Monday 17 June 2024

Kalaman Soyayya A Hirar Farko

Tura Wannan Zuwa Ga

Lokacin da ka nemi izini  a wajen Budurwa domim kawo mata ziyara gidansu, idan ta amince. Yadda ake samun matsala shi ne kalaman da za ka yi amfani da su ta yadda za ka sace zuciyarta ka tafi da wayonta, ka ja hankalinta ta ji kamar ta bi ka gidanku.Kalaman Soyayya A Hirar Farko
Hoto: Getty Images


MarubuciImran Musa Jahun


Shi ne wasu samarin ba su iya ba, dalilin da ya sa kenan 'yanmata ba su amincewa da soyayyar ku.


Wallahi ko ba ka da kuɗi idan ka iya zance me daɗi na kwantar da hankali, mace za ta so ka saboda suna da tausayi.


Ga yadda za ka yi;


Haƙiƙa na yi farin ciki da har kika ba ni damar ziyartar gidanku, tun lokacin da muka haɗu na ji son ki ya shiga cikin zuciyata.


Wannan shi ne dalilin da ya sa na buƙaci ki ba ni izini na same ki a gida domin mu tattauna.


Bayan rabuwar mu da ke na lura ke mace ce mai kyakkyawar halayya da kuma tarbiyya me kyau.


Kina da Ilimi da hankali da tunani. Sannan kin iya mutunta surar jikinki wajen kyautata sa sutura da kuma nutsuwa a wajen magana.


Wannan su ne abubuwan da suka ja hankalina.


Ina so na zama garkuwa a gareki don kare miki mutuncinki.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user