Monday 17 June 2024

Ire-iren Matan Da Za Ku Daina Yin Soyayya Da Su

Tura Wannan Zuwa Ga

A lokacin da na karanta rubutun Fakihu M.Sani Jingir da yake cewa, "Duk macen da tun kafin ka aure ta, Allah Ya sa ka fahimci cewa, idan ka aure ta akwai yiwuwar za ku rabu, saboda wasu ɗabi'unta waɗanda ba su yi maka ba, ina mai ba ka shawarar ka rabu da ita tun kafin ka aure ta, kada sai bayan ka aure  ta, ta haifo maka 'ya'yan da ba za su girma a ƙarƙashin kulawar uwarsu ba, bayan ka sake ta, daga baya 'ya'yanka su zamar wa al'umma matsala." Na fahimci muna da ra'ayi iri ɗaya.


Ire-iren Matan Da Za Ku Daina Yin Soyayya Da Su
Hoto: The press radio 


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


Duk tsananin son da nake yi miki, ban ga amfanin kin ce kina so na, ni ma na ce ina son ki ba, amma tun kafin mu yi aure idan na ce ki bar yin kaza ba za ki bari ba, idan na ce gyara kaza ba za ki gyara ba, idan na ce ki daina kaza sai ki kasa dainawa, idan na ce ba na son kaza, sai ki nuna kamar a lokacin ke kuma  ki ka fara son shi?


Wace irin rayuwar aure kake hango wa waɗannan masoyan idan suka yi aure a haka? Ko kana tunanin za ta yi masa biyayya ta ba shi kulawar da yake buƙata, wadda ta kasa ba shi ita tun suna rayuwar samartaka, lokacin da ake sa ran akwai soyayya tsantsa a tsakaninsu da kunya da kara da kuma haƙuri da juna?


Idan har ka fahimci wadda kake ƙauna, ba za ta iya yi maka abin da kake tsammani daga gare ta ba, idan kun yi aure, irin su; biyayya, ɗaukar shawara, nuna kulawa, damuwa da damuwarka, kuma ka gano akwai wata a gefe da take tsananin ƙaunarka, tana jin maganarka, tana ɗaukar shawarwarinka masu amfani a gare ta, to ina mai ba ka shawara ka zaɓi wannan ta biyun komai muninta, ko ba mai siffarta kake nema ba, ka karɓe ta, ka mutunta ta, ka ba ta kulawa.


Bayan aurenku, za ta bi ka sau-da-ƙafa, za ta riƙe ka, ta ririta ka, za ta ɗauke ka tamkar wani Sarki da za ta rayu a ƙarƙashin inuwarsa, rayuwa ta har abada.


Idan kuwa ka biye wa kyawu, da soyayya ta fatar baki, a ƙarshe za su tafi su bar ka a cikin duhu da cizon yatsa, da yin da-na-sani na tsawon rayuwa, wanda daga ƙarshe sai ɗayanku ya buƙaci SAKI! Domin neman makararriyar mafita, 'ya'yan da kuka haifa su zama marayun ƙarfi da yaji, su gaza samun ingantacciyar rayuwa irin ta iyaye.


Shi aure ba soyayya kawai yake buƙata ba, yana buƙatar fahimtar juna, kyautatawa, da kuma tausayawa daga kowane ɓangare na namijin da na macen, saboda a ƙarshe dole kyawun da ake ji da shi da soyayyar da ake ji da ita, da kunyar da take a tsakani su gushe, sai ya rage saura zaman HAƘURI. 


Wannan ita ce rayuwar kowane gida mai tsari.


Idan har ke da nake ƙauna, fiye da kowace budurwa a faɗin duniya, kina karanta wannan saƙon nawa, ki sani, a duk lokacin da ki ka ji na ce mu rabu, to wannan tunanin shi ne yake zuwa a cikin zuciyata, ba wai don na daina son ki ba ne ba.


Kin kasa sauyawa zuwa yadda nake hasashen za mu iya rayuwa a tare, ba tare da kin cutar da ni ko ni na cutar da ke ba. 


Zan iya jure zafin rabuwa da abin da nake fatan ya zama nawa, amma ba zan iya jure raɗaɗin rabuwa da abin da ya zamo nawa ba, na san zai haifar min da miki mai yaɗuwa a cikin zuciyata da ba shi da magani.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.


Allah Ka haɗa mu da mata na-gari, waɗanda za mu yi kwaɗayin ci gaba da rayuwa tare da su, a gidan Aljanna.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user