Sunday 1 October 2017

Magana Jari ce: LABARIN SARKIN ZAIRANA DA SARKIN BOKAYE GARA

Tura Wannan Zuwa

Daga littafin Magana Jari Ce 1
Na Alhaji Abubakar Imam
(c) NNPC Nigeria

Akwai wani Sarki a Zairana wanda Allah ya nufa
da kiba, abin har ba iyaka. Idan ka gan shi sai ka
ce giwa, in ya zauna ba yadda zai yi ya ga
cibiyarsa, dokin duniyan nan duk ba mai iya
daukarsa. In ya tashi daga zauren gidansa zai
shiga, mutum ya yi tafiyar loko biyu Sarkin nan
bai isa ba.
Sarki fa duk abin duniya ya dame shi bisa ga
wannan kiba, shi kuwa ba abin ya ki cin abinci ba
ya mutu. Saboda haka ya tara bokayen kasarsa,
ya ce su yi kokari su samam masa maganin da
zai sha ya rage kiba. Bokayen suka shiga
aikinsu. Kowa sai ya sassako wannan itace, ya
gino wannan sauya, ya kai wa Sarki. Ya yi ta
sha, amma a banza. Maimakon ya ragu sai
karuwa ya ke kullum safe, sai ka ce ma maganin
ya kara kiba su ke ba shi. Da Sarki ya ga haka
sai ransa ya kara baci, ya yi kamar ya kashe
kansa don haushi. Ga duniya Allah ya ba shi,
kiba ta hana shi jin dadin cinta.

Yana nan haka sai ya ji labarin wani boka wanda
a ke kira Gara Mai Aburkuma. Sarki ya aika aka
kira shi, ya bayyana masa bakin cinkinsa. Ya ce
in ya warkad da shi kuwa zai yi masa kyauta har
ya kasa godiya.

Gara ya ce, “To, Allah ya taimake mu. Amma in
ka yarda, ranka ya dade, ina so a ba ni kwana
uku in je in shawarci Aburkuma, Inna uwa ma ba
da mama, abina da muka yi da ita duka zan zo in
gaya maka.” Sarki ya ce, “To, je ka, na ba ka
iznin kwana uku, amma kada ka wuce haka.”

Gara ya yi ban kwana, ya tafi. Ya yi ta tunanin
inda zai fito wa Sarki ya yaudare shi. Ya san dai,
in ba wautar Sarki ba, wane boka ne zai iya ta da
hukuncin Allah?
Bayan kwana uku sai Gara ya komo wajen Sarki,
ya ce, “Allah ya ba ka nasara, na dawo.” Sarki ya
ce, “To, ina labari?”
Gare ya ce, “Allah ya daukake ka, ai sai a bar
kaza cikin gashinta, al’amarin ya tayar mini da
hankali.”
Sarki ya ce, “Me ka gani, na ce. Fada mini mana
in ji.”

Gara ya ce, “Allah ya ja zamaninka, ai ba na iya
fadin abin da Inna ta gaya mini. Saboda bakin
cikin al’amarin, jiya, na rantse har da rawaninka,
ban yi barci ba. Abin da na gani ya fi sai a bar
wata wahalar neman magani, a tasam ma
istingifari.”

Sarki ya fusata, ya ce, “Yau ga zancen banza. Na
ce ka gaya mini abin da ka gani, ka tsaya kana
kewaye-kewaye.”

Gara ya ce, “Allah ya yi wa Sarki rahama, Inna ta
ce saura kwana arba’in ka riga mu gidan
gaskiya.” Sarki ya fusata, ya ce a kama shi a
daure. Dogarawa suka café shi. Gara ya ce, “Da
ma abin da na ke gudu ke nan da gaya maka
gaskiya.” Aka dai iza keyarsa zuwa gidan
kurkuku.

Sarki ya shiga zulumin abin nan da Gara ya fadi,
ya ce, “Na san Gara fa shahararre ne bisa ga
al’amari da aljannu. Ba abin da ya fi dai sai a rika
kidaya kwanakina da ya fadi. In sun cika arba’in
na ga ban mutu ba, na san Gara karya ya ke yi.

In kuwa na ga bayan kwana talatin da takwas, ko
talatin da tara, na fara ‘yar mashasshara na san
ni tawa ta kare.”

Wannan zulumin da ke ran Sarki fa ya sa ya
tsunke. Ko abinci ba ya iya cin abin kirki, balle
ma ya faranta ransa da wadansu kawace
kawacen duniya. Saboda haka kullum sai ramewa
ya ke don zulumi Duk mutane suka rasa kansa
suka rasa gindinsa.

Bayan kwana talatin da wannan magana sai
tashin hankalin nan ya yi masa yawa, har ya sa
kansa ya rika ciwo. Rana ta talatin da tara da ya
ji ciwon kan na karuwa, sai ya kira dansa ya
danka masa mabudin taskoki, ya yi ta yi masa
wasiya, yana gargadinsa yana cewa su tasu ta
kare. Yaro bai san abin da ya ke nufi ba,
tsammani ya ke don ya fara tsufa ne ya ke so ya
nuna masa al’amuran mulki.

Ana nan dai kwana arba’in suka cika, Sarki na
jiran mutuwa, bai ga ya mutu ba. Kwanaki dai
suka kai kwana arba’in da biyar, Sarki bai ga ya
mutu ba. Sai ya aika aka zo da Gara daga gidan
sarka, ya ce, “Ka ce bayan kwana arba’in zan
mutu, ga shi yau kwana arba’in da biyar da
maganar, ban mutu ba.”

Gara ya ce, ‘Da ma maganin ka rage kiba ka
tambaye ni, to, karyan nan da na yi na ce saura
kwana arba’in ka mutu ita ce maganin. Ka
tambayi kowa nan garin ka ji in ba ka rage kiba
ba.”

Da Sarki y ji haka, sai hankalinsa ya kwanta, ya
bushe da dariya, mutane suka yi kyakkewa baki
daya, suka ce, “Lalle Gara ya isa dan duniya.”
Gara ya ce wa Sarki, “Ba abin dariya ba ne, sai
ka ba ni abin da ka alkawarta.”

Sarki ya sa aka yi ta kawo masa riguna da
zannuwa da wanduna, ya kuma ce duk mai
kaunarsa ya yi wa Gara kyauta. Mutane suka yi
ta zuba masa kudi, tun yana godiya har ya fashe
da kuka don murna. Sarki ya sallame shi, ya
kwashe kayan da aka ba shi duk, ya tafi.
Kullum in an ta da labari, sai Sarki ya yi ta yi wa
kansa dariya in ya tuna abin da ya yi daren da
kwanan nan arba’in za su cika, da ya yi ta yawo
tsakar gida shi kadai, ya kai gwauro ya kai mari,
yana ta salati ga Fiyayyen talikai.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: