Wednesday, 20 November 2024

Zazzafar Wasikar Soyayya Ta Ustazi Zuwa Ga Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga masoyiyata.


Assalamu Alaikum, bayan dubun gaisuwa da ƙarin ƙauna a gare ki.


Yaa abar ƙaunata na sani kina da ɗimbin masoya bayan ni amma dai ina so ki sani cewa: ba zan gushe ba ina jaddada soyayya ta a gare ki kuma ina fatan haɗuwa da ke.


Zazzafar Wasikar Soyayya Ta Ustazi Zuwa Ga Masoyiya
Hoto: Dreams time 

Marubuci:- Umar Shehu Zaria


Na samu labarin cewa sadakin ki yana da matuƙar tsada amma duk da haka ba zan haƙura ba domin ba zan gushe ba ina zama da yunwa a cikin zafin rana a matsayin mai azumi kuma na hana idona bacci ina sallar dare, har sai na samu natsuwa akan cewa an yi mun masauki a cikin ki.


Na sani datti ba ya zama a cikin ki, shi ya sa aka ce masu al-Qur'ani za su samu daraja a cikin ki, don haka in shaa Allahu Ta'ala zan hana idanuwana bacci har sai na samu kaso mai tsoka a cikin al-Qur'ani.


Ina so ki sani ya sanyin zuciyata cewa tunda na ji Ubangijinki ya ce akwai Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, a cikin ki, tun daga nan na ɗimauce da ƙaunar ki ko na samu na yi maƙwabtaka da Farin Jakada.


Wato ba ni da wasu kalmomi da za su iya bayyana yadda nake ƙaunar ki a raina amma ina fatan ranar da za mu haɗu da ke na ji Mala'iku sun ce da ni: "Yaa Umar Shehu Zaria ka shiga cikin aminci".


Ina rokon Allah ya sa ina da rabon samun matsuguni a farfajiyarki.


Haza wa salam.


Sai mun haɗu.


Daga Umar Shehu Zaria zuwa ga abun Ƙaunata JANNATUL FIRDAUS.


Umar Shehu Zaria 

18 Jumada al-Ula, 1446.

(20/11/2024).


ƘARIN BAYANI


Wannan wasiƙar a zahiri ya rubuta ta ne ba zuwa ga masoyiya (Mutum) ba, ya rubuta ne zuwa ga Aljanna, amma za ku iya juya ta zuwa ga masoyiyar ku (Mutum), idan har ta burge ku.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user