Monday 17 June 2024

Korafin Jama'a A Game Da Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

 Mai aure na cewa: "Ina ma dai ma ban yi aure ba."


YAUSHE ZA KU HUTA?
Hoto: Salon



 
Gwauro/Tuzuru na cewa: "Ina ma dai na yi aure na huta".

Mai kuɗi na cewa: "Ina ma dai na samu hutun zuciya".

Talaka na cewa: "Ina ma ni mai kuɗi ne, na huta".

Tsoho na cewa: "Ina ma dai samartaka ta ta dawo.".

Babba na cewa: "Ina ma dai a ce ni yaro ne, babu wani nauyi a kaina na sha wasa na".

Yaro na cewa: "Ina ma a ce ni babba ne"

Rayayye na cewa: "Ina ma dai na mutu na huta.".

Matacce na cewa: Ina ma dai na dawo duniya don na gyara kurakuraina".

Yaushe za ka samu huta ne ya kai Ɗan Adam?

(Saurara ka ji! Da ambaton Allah zuciya take samun nutsuwa) Ra’ad: 28
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user