Thursday 12 September 2024

Karanta Takaitaccen Sakon Barka Da Dare Na Soyayya

Tura Wannan Zuwa Ga

Sallamar salama mai tattare da amincin Ubangiji nake fata ya ci gaba da tabbatuwa a gare ki, ya ke zaɓin zuciyata.


Takaitaccen Sakon Barka Da Dare Na Soyayya
Hoto: En Dream

Marubuci:- It'z Nazeephancy DH


Haƙiƙa zuciyata ta zaɓe ki ne a bisa ilimin ki da kuma natsuwarki, saboda haka ina sonki, irin son da soyayya take alfahari da shi.


Saƙon gaisuwar barka da dare mai cike da ƙayataccen murmushi a kan fuskata ya isa gare ki yana mai wanzar da farin cikin da zai sanya zuciyarki miƙa saƙon murmushi akan fuskarki.


Barka da dare zaɓina.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user