Thursday 5 September 2024

Aminin Banza Ko Aminin Gaskiya?

Tura Wannan Zuwa Ga

Za ku zauna tare da shi, ka amince masa, kake sanar da shi sirrikanka, kake damƙa masa amanarka, ka kuma dinga neman shawara a wajensa.


Aminan banza ko aminan ƙwarai?
Hoto: Times of India


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


Watarana za ka sanar da shi wani sirrinka, a matsayinsa na wanda ka kira da AMININKA, da zarar kun rabu, shi ma yana da nasa aminin, sai ya je ya kwashe labari da sirrin da kuka tattauna, ya sanar da shi, shi ma wannan aminin ya sanar da nasa aminin, har zance ya game gari, a saboda haka ake cewa "Ko ƙasa mutum ya shiga ya yi magana ya fito, to sai ta fito waje kowa ya ji" ni kuma na ce karya ne, ka binciki amininka.


Tabbas samun aminai masu iya riƙe sirri da kare mutunci da darajar abokansu ya yi ƙaranci.


A halin yanzu amininka shi ne wanda za a ke zaunawa tare da shi, ana zagin ka, shi ne wanda zai ke tona aibunka, shi ne kuma mai yin baƙin ciki ga samun ci-gabanka.


Ɓoye sirrinka kar da ka bayyana shi ga kowa, ba ya ga mahaifiyarka, tabbas ita kaɗai ce za ta iya riƙe maka sirri, ta kuma ɓoye aibunka, komai daren daɗewa.


Allah ya ba mu aminai na gari, masu riƙon amana. Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user