Wednesday 14 August 2024

Kalaman Begen Masoyiya Cikin Wake

Tura Wannan Zuwa Ga

Asam'u kin tafi kin bar ni,

Begenki ban yi da wasa ba.


Begen masoyiya
Hoto: Wallpapers Net



Marubuci:- Abdulrahman Aliyu


Muna zamanmu muna taɗi,


Tamkar ba za mu gushe nan ba.


A ka ce da ni tafiya za ku yi,

Ba za mu sake gamewa ba.


Ni sai na ɗauka wasa ne,

Ko zuci ban yi tunani ba.


Sai ga shi kin tafi kin bar ni,

Wata mai kamar ki ba zan gani ba.


Abin yana ban mamaki,

Na kasa ma rufe bakina.


Idanuwana sun narke,

Ban samu kifta idanu ba.


Kafin a ce a jima Malam,

Ban san abin da yake nan ba.


Aka ce a kai ni wajen malam,

Boka ba zai iya wannan ba.


Aboki zo ka Ji zancen nan,

Ciwon fa ba iska ce ba.


Bagenta ne ya jiɓince ni,

Ban san akwai wani bege ba.


In har ana so in warke,

Asam'u ba tafiya ta yi ba.


Ganinta ma wani dace ne,

Ko da ba za mu yi zance ba.


Zancenta ya fi na littafi,

In ba na addini ne ba.


Godiya ga Alkali Husaini Ahmad Sufi

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user