Showing posts sorted by relevance for query Usman Yanmaza. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Usman Yanmaza. Sort by date Show all posts

Monday, 18 November 2024

Tafiyar Da Rayuwa Cikin Nasara

Tafiyar Da Rayuwa Cikin Nasara

Kar ka taɓa jin tsoron rashin nasara ko faɗuwa, faɗuwa da rashin nasara waɗannan duka sunna ce ta rayuwa, saboda su suke taimakonmu wajen girmanmu. Kar ka kuskura ka ji tsoron faɗuwa ko rashin nasara akan wani abu saboda wani lokacin sai ka faɗi kake koyon wani sabon abun, sai ka rasa abu kake sanin muhimmancin shi.


Tafiyar da rayuwa cikin nasara
Hoto: Mohammadimran229182

Marubuci:- Usman Yanmaza


Kar ka rinƙa haɗa kanka da sauran mutane, dole ne wani ya fi ka kuma kai ma ka fi wani, kowa yana da irin nasa abun na musamman da sauran mutane ba su da shi, abu mai muhimmanci shi ne ka maida hankali wajen cimma abubuwan da ka saka a gaba kar ka damu da na wasu.


Ka ringa ɗaukar darasi daga kurakuranka. 


Kowa yana kuskure a rayuwa, abu mai muhimmanci shi ne ka ringa ɗaukar darasi a kurakuranka hakan zai ba ka damar gyara gaba domin kauce ma hakan.


Ka yarda da kanka kawai shi ne babba a rayuwarka. Musamman idan ka saƙa wani burinka, ka yarda cewa watarana za ka cimma burinka akan hakan, sannan ka tabbatar kana aiki tuƙuru wajen cimma hakan. Kar ka zamo mara buri.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

Sunday, 24 November 2024

Dalilan Samuwar Dabi'u Kyawawa Da Dabi'u Munana

Dalilan Samuwar Dabi'u Kyawawa Da Dabi'u Munana

A Falsafance ya nuna ƙiriƙiri dangane da alaƙar da ke tsakanin ƙwaƙwalwa (Brain) da ɗabi'a (Habit) wanda abubuwa guda biyu ne masu tafiya da juna hannu bibbiyu.


Dalilan Samuwar Ɗabi'u Kyawawa Da Ɗabi'u Munana
Hoto: R pics/Reddit

Marubuci:- Usman Yanmaza


Masana ilimin ƙwaƙwalwa wato "neurologists" suna nuni da cewa a cikin bangon ƙwaƙwalwa akwai wani gefe a cikin ƙwaƙwalwar wanda ake kira "Basal ganglia" wanda yake amfani wajen riƙon abubuwa wanda jiki ko ayyuka suke yi na yau da kullum, ita wannan Basal ganglia ɗin ita ce matattarar ɗabi'u koda a lokacin ƙwaƙwalwa tana bacci ko hutu.


A kan samu daga cikin mutane wanda suka samu rauni a Basal ganglia nasu za ka ga sun kasance suna da ciwon mantuwa wanda yanzu za ku yi magana amma cikin minti ɗaya ya manta, zai iya manta yadda yake wanka, zai iya manta fuskar abokansa da sauransu. A cikin dabbobi misali za ka ga ɓera yana da mantuwa, yanzu tarko zai kama shi amma ana cire shi zai sake komawa wajen tarkon saboda mantuwa.


Masanan sun ci-gaba da cewa "ɗabi'a" ta kan wanzu ne saboda "ƙwaƙwalwa" a kullum tana neman sauƙaƙa yadda za ta rage wahalhalu ga kanta ne, shi yasa take sarrafa aiki ko hankali da zuciya wajen bin jiki. Sannan ɗabi'a babbar aba ce a rayuwar Ɗan Adam, shin ka taɓa tambayar kanka me kake fara yi idan ka tashi daga bacci? Goge baki kake fara yi, ko banɗaki kake fara shiga, ko wanka kake fara yi? Sannan ka taɓa lura da abin da kake fara yi idan ka dawo daga wajen aiki ko wajen kasuwanci? Ka taɓa lura da abin da kake yi kafin ka kwanta bacci? Duk waɗannan suna daga cikin ɗabi'a wato "Habit management".


Amma abun tambayar anan shi ne ko ɗabi'a tana tafiya da ƙwaƙwalwa? Eh tabbas tana tafiya da ƙwaƙwalwa amma ba lallai ɗabi'ar ta zamanto mai kyau ba, ɗabi'a a muhallinta na "habit" tana da 'ya'ya wato ɗabi'u masu kyau "Good habits" da ɗabi'u marasa kyau "Bad habits". Amma fa kowanne daga cikin biyun sunan shi ɗabi'a.


Daga cikin Ɗabi'u Masu Kyau akwai wanda za ka ga masu shi kullum suna kyawawan abubuwa saboda ya bi jikinsu, misali kyauta, yawan gaisuwa, sabawa da jama'a, girmama mutane, taimako da sauransu.


Daga cikin Ɗabi'u Marasa Kyau akwai irin su shaye-shaye, rashin kunya, zagi, ta'addanci, sace-sace da sauransu.


Masana sukan faɗa cewa, kai za ka fara alƙalanci dangane da ɗabi'unka. Ka fi kowa sanin abubuwan da kake yi idan masu kyau ne ko akasin haka. 


Ƙwaƙwalwa abokiyar ɗabi'a ce na kyau ko akasin haka, matsalar shi ne sarrafa ƙwaƙwalwar wajen mai da ita ɗabi'a musamman masu kyau anan kuma jan aikin yake.


To ina mafita? Ku ci-gaba da bibiyar mu.

Tuesday, 12 November 2024

Zafafan Tambayoyi Ga Kowanne Matashi

Zafafan Tambayoyi Ga Kowanne Matashi

Ga wasu tambayoyi ga kowanne matashin da ya wuce shekaru ashirin a duniya wacce sanin amsar ta ya ke da matuƙar muhimmanci.


Zafafan Tambayoyi Ga Kowanne Matashi
Hoto: Youth time mag

Marubuci:- Usman Yanmaza


Shin idan aka tambaye ka, wacce nasara ka taɓa cimmawa a rayuwa, ta ya ka cimma wannan nasara, kana da amsar da za ka bayar?


Shin idan aka tambaye ka mene ne manufarka? Wanne tsari ka yi wa rayuwar ka don cimma waɗannan manufofi kana da amsoshin waɗannan tambayoyin?


Shin wanne buri kake son cimmawa nan kusa, waɗanne ne kuma kake son cimmawa nan gaba (short and long term goals), sannan kuma ta ya za ka cimma waɗannan burikan? Shin ko kana da amsar wannan tambayar?


Shin da me za'a iya tuna ka ko bayan ranka? Wanne tasiri ka yi wa sauran mutane a tsawon rayuwar ka, da za su iya tuna ka su yi maka addu'a dalilin shi?


Shin idan aka tambaye ka, wanne abu ne kake aikatawa, kake son ka daina aikata shi, amma ka kasa hakan? Wanne tsari kake don daina aikata wannan abin?

Wednesday, 6 November 2024

Bambanci Tsakanin Mai Ilimi Da Mai Hikima

Bambanci Tsakanin Mai Ilimi Da Mai Hikima

Akwai bambanci tsakanin ilimi "Knowledge" da kuma hikima "Wisdom" amma sai dai ba kowa ba ne yake iya tantance su ba. 


Bambancin Mai Ilimi Da Mai Hikima
Hoto: Egypt today

Marubuci:- Usman Yanmaza 


Shi ilimi abu ne wanda ake koya kuma a iya, ko a ƙware bisa maida hankali (rigorous test, practice and learning), ita kuma hikima, hikima ce da Allah yake ba wa mutum kaitsaye koda kuwa ba ya da ilimi. 


Ita hikima ba ta buƙatar ilimi saboda akan samu mutane da yawa wanda ba su je makaranta ba amma suna da azanci a abubuwa wanda ko wanda ya je makarantar ma ba zai nuna musu wasu abubuwan ba. To amma a falsafance akwai abin da yake haɗa ilimi (knowledge) da hikima (wisdom) wato shi ne kuma basira "cognitive - ability" wanda shi kuma ƙoƙarin ƙwaƙwalwa ne wajen yin amfani da abubuwa.


Sannan kuma akwai bambanci tsakanin mutum mai hikima (wisdom) wanda kuma har yanzu yana da ilimi (knowledge) da kuma wanda yake da hikima amma ba ya da ilimi, ta inda shi mai hikima wanda yake da ilimi yake saurin cin moriya akan abubuwa saɓanin shi wanda yake da hikima amma ba ya da ilimi.


To amma ko ka san akwai bambanci tsakanin "hikima" da "manyance"? Akwai wanda suke son su ringa abubuwa na hikimomi amma sai su faɗa manyance ba tare da sun sani ba, musamman idan ba su yarda cewa ba su da ita (hikimar) ba, ta inda a lokaci guda manyancen kuma sai mutane su ɗauka hikima ce, kafin ka ankara kuma ya fara maida mutane shashashu "fooling" ɗinsu. Shikenan kuma ya zamo "shugaban sakarkaru" ba tare da su sun san ba hikima yake da shi ba zallan manyance ne kawai.


Sannan idan Allah ya yi ka mai hikima to haka za ka ringa abubuwan ilimi da azanci (koda ba ka je makarantar ba) amma kasancewar zamantakewa ko wata baiwa sai ka ga ya haska maka wasu abubuwan da masu ilimi kaɗai suke da ikon magana akai, wanin ma har ka fi su.


Shi mai hikima zai iya juya wani abu (idea) na mai ilimi ba tare da shi mai ilimin ma ya iya gane hakan ba. Akwai tarin misali dangane da haka.


Sannan kowane Ɗan Adam ba'a rasa shi da wata ɓoyayyiyar baiwa koda ba shi da ilimi, aƙalla yana da wata baiwar da Allah ya masa wadda ba kowa ya sani ba, wataƙila shi kansa ma bai lura yana da baiwar ba, ko kuma bai san hakan baiwa ba ce ba.