dan wani ‘kyale-‘kyalen duniya.

Ita ma irin wannan soyayya ba ta cika nisa ba, da zarar abun da ake yin soyayyar dan shi ya gushe, sai a fara shirye-shiryen nesanta da juna.

3-SOYAYYA TA HAK’IK’A KO GASKIYA: Irin wannan soyayya ita ce wadda ake amfani da hankali da tinani wajen kafa ta. Duk soyayyar da ba a gina ta a kan sha’awa ko wani abun duniya, ko wani mugun nufi ba, to wannan soyayya ta gaskiya ce.

Kuma ita ce irin soyayyar da take d’orewa wadda ba ta yankewa har abada.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user