Monday 2 October 2017

6. YAWON DUNIYAR HAJJI BABA Na James Morier Abubakar Tunau Ya Fansar Da Shi

Tura Wannan Zuwa

“Daga nan sai majalisa suka kosa su ji yadda na
sami wannan daraja. Na ce musu, ‘Da farko dai
ubana ya mutu ya bar mini gadon jaka saba'in,
Sarki kuwa ya yarda in ci gadon. Da yana so da
ya rike. Kuma ga shi ma’aji yana son ya ci ni
tarar jaka tamanin da hud’u, Sarki bai yarda ba.’
Na dai yi ta yabon Sarki, aka kuwa kwashe aka
fada masa. Shi kuma ya ba ni rigunan daraja, da
kwat da 'yar ciki da hula da alkyabba. Sa'an nan
kuma ya ce ni ne Sarkin Mawaka. Ga al’ada kuwa
a kan sa wannan hula har kwana uku ba fashi,
don mutane su yabe ni. Na kuwa sa.
“Sa'an nan na rubuta waka na zazzagi ma’ajin
nan daga sama har kafarsa, amma ba wanda ya
gane zambo ne don da Larabci na rubuta. Kowa
yana tsammanin yabo na yi. Ba a waka kadai na
shahara ba. A’a, har ma na kware da aikin
makaniki. Na yi abubuwa tuli da a ke sha'awa
tasu a fada. Ina kan hanyar yin tufafi ke nan sai
Sarki ya tsauta mini, ya ce nn manne wa wakata.
In yana son tufaii ne ai ya aika a kawo masa
daga Turai. Na bi umumin Sarki na bari.
Sa'ad da bikin sabuwar shekara ya kusa
kewayowa, sai na rubuta waka na ba Sarki
kyauta, don al’ada ce ga ko wane baran Sarki ya
ba shi kyauta a wannan rana. Da ranar ta zo ya
sa manyan mutane suka sumbance ni a gaban
taro don wannan kyauta da na ba shi. A cikin
wakar na kwatanta hakoran Sarki da lu'ulu'u,
gemunsa da gashin bakinsa kamar yadda ruwan
teku ke tashi sama ya kwanta, da dai sauran
yabo irin wadannan. Kowa ya yi ta yabona
saboda fasahata ta tsara abubuwa. Suka kuma
ce mawakin Sarki na da jaki ne in an gwada shi
da ni.
“Ta haka na ji dadi kwarai wurin Sarki. Don ma
Sarkin yana sona da samun arziki da daraja, sai
ya sa ni in rika kai wa dansa Sarkin Fars
sababbin rigunansa a ko wace karshen shekara.
Da na isa Shiraz aka karbe ni da murna, aka yi ta
ba ni kyauta masu daraja. Da na hada su da abin
da na samu a kauyukan da na bi, na sami kudi
masu yawa. Amma abin da ya same ni jiya din
nan ya sa na yi hasarar kome, ga shi yanzu na
komo mai bakin ciki kwarai.

“Idan ba ka yi kokarin ka taimake ni na gudu ba,
na sani zam mutu. Kudin da na ke da su
wadanda zan iya fansar kaina an sace mini, ban
kuwa san inda zan sake samun wadansu ba.
Kaddara ce dai da na fada a hannun mutanen
nan, don haka ba zan yi bacin rai ba. Amma ina
rokonka da ya ke kai Musulmi ne dan'uwana ka
taimake ni cikin bacin raina.”

BABI NA 4

Na Yi Gudun Gara Na Fada Zago
BAYAN da mawakin nan ya kare ba ni labarin
kansa, sai na yi masa alkawarin zan yi iyakar
kokarina in taimake shi, amma na ce masa a
yanzu kam sai ya dauki hakuri, don ni kaina ban
shirya hanyar da zan gudu ba tukuna balle in
taimaki wani. Ba dama in gudu a wannan lokaci,
don duk idanunsu a kaina ne, dawakinsu kuma im
ba su fi nawa gudu ba, to, sa zo daya. Bayan
haka kuma ban san wurin sosai da sosai ba, don
haka ya zama tilas in dakata sai na sami fili.
Muna cikin tafiya sai muka zo daf da inda za mu
ketare wata babbar hanya wadda ta taso daga
Tehran zuwa Meshed, wajen mil saba’in daga
gabashin Damgan. A nan Alhassan Sultan ya ce
mu tsaya mu nemi maboya, ko za mu yi sa'ar
mu sami wani ayari mai wucewa mu wawashe
su. Aka kuma aika da wani ya je ya yi gadi, da
cewa ya ga alamar ayari, ya zo ya fada.
Kashegari da asuba sai ga mai gadin nan a
sukwane, ya zo duk yana huci ya ce ya ga kura
ta murtike daga hanyar Damgan, kurar kuwa ta
nufo inda mu ke ne, watau a hanyar da ta nufi
Meshed.
Nan da nan muka shirya. Aka daure bayin nan
uku hannu da kafa, aka bar su nan inda muka
kwana, wai im mun dawo mu dauke su. Mu kuwa
muka shiga makamai, muka kama hanya a
hankali, za mu fashi. Alhassan da kansa ya ja
gaba don ya ga ta inda za a bullo wa ayarin. Ya
kira ni ya ce, “To, Alhaji, ga zarafi ya zo da za ka
nuna jaruntaka. Za ka bi ni ka ga dabarun da zan
yi duka, don kai ma wata rana ka iya bi da
mutane da kanka. Na kirawo ka ne don watakila
zan so tafinta, domin ba wanda ya iya
harshemmu. Za mu matsa kusa da su, watakila
mu yi 'yar gardama da madugun, amma im bai
yarda mu daidaita ba, to, sai dukanmu da
mutanemmu mu auka musu baki daya."
Da matafiyan nan suka matso sai na ga Alhassan
ya damu. Ya ce, “Ina fa tsoro wannan ba ayari
ba ne, sun faye tafiya a tattare. Bayan haka ma
ban ji karar gwarje ba, kura kuma ta cika
murtukewa a wuri daya. Na ga masu, kai, Sojan
Doki ne, yau mun hadu da gamommu." Da dai
suka matso, sai muka ga ba ayari ba ne, watakila
wani shahararren mutum ne kamar Gwamnan
wata kasa, za shi wani wuri. Ga ’yan rakiyarsa
nan birjik, ga dawaki barkatai. Muka juya mu
gudu, amma ni na sassauta har suka iso kaina.
Suka buge ni daga kan doki, suka kwace mini
kome da kome, har da kudina £30. Suka daure
hannuwana a baya, ko da ya ke na ce musu ba
zan gudu ba. In na bude baki zan yi magana sai
ka ji am mare ni, aka ja ni gaban Sarkinsu.
Da ganinsa na san lalle shi dan Sarki ne. Da
zuwana kusa da shi na san zaton da na yi
gaskiya ne, don nan da nan aka rufe ni da duka
wai in kwanta a gabansa. Duk mutane suka
kewaye shi, sa‘an nan ya ce a kwance ni. Da
kwance ni sai na yi wuf na kama alkyabbarsa, na
yi ta rokon sa ya cece ni. Wani ya fusata ya zo
zai bankade ni, amma dan Sarkin ya ce a kyale
ni, na sami mafaka. Bayan da ya ce wa barorinsa
kada wani ya taba ni, sai ya ce im ba shi labarin
yadda na shiga irin wannan hali. Na fadi bisa
guwawuna, na sumbanci kasa, sa’an nan na fada
masa duk yadda aka yi. Na ce kuma in yana so
ya tabbata abin da na fada sai mutanensa su
auka wa ‘yam fashin, domin suna nan kusa, su
kwanto mawakin Sarkl da wadansu mutanen
Farisa guda biyu. Na kare magana ke nan sai ga
wadanda suka raraki Alhassan Sultan sun dawo
suna huci, suka ce sai a shirya yaki don ga ’yam
fashin nan wajen dubu sun nufo kammu. Na yi na
yi in ce musu su ashirin ne kawai, amma ba
wanda ya gaskata. Suka ce muddin 'yam fashin
suka auka musu, to, za su kashe ni.
Nan da nan aka watse aka yi ta dudduba hanyar
da 'yam fashin za su fito. Ni an kwace dokina,
don haka na hau wani alfadari mai dauke da
kaya. Na ga ba ni da ko anini ba kuma aboki, sai
na shiga zullumi, raina ya yi matukar baci. Na yi
na yi da mutanen nan su gane ba ni da nufin
mugunta, su ji tausayina su yi mini alheri, amma
ban da dariya ba su yi mini kome. Sai dai wani
mai alfadari sunansa Ali katir ya kunna lofensa
ya ba ni ya ce mini, “Dana, kome na duniyan nan
yana hannun Allah ne. Da Allah ya mayad da
alfadarin nawa fari ne, na iya maishe shi baki ? A
wata rana alfadarin nan ya kan ci dawa, a wata
rana kuma ya kan ci kaya. Za mu iya gaba da
kaddara ne ? Sha lofenka kawai ka ji dadi, ka yi
godiya don abin bai baci da yawa gare ka ba."
Wannan magana ta kwantar mini da rai.
Muna cikin tafiya ya ce shi dan Sarkin nan da na
fada hannunsa, shi ne da na biyar na Sarkin
Farisa, bai dade ba da aka nada shi Gwamnan
Khorassan. Yanzu yana hanyar zuwa
hedkwatarsa ce a Meshed. Dalilin da ya sa
mutane da yawa ke raka shi kuwa, shi ne an
sami labari akwai ’yam fashi a hanya. An ce
masa in ya isa ya tayar wa ’yam fashin gadan-
gadan, ya aika da kawunansu da zai iya samu
zuwa Tehran, don a jibge su a kofar fada. Wai na
yi sa’a kwarai da ba a yanke nawa ba.
Da muka isa inda za mu huta na yi niyyar in ga
dan Sarkin nan, don ko na sami £30 dina, da
dokina, da makamaina. Na yi sa'a kuwa na gan
shi yana zaune a tabarma. Ko da na matso sai
fadawansa suka yi wuf kamar za su bankade ni,
amma kafin su sami dama na daga murya da
karfi na ce ina da kara da zan kai ga dan Sarki.
Da dan Sarkin ya ji, ya ce a kira ni. Da na zo ya
tambaye ni abin da na ke so. Na ba shi labarin
yadda aka yi mini satar dokina, da kudina, da
makamaina. Ya ce a mayar mini da dokin da
makaman. Ya tambayi ko su wane ne suka yi
mini fashi. Nan da nan aka turo keyarsu gabansa.

Ya tambaye su ina kudin da suka sace mini?
Suka ce ba su saci kome ba. Dan Sarkin ya ce a
tambaye su. Tun da aka fara koli koli da su, sai
suka ce suna nan. Suka kawo kudin, dan Sarkin
ya kirga ya daga tabarmarsa ya zuba, ya ce mini.
“Tashi an sallame ka.” Na tsaya ko zai miko mini
kudin amma ina! Da dai na ce ina kudina, shi ke
nan sai na ji an rufe ni da duka, aka ce mini
maza in tafi im ba ina so a yanke mini kunne ba!
Ka ji ikon Allah, ni da kudina wai har za a yanke
mini kunne!

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, da karfe
tara na dare (9:00PM), in sha Allah.
Allah ya kai mu.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏.

.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: