Showing posts sorted by relevance for query Buzu Danfillo. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Buzu Danfillo. Sort by date Show all posts

Monday, 11 November 2024

Duniya Na Bukatar Ire-iren Baiwar Ka

Duniya Na Bukatar Ire-iren Baiwar Ka

Duniya na buƙatar baiwar ka, muhimmancin ka ya kai haka. Mutum ba ya bada baiwa, aljani ba ya bada baiwa, sheɗani ba ya bada baiwa, Allah ne kaɗai mai bada baiwa, kuma ba ya kuskure bare sharri.


Duniya na buƙatar ire-iren baiwar ka
Hoto: Pinterest

Marubuci:- Buzu Danfillo


Duk wanda zai janyo ka ƙasa da kushe da yasassun maganganu akan burin ka, ka fahimci cewa a sama da shi kake don sai yana ƙasan ka ne zai iya janyo ka ƙasa.


Shawara ita ce share banza ka ɗaga kai sama izuwa ga masu ƙoƙarin janyo ka sama da kalaman ƙwararawa da shawarwari.


Yadda wanda bai haihu ba ba ya sanin zafin ɗa, cima zaune ba ya sanin zafin kuɗi, to haka mara baiwa ba ya sanin daraja da amfanin ta, mahangar ka kai mai ita ba ɗaya ba ce da tasa. Martaba baiwa ita ma baiwa ce.


DUBA WANNAN: Karanta Ire-iren Baiwar Ɗan Adam 14 Masu Ban Mamaki


Gano hanyar sarrafa baiwar ka, tsarkake niyya ka shiga fagen fafatawa. Nasara na nan tafe!


Jinjina ga masu burika a fannoni daban-daban.


Ku yi buri don cimma shi a zahiri.


Ina tare da duk wani mai buri kuma zan goya masa baya koda 'yan ɗacin rayuwa za su jirkita tekun zuma ne izuwa maɗatai. Buzu na nan tare da ku.

Friday, 15 November 2024

Idan Ba Su Fahimci Baiwar Ka Ba

Idan Ba Su Fahimci Baiwar Ka Ba

Ga duk mai fama da tsangwamar jama'ar da'irar sa da ke yi masa hukuncin kuɗin goro da ƙin fahimtar sa da gangan dangane da baiwa ko burin sa, ka sani kai ɗaya ne daga cikin miliyoyin waɗanda ake sheƙe wa mafarkan su ko burikan su a kowacce rana. 


Idan ba su fahimci baiwar ka ba
Hoto: Photohobo/Freepik

Marubuci:- Buzu Danfillo


Idan kana daga cikin su, ka yaɗa wannan saƙon don nuna bara'ar ka akan wannan ɗabi'a ta koma-baya, tare da haska wa ire-iren ka cewa ba su kaɗai ba ne. Buzu na nan tare da ku.


Mun jima muna yi wa kanmu ƙeta ta yadda wasu ke morar fasihan mu sannan mu taya su ta hanyar sallama musu cewar ai dama fasahar su ce.


Duk da'irar da ba ta fahimci muhimmanci da fa'idar baiwa da fikirar ka ba, kada ka cancantar da ita zaman ka a cikin ta balle wawayen cikin ta su samu damar doɗe maka hasken lamirin ka da bakunan su marasa albarkar iya faɗin alkhairi, duk girma da yadda kake son wannan da'ira, ka motsa nesa daga gare ta, kuma ka gode wa Allah da kai ba bishiya ba ce.

Wednesday, 13 November 2024

Gina Babban Buri A Rayuwa

Gina Babban Buri A Rayuwa

A wasu shekaru can baya da yawa, wanda ya soma cewa duniya mulmule ce kamar ƙwallo saɓanin a mare kamar faranti (yadda aka ɗauka a da), kashe shi aka yi wai don ya kawo wata magana saɓanin abun da sarki da sauran gama garin mutane suka yi imani da shi a lokacin.


Gina babban buri a rayuwa
Hoto: Startup Nation

Marubuci:- Buzu Danfillo


Ai zairaitu (zombies) ba sa taɓa daina bin ka a guje kuma a fusace muddin kana a mutum ɗinka, har sai sun ga sun cije ka kai ma ka rikiɗe ka zama su, sannan kun tafi tare neman wani wanda yake a mutum bai zama irin ku kai da su ba. Kusan haka yawancin al'umma take a yanzu.


Ka samu babban burin da kake son cimmawa ta yadda har sai girman shi ya razana masu ƙaramin tunani, hakazalika tsukakken tunani sun fara kiran ka da mahaukaci suna yi maka habaici, to a nan shi ne ka hau ƙadamin daidai.


Duk wani ci-gaban al'ajabi a duniyar nan sai da aka kai ga haka kan a cimma shi. 

Friday, 1 November 2024

Komai Da Lokacin Shi

Komai Da Lokacin Shi

Ba kowa ke son lokacin zafi ba, amma ba ruwan shi yanayin da wannan, da zarar lokacin sa ya yi zai zo kuma ba zai tafi ba har sai lokacin nasa ya ƙare, hakazalika lokacin sanyi, damina da hunturu. 


Komai da lokacin shi
Hoto: Live science

Marubuci:- Buzu Danfillo


Ba sa hana kowa faɗin ra'ayinsa dangane da so ko ƙin su, kamar yadda ba sa bari ra'ayin kowan ya hana su wanzuwa a lokacin wanzuwarsu tare da gusawa a lokacin gushewar su.


Ni kaina da wannan tsari nake aiki, bakinka naka, gaɓoɓina nawa.


Kowa ya sarrafa abun da yake da iko da shi.


Kai ma idan har kana son zama lafiya da lamirinka da nutsuwar ranka, ka koyi rayuwa bisa tsare-tsare da ma'aunanka ba na 'yan zauna-gefe ba.


Idan abu ya kulle maka kai ka nemi shawara. Wannan bisa buƙatarka ne, amma kada ka tanka wa masu cushen shawarar da ba ka nema ba, hasali irin waɗannan sun fi kowa buƙatar shawara a rayuwa.


Ka yi komai a lokacin ka ba a lokacinsu ba, ba tare da neman fahimtar da kowa dalili ko uzurinka ba.

Saturday, 9 November 2024

Zantuttukan Karfafa Gwiwa Ga Wanda Ya Fidda Rai Na Cikar Burin Shi

Zantuttukan Karfafa Gwiwa Ga Wanda Ya Fidda Rai Na Cikar Burin Shi

Idan kana da burin da kake son cimmawa, sai kuma ya zama abokai da makusanta ba sa mara maka baya, to ka sani ba haƙƙin ka ba ne a kansu sai sun mara maka baya, duk da cewa ya kyautu su yi hakan, hasali wannan jarrabawa ce mai fayyace cancantar ka a kan wannan buri ko akasin haka.


Zantuttukan Karfafa Gwiwa Ga Wanda Ya Fidda Rai Na Cikar Burin Shi
Hoto: Psychowellness center

Marubuci:- Buzu Danfillo


Shin za ka iya tsaya wa kanka yayin da hatta na kusa da kai sun yi wasarere da mafarkin ka ko burin ka? Ko kuma nasarar ka ta raja'a ne a kan ra'ayoyin waɗanda ba su da fahimta ko ilimi akan abun da ka sa a gaba? Wannan jarrabawa ba tsakanin kai da su ba ne, tsakanin kanka da kanka ne.


Za ka iya hawa hanyar muradin ka kai kaɗai ko sai da 'yan rakiya?


Yadda ba dole ba ne sai sun mara maka baya, kai ma ba dole ba ne sai ka yi da su, ba a shafi ɗaya kuke ba, hakazalika ba amo ɗaya kuke yi kai da su ba, don haka ba za ku taɓa fuskantar juna ba.


Yayin da ƙasa ta ƙi karɓar shuka ba shukar ake sauyawa ba, ƙasar ake sauyawa don haka idan mafarkin ka ko burin ka ya ƙi shukuwa a ƙasar gaban ka, to tuge shukarka ka nema mata ƙasar da za ta girmar da ita, babu riƙo ba ƙullaceceniya. 


Sai dai zuwa gaba idan ka yi nasara, kada ka ba kowannen su damar haskawa tare da kai wato shining da kai. Irin "Ai wane ga gidan mu ga gidan su". Ɗin nan. Kawai ka fuske irin na rashin ganewa ɗin nan, ehi.


Waɗanda suka fi mu ci gaba a duk faɗin duniya ba basira ko baiwa suka fi mu ba, tsari, ɗabi'a da ɗa'a suka fi mu.


Baiwa da Fikira ba su da al'umma, addini, jinsi, ƙabila, yare/harshe ko ƙasa. Lamunci hakan ka samu sa'ada.