Thursday 24 October 2024

Sakonnin Bayyana Yanayi A Soyayya Ga Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Amincin Allah ya tabbata a gare ki sarauniyar mata, dole na yi miki jinjina domin kin tafi mini da zuciyata. Ke ce muradina.


Bayyana yanayi a soyayya ga budurwa
Hoto: Merg2358

Marubuci:- Prince E


Zan so ki sani kuma ki sanar da zuciyarki lungu da saƙo a kan cewa kin tabbata haske mai haskaka zuciyata.


Amincin Allah ya tabbata a gare ki kyakkyawar ɗiya/'ya mai alkunya. 


Ke ce irin halittar farin cikin da ke faranta zuciyata tare da gangar jikina gaba-ɗaya.


A dalilin son ki nake ta faman shan wahala amman ke tamkar ba ki sani ba.


A kullum jin tattausan muryarki kan sanya zuciyata cikin farin ciki mara misaltuwa.


Ƙaunarki ta shiga ruhina, ta mamaye dukkanin ilahirin sassan jikina, ba ni da abin tunƙaho, abin alfahari a rayuwata wanda ya wuce a wayi gari ni da ke mun zama mallakin juna.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user