Friday 6 September 2024

Shubuhar Farko A Tarihi

Tura Wannan Zuwa Ga

Shubuhohi sun daɗe a duniya kamar daɗewar ƙarya da gaskiya.


Shubuhar Farko A Tarihi
Hoto: Langit7

MarubuciAhmad Murtala Mansur


Shubuhar farko a duniya ita ce Shubuhar Iblis ta yadda ya ƙeƙasa ƙasa ya ƙi bin umarnin Allah Ta'ala na yin sujjada ga Annabi Adam alaihissalam bisa Shubuhar cewa shi ya fi Annabi Adam daraja saboda shi an halicce shi da wuta shi kuwa Annabi Adam da ƙasa aka yi shi.


Sakamakon haka Allah ya la'ance shi ya kore shi daga rahamarsa.


A maimakon ya yi nadama ya tuba sai ya lashi takobin sai ya ɓatar da zuri'ar Annabi Adam ya raba su da hanyar gaskiya saboda ya samu abokan zama a wuta.


Daga nan ya rinƙa ƙirƙirar Shubuhohi da yaɗa su ga mabiyan sa, wanda ya haifar da nau'o'in kafirci da munafunci da bidi'o'i da fasiƙanci iri-iri a duniya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user