Friday 16 August 2024

Ingantattun Siffofi 8 Na Shaidan

Tura Wannan Zuwa Ga

1. Girman kai ya ƙi sujjada ga Annabi Adam (A.S), bayan kuwa Allah ya sa shi.


Suffofin Shaiɗan
Hoto: Life in saudi arabia


MarubuciSheikh Aminu Ibrahim Daurawa


2. Ƙarya ya yi wa Annabi Adam (A.S) ƙaryar cewa wanda ya ci wannan bishiya zai dawwama kuma zai samu mulki na dindindin.


3. Hassada, ya yi wa Annabi Adam (A.S) hassada na matsayin da Allah ya ba shi.


4. An kira shi ɗagutu saboda komai nasa baya kan tsari.


5. An kira shi maridan wato mai tsarin kai, saboda ya ƙi jinin gaskiya. 


6. An kira shi rajem wato jefaffai, saboda babu shi babu rahamar Allah.


7. An kira shi la'ananne, saboda ya yi nisa daga dukkan alkhairi. 


8. An kira shi maƙiyi, saboda mummunar ƙiyayyar da yake nunawa duk mai son Allah. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user