Tuesday 10 September 2024

Kalaman Soyayya Na Rabuwa Da Masoyiya Cikin Yanayi Na Damuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Na so a ce Allah ya ƙaddara rayuwarmu a tare a matsayin miji da mata, yadda zan nuna sakayyata a gare ki da kulawata, da soyayya ta  girma.


Rabuwa Da Masoyiya Cikin Yanayi Na Damuwa
Hoto: Zella life

Marubuci:- Muh'd Captain 


Ina jin kaina  kamar ba ni ba, tabbas ban san ya rayuwata za ta kasance ba tare da ke ba.


Ke ce mafarkina a duniyar soyayya amma na rasa ki me ya sa haka? Wanne irin laifi na yi wa soyayya ne?


Na koyi abubuwa masu girma na rayuwa a tare da ke. Ta musamman ce ke, na yi kukan zuciya wanda ya fi komai ciwo.


Tabbas ba ni da ikon canza ƙaddara amma da ke ce zaɓina, zan sadaukar da wasu ababen da na mallaka nawa a kanki.


Ba na jin zan iya sake soyayya a cikin rayuwata, ciwon da ke zuciyata ba zai warke ba har abada,  ke ce a raina da zuciyata, ina son ki har ƙarshen numfashina.


Ina fatan Allah ya ɗaukaka dajararki a cikin jinsin mata, amma ina tausayin kaina, rayuwa babu ke akwai ciwo a gare ni.


Na bar ki lafiya, Ubangiji ya yi miki albarka, ya kuma albarkaci rayuwar ki.


Tabbas soyayya ta fi komai sa farin ciki.


Kuma ta fi komai sa baƙin ciki a zuciya.


Ina da-na-sanin fara soyayya a cikin rayuwata a yanzu.


Me yasa? Me yasa za ki min haka a soyayya?

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user