Friday 30 August 2024

Siffofi 17 Na Mutanen Shaidan

Tura Wannan Zuwa Ga

Idan mutum yana da waɗannan siffofi sheɗan yana saurin shiga cikin rayuwarsa ya halaka shi, domin mai waɗannan siffofi, la budda zai zama mabiyin Sheɗani, 


Mutanen Shaiɗan
Hoto: Britannica


MarubuciSheikh Aminu Ibrahim Daurawa


1.  Jahilcin addini, ba karatu babu tambaya, sai musu da jayayya.


2.  Yawan fushi mai tsanani, shi yake kawo saurin ɗaukan mataki, wanda ake da-na-sani.


3.  Tsananin son duniya wanda yake makantar da ido da zuciya. Mutum ya yi ta yin abin da bai kamata ba domin kawai ya samu duniya.


4.  Tsawaita buri, sai na zama kaza sai na yi Kaza kuma duk a kan duniya.


5.  Kwaɗayi, wanda zai kai ga zubar da mutunci, da ɓarin lahira akan abin duniya.


6.  Rowa, wacce za ta hana fitar da haƙƙin Allah.


7.  Girman kai, ƙin karɓar gaskiya da wulaƙanta mutane.


8.  Son zuga, kirari da ƙarya da gaskiya.


9.  Riya, yin aikin lahira ba don Allah ba don mutane su gani su yaba.


10.  Alfahari da taƙama jiji da kai, har yana ganin kowa a banza.


11.  Mugun zari da zarmaiwa wajen son abin duniya ga kwaɗayi ga rowa.


12.  Biyewa son zuciya, mutun ya san gaskiya amma sai ya kauce mata da gangan.


13.  Mummunan zato ga Allah ta'ala, da bayin sa.


14.  Wulaƙanta duk wani na ƙasa da kai a komai.


15.  Raina zunubi da ɗaukan ba a bakin komai ba, ko kuma a fake da wani aiki, ko wata falala.


16.  Rashin sanin Allah game da yadda ake samun rahamarsa da yadda ake tsira daga azabar sa, mutum ya zama yana son rahama kuma yana tsoran azaba amma ya ƙi bin koyarwar Annabi (S.A.W), yana bin wasu hanyoyi daban ba yadda Annabi (S.A.W) ya bayyana ba. 


17. Domin Annabi (S.A.W) ya ce: kowa cikin al'umma ta zai shiga aljanna sai wanda ba ya so, sai sahabbai suka ce Ya Rasulallah waye ba ya so? Sai ya ce : duk wanda ya yi biyayya a gare ni zai shiga aljanna, wanda kuwa ya ƙi, ba zai shiga ba. Bukhari. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user